Chapter 32
Chapter 32
sosai ga wani shining datakeyi kanan yasha kitso da lalle ga halawa da momy tasa ayi mata kai abindai sai wanda yagani ,washe gari misalin 11:am Humaid ne yai sallama cikin shigar shi ta 'alfarma samun su momy yayi a parlor lokacin suka gama breakfast kasancewar ba da wuri sukeyi ba Khadija na d'akinta tana shirya kayanta tunda momy tace ”sai k'arfe 5:pm zasu tafi. Durk'usawa yai ya gaida momy ,amsawa tayi cike da kulawa ta mik'e tabar gurin sbda tasan abinda ya kawoshi ,😥ayya mom kin maida Humaid....🤐 kai tsaye d'akin khady ya shige yana yanga yana dariya yau dai gani ga baby na ,ta6e baki Khadija tayi tace ”to anfasa ai zaro ido Humaid yayi yace ”hhh dana sunkuceki mun wuce ai, dariya suka sa d'aukar yaran yayi yana yimusu adu'a bayan ya gama yace ”to tashi muje ,momy data ke shirin shigowa kiran Khadija takawo yaran ayi musu wanka ta tsinto maganar Humaid a sama , yana cewa tashi mutafi ,dubanshi tayi tace ” Humaid yaushe kazamo marar kunya ne ?eyye sunkuyar da kansa yayi dan yasan tabbas yayi laifi ,muryar Momy ce tadawo dashi daga hayyacin sa tace ”to yanzu ba da bane ka kular min da yarinya ,insha Allah Humaid yace daganan ya tashi yai gaba ,nasihoyi momy take yiwa Khadija sosai kuma yana shiga kunnen ta." misalin 5:pm Humaid ya dawo suka wuce shida Khadija ,momy ta sanya musu albarka haka ma dady , fatan alkhairi yayi musu . Da isar su suka tarar da komai an gyara gidan sai k'amshi yake zubawa ,yada zango Khadija tayi parlor kan d'aya daga cikin kujerun tayada zango ,Dady na hanunta shikuma Humaid Abba ya d'auko ,duka sunyi barci ,d'aukarsu yai d'aya bayan d'aya yaje ya kwantar dasu. Soyayya suke zubawa sosai Humaid yayi k'iba hakama Khadija sbda momy ta d'aukar mata mai aiki ,watan su Dady da Abba biyu ,Khadija ta tambayi Humaid zuwa k'auye ,baiyi yink'urin hanata ba sbda yasan ta dad'e bata je ba ,sunsa rana kasan cewar gobe weekend ne ,Khadija ce ta kira momy take gaya mata , momy tai farinciki tace ”mata subiyo tanan tanada sak'o ." Washe gari misalin k'arfe goma na safiya ,sun gama shiri kwana biyu Khadija zatayi Humaid kuma 'a ranar zai dawo ,kayanta wanda bata sawa ta loda a d'an ma dai_dai cin akwati suka shige mota ,kai tsaye gidan momy suka nufa ko zama basuyi ba suna gaisawa ta tambayi lpyr yaran ta gansu suka wuce ,tsara sosai Humaid yayiwa su Inna hauwa. Da isarsu garin Humaid ya kwashe da dariya harda tafawa yace ”boys ko inbaku labarin momynku ne yakuma sa dariya ,Khadija ta gano shi sarai ta sha murr taki kulashi sai da suka sukane ya kar6eta yaran ,da sallama suka shiga gidan su inna ,cikin fara'a inna tace ”wa'alaikumussalm oyoyo da masu jego ,Sahura dake d'akin inna tana kwaliya tace ”to wai suwaye sukazo ne naji kinta wani zumudi ,inna ce tace ”y'an binni ne sukazo su Humaidu ,da gudu Khadija ta fito tana washe hak'ora bakinnan yasha jan janbaki ga wani lafcecen Baki a girarta , Khadija ce ta bud'e baki tana cewa Sahura ina zakikai wanan tsayin ,dariya Sahura tayi tace ”akwai kayane in kwaso ¿a lokacinne Humaid yai mgna yace ”eh suna bayan mota da gudu ta fice tana tsalle Inna ce tace ”angirma ba 'asan angirma ba jibeta ,takusa kaiwa waje tajiyo inna tace ”ed'in ta murgud'a baki ,kwaso kayan takeyi kamar wata giwa sbda k'arfi da Allah ya zuba mata 'abin ba'a magana. Ibayan sun shiga d'aki 'inna ta kawo musu fura da nono ,kar6ar yaran tayi ta goya d'aya d'aya kuma yana hannunta ,tsarabar suka mik'awa inna dakuma sak'on momy ,da kayanda Khadija ta kawowa Sahura 'aiko sunyiurna ,mik'ewa Humaid yayi sbda lokacin sallah yayi na azhar Khadija ma sallar tayi daganan ta kwanta a katifar inna Humaid na dawowa yce zai koma kasancewar yanada ,aiyuka masu yawa . Washe gari Malam Adamu na yiwa su twins wasa yace ”ya Jalal lpy Lou ai matarsa ta aihu ma ,masha Allah mai aka samu cewar Adamu ,Khadija ce tace ”namiji ,sukad'an ta6a yira ,da wuri ta kwanta sbda da wuri zata koma Sahura ko tace ”zatabi Khadija babanta yaki yarda wai yayi mata miji karta biyewa samarin binni lol. Da komawarsu wani zazza6i ya lulu6e Khadija ,Humaid da yashigo yake tambayar yaushe ta dawo ya ganta kwance kamar wacce ta dad'e tana ciwo amai ne yake yunk'urin taso mata ,dagudu tayi toilet tana gamawa ta wanke fuskarta , Washe gari hospital suka nufa inda shi da kanshi ya aunata result ne ya fito ganin Khadija na d'auke da cikin wata d'aya yasashi zaro ido ,sbda 'a lokacin Dady da Abba watansu Uku ,magunguna ya had'o musu ita da yaran masu k'ara lafiya ita kuma tana yawan shan fruits farin ciki ya wanzu a wanan familyn sai dai muyi mata adu'ar Allah ya sauketa lpy . Takuce har kullum mom Islam nayi muku fatan alkairi,abinda nafad'a ba dai_dai ba Allah ka yafemana Allah ka shirya mana zuri'a alhamdulilh🥰🤝. 08141799224👍
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32