Chapter 12
Chapter 12
gani sai me yanzu mezan miki hak'ik'a Ramsy taji zafin hakan amma sai ta daure tace"dama maganar dinner ne shine nace kafin a tafi ne za'ayi kokuma sai ankai amarya, jin ya daka mata tsawa yasata zabura tace"daga tambaya saika nemi firgita ni ,to kasani ko a gidan mu babu mai yimin tsawa ka kiyaye ,ko kulata baiyi ba yaja waya ya kashe ,Khadija ko kuka takeyi dama tasan za'ayi hakan ,tafara magana da k'arfi tana cewa"daman wlhi na kawo wanan ranan saboda yaga 'an d'aura 'aure nazama mallakin shi shine ya keson wulak'anta ni."✍️✍️✍️. *MOM ISLAM CE*✍️✍️✍️.. *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 21_22 ____Kashe wayar yayi gaba d'aya dan bayason jin duk wani abu daya shafi Khadija saboda 'a halin yanzu wutar k'iyayyar ta ce take ruruwa 'acikin zuciyar shi, da misalin k'arfe tara na dare saiga motocin angwaye sun zo d'aukar amarya ,bayan angama yimata makeup dasu nasiha 'aka ce tafito su tafi , tunda taji haka ta k'ank'ame momy sosai tanajin zafin tafiyar da za'ayi da ita saboda tayi nadamar auran Humaid amma babu inda zatayi dole ta yarda kodan soyayyar da su momy suka nuna mata gashi dady harda bata mukullin mota,tana cikin tunani ne taji muryar momy na cewa , ina Khadija tayi share hawayen ta tayi kana ta gyara yafa gyalen ta ,jin alamun shigowar umma yasata dai_daita nutsuwar ta , bayan momy ta shigo ta ganta 'a zaune ta takure gefe d'aya , cikin azama tace"taso taso muje kiyi wanka kinga masu mota sun iso." Jiki babu k'wari Khadija ta tashi ta rufawa momy baya , bayan sun wuce toilet d'in momy ne momy tace "zonan suna shiga momy ta had'a mata wasu turaruka dakuma magun guna ta shige wanka , bayan ta fito ne momy tasa 'ayi mata makeup aka fito mata da kayan dazata sa , fans kuzo kuga Khadija kamar tauraruwa kowa sai mararin ganinta yakeyi, bayan sungama ne aka fito da ita tana sanye da swiss lace mai ruwan ganye ,fito da ita sukayi aka fara rangad'a gud'a Khadija kuka takeyi sosai kamar 'ranta zai fita, momy juyawa tayi saboda bazata iya ganin Khadija 'a yanayin kukan da takeyi ba ,wata kakar su Humaid ce tace" zo yarinya kiyi bismillah ki shiga ,haka Khadija tashige mota tana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare , tunda suka tafi momy ta koma bedroom d'inta tana ta sharar hawaye , ganin ai yau ranar farinciki ce a gurinta yasata murmushi da yau Humaid ya auri wacce take so adu'a tayi musu kana ta haura sama gurin dady ,samunshi tayi kwance yana duba wani file na business d'inshi yana ganinta yafara sakin murmushi k'arasawa tayi ta fad'a saman k'irjin shi tana shafa mai kai ,cikin jin d'ad'i dady yace ,lovely na menene ?"🤭momy ce tafashe da kuka tana cewa shikenan yanzu zan dena ganin Khadija 'a kusa dani." Gyara musu kwanciya dady 'yayi kana yafara share mata hawayen fuskar ta daganan'na rufo musu k'ofa ." *GIDAN AMARYA KHADIJA*👰. Zaune take tana ta gurshek'en kuka babbar k'awar ta Ramsy ce tazo kusa da ita tana cewa habba Khady maiyasa saikace ba 'auran soyayya ba ,share hawayen ta tayi batace komai ba ,dan a halin yanzu batajin zata iya wata magana tunda babu mai fahimtar ta, wanka ta sake yi ,kana suka k'ara yi mata make-up wanda yafi na d'azu aka sauya mata kaya zuwa wani material mai laushi suka feshe ta da turaruka masu k'amshi wow koni danaga Khady saida na yarda 'alk'alami na , shirin tafiya suka farayi ai kuwa Khadija na ganin hakan tafara gurshek'en kuka mai tsuma zuciya mai saurare ,zuciyar ta bata gama tsinkewa ba sai lokacin da taga sun yafa mayafi suna shirin fita ,durk'usawa tayi tana cewa kuyi hak'uri ku tafi dani ,nikuwa nace aure fa kikayi hhh yarinya ki gane aure yafi gaban wasa ." Haka tanaji tana gani suka wuce suka barta ,komawa tayi ta haye makeken gadon ta daya k'awata d'akin, kwanciya tayi can kuma tafara jin tsoro na shigar ta ,misalin 10:pm taji alamun shigowar mota, wani tsoron takuma ji tana 'adu'a 'a cikin zuciyar ta mik'ewa tayi ta lek'a ta window hango shi tayi shi kad'ai yana shirin fitowa daga mota, sanye yake da shadda mai kalar brown wace ta k'ara fito da ainihin kyan shi ,bayan ya rufe motar ne ya d'auko wata leda ya yi hanyar shigowa parlon ,Khadija ce ta koma ta gyara rufe fuskarta da mayafin jikin ta 'takoma tsakiyar gado ta zauna ,da sallama 'a bakinshi ya shigo zama yayi a d'aya daga cikin kujerar d'akin kasancewar bedroom d'in 'nata kujeru biyu ne ammafa sun k'awata d'akin ,bayan ya zauna ne yace"inkinyi ra'ayi zaki iya bud'e fuskarki ,wanan maganar ba k'aramin dukan Khadija tayi ba ,amma batace komai ba ,kuma d'ago kai yayi yakuma cewa to mekuma zaki 6oyemin bayan angama tallarsu a titi ,a firgice ta mik'e tana nuna Humaid 'da yatsa abinda bata ta6a yiba kenan ko musu dasu batayi amma yaukan ya kaita mak'ura ". Cewa tayi duk abinda ka fad'a 'a kaina nayi shiru ban kulaka ba yanzu kuma ka sake jifana da wanan mumunanr kalmar ?" to wallahi bazan lamunta ba ,kafin ta k'arasa ya wanketa da mari jiki na rawa tace"kozaka kasheni wallahi sai Allah ya sakamin ,wurga mata ledar yayi ya fice a fusace , kwanciya tayi tafara gurshek'en kuka gashi babu mai rarrashin ta. Misalin k'arfe 11:pm ta mik'e ta daddafa bango saboda mugun ciwon da kanta yakeyi bata gani sosai,toilet 'ta shiga ta wanko bakinta tazo ta zauna tana son cin abinci gashi matsanancin ciwon kai na damunta ,ba'a fushi da 'abinci ,janyo ledar daya wurgo mata tayi tana bud'ewa taga mutuniyar tace wato kaza gasashiya da yogurt aiko tafara yagowa tanaci tana shan yogurt d'in ,duk girman kazar saida tayi rabi ,alokacin'ne taji ciwon kan ya ragu ba kamar da ba ,mik'ewa tayi ta cire kayan jikinta ta sauya izuwa sleeping dress sosai kayan sukayi mata kyau ,bayan tayi adu'ar kwanciya bacci ,tana kwanciya bacci mai nauyi ya tasheta tare da mugayen mafarkai masu firgitar wa, washe gari tunda tayi sallahar asbha ta koma bacci ba ita ta farka ba sai misalin karfe 9:am lokacin ma jin alamun 'nocking d'in k'ofa ne ya tayar da ita". Zumbulelen hijab d'inta tasa kana ta nufi k'ofa ,tana fita parlor takuma ji ana nocking cikin azama ta isa k'ofar ta bud'e ,ganin yar aikin momy ce yasa Khadija washe baki tace"yaushe kika dawo ne Ummi?"Ummi cikin jin dad'i da tarbar da Khadija tayi mata tace"yau kwanana d'aya ,Khadija ce tace"to kishiga mana kamar bak'uwa ,shiga Ummi tayi bayan ta mik'awa Khadija abincin da momy tabayar akawo musu tuwon shinkafa ne miyar shuwaka wacce taji nama kamar zasuyi magana kai dakaga tuwon kasan zaiyi dad'i ,jere kulolin tayi a dining ta dawo ta zauna ,kusada Ummi ,tambayar ta tashiga yi 'inasu momy da yaya Jalal 'lafiya Lou tace"daganan Khadija ta kunna musu kallo ,Khadija ce ta mik'e tace Ummi ki jirani yanzu zanyi wanka in fito ,Ummi data tuna da kashedin da Momy tayi mata yasata cewa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32