Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,178 words 0 views Progress saved
Download Book

muje tare ,hannun dady ta rik'e tana kuka suka fita , duk wanan hayaniyar da girgizar duk a part d'in Khadija yake faruwa hatta k'ofar ma girgiza takeyi kuma a bud'e take ,dady na shirin lek'awa momy ta rik'oshi tace muje mu nemo malamai dan Allah ,hankalin dady a tashe damu warshi wane hali baiwar Allah take ciki marainiya ,kutsa kai yayi momy na tsaye ya wuce ,kwance ya sameta d'akinta duk ruwa mai had'e da jan abu mai kamada jini sai wasu surutai takeyi ,kafin dady yace ”bismillah kawai aka d'aukeshi aka gwara da jikin bango ,ihu momy takeyi iya k'arfinta gadai khadija a kwance shikuma dady ,kowaye yayi mai haka oho , mai gadi ne da driver sukayo cikin gidan a tsorace ,momy babu magana sabda kuka yaci k'arfinta saidai nuni da hannu ,hango dady sukayi a mak'ale a jikin bango shi bai sauka ba shikuma bai yi sama ba, wani hayaki ne ke fitowa amma Khadija na kwance tana bacci ,driver ne yace ”anya babu shed'anu a lamarin kafin ya rufe baki yaji an wankamai mari ,ganin basuga kowaba yasa mai gadin da driver da momy suka arce da gudu , d'akinta momy ta koma ta d'auko wayarta ta kirawo Jalal ring d'aya ya d'aga yana sallam momy ko amsawa batayi tace ”Jalal.ka kirawo mai ruqyya dan Allah dadynku tana kuka to yace kashe wayar momy tayi tana adu ar datazo daga bakinta , bayan 30minutes sai gashinan shida wani babban malami sun shigo ." Gai sawa sukayi da momy daganan tayimai bayanin ciwon Khadija dakuma halin da dady yake ciki ,ruwa ya buk'ata domin alwalah bayan ya idar da alwalar ne yace ”a nunamai d'akin ,momy ce ta shige gaba itada Jalal shikuma malamin na baya da Qur'ani a hannunshi ,da hannu momy tayimasa nuni da d'akin ,lek'awa yayi ya hango dady jingine a jikin bango shi baya k'asa auxubillahi yace ” a lokacin da yake karanta suratul bak'ara ,jikin dady ne ke jijiga yana wani gurnani tsananta adu'a malamin yayi , Allah cikin ikonsa saiga dady ya fad'o yana tangad'i ,malamin ne yace ”asamu yayi wanka kuma ya kwanta ,kan Khadija aka koma daketa bacci ko motsi batayi adu'oli iri _iri malamin yayi amma har yanzu shiru ,d'akin sai fitarda wani hayak'i takeyi mai ban tsoro." Fitowa malamin yayi yana yarfe gumi yace ”zanje in dawo ,to su momy sukace daganan suka rufo k'ofar khadija ,da fitar malamin gidan duka ya kaure da kururuwa mai firgitarwa daga momy har Jalal sun kasa koda motsi ne ,dama dady bai tashiba tunda yai wanka ,jin girgizar tayi yawa yasa momy shiga bathroom d'inta d'auko buta tana shirin zuba ruwan alwal wasu abubuwa tagani na ban tsoro hakan yasata ficewa tana salati Jalal ne yace ”momy to yanxu ya za'ayi ¿ jin momy tayi shiru yasashi kallon inda take kallo ,wata halitta ce mai abin tsoro da girman ta ya zarce tsawon d'akin a sunkuye take tafiya ,idanuwan momy suk k'afe bataji bata gani ,kafin wanan abin ya iso Jalal cikin tashin hankali ya cici6i momy yai da ita d'aki suna gudu halittar na binsu Allah yabashi ikon rufe k'ofar ba tareda wanan halittar ta shiga ba." Ruwa yadinga yayafawa momy amma shiru ,a karo na biyu ne ya bud'e ma dai _dai cin fridge d'inta ya ciro ruwan sanyi yana yayyafa mata cikin sa'a ta mik'e tana salati, sallamar malam sukaji babu wanda yai k'ok'arin tashi malamin yace ”yanaga babu kowa Jalal ne cikin d'aga murya yace ” kaje d'akin mara lafiyar ,gamunan momy na ce babu lafiya ,shigewa d'akin malamin yayi daganan yafara adu'oi yana tofa mata yanayi yana tofa mata wata atishawa tayi mai k'arfi wacce tayi dai dai da tashin dady daga bacci ,momy take kira iya k'arfinta ,momy najin muryar Khadija ta fice da sauri tana cewa yaushe rabon da daughter ta kirani, fara'a ce ta baiyyana a fuskarta tashiga d'akin zaune ta sameta ,da shigar momy Khadija tace ” momy maiya faru ne babu komai momy tace ”daganan malamin yace ”hajiya muje parlor inyi miki bayani OK tace suka wuce Khadija tashi tayi ta shiga wanka ,ganin duniyar takeyi kamar sabuwa.*LADIDIN KAUYE* Page 53 & 54 Malamin ne yace ”dole sai kun kiyaye da shan maganinta to momy tace ”yabasu adu'oi da zasu dingayi a gidan , momy ce tacewa "Khadija ta shirya suje airport itada Khalel , cikin sauri ta nufi d'akinta dan yanzu burinta bai wuce taga mijinta ba , Jalal ne yashigo yana k'walawa khadija kira , fitowa tayi cikin wata shiga mai d'aukar hankali , less ne pink a jikinta sai gyalenta fari takalmi fari jaka pink and wait, wow kuzo kuga Khady , suka shige mota zuwa airport , mutane ne keta saukowa , hango wani had'ad'en saurayi tayi mai kamada Humaid ,tunani tafara kodai humaid ne ?" sanye yake da bak'ar rigar sanyi my adon flawoyi gashi yayi haske sai dai ya rame sosai , da zuwanshi yayi hugging gimbiyarshi , shidai Jalal na gefe yana zaro ido , sunkuceta yayi ya rungumeta yana yimata rad'a a kunne wanda nima banji me suke cewa ba ,Jalal ne yace ”wato ni an manta dani ko ?"dariya Humaid yayi ya doki k'afad'arshi yace ”am sorry kuna raina dukkan ku , mota suka shige ,Humaid da Khadija a Back side ,Jalal yana gaba yana driving,da isarsu gida sukaci karo da anshirya walima gagaruma gurin ya kawatu da flawoyi masu wuta suka shige ciki ." funny & love story 55_56 Dady da momy suka zauna a kujerun da aka zagaye gurin suna adu'a Jalal ne yace ”bari a yanka cake sai 'intafi gida ,momy ko dariya takeyi farinciki fall zuciyarta ,durk'usawa Humaid yayi ya gaida dady yaje ya gaida momy ya dawo kusada Khadija ya zauna sunci sunsha dan abinci ma daga hotel aka kawo ,misalin k'arfe biyar dady yacewa Humaid ya d'auki matarshi ya wuce ,wanan karon dai Khadija batayi kuka ba, sai da sukayi sallahr isha'i sanan suka d'unguma zuwa gidansu ,hira sukeyi jefi jefi ,da isar su gidan sabon mai gadin da dady 'ya sa musu ya wangale gate d'in yana yimusu sannu da zuwa ,da shigarsu yai parking a ya fito yana mai yiwa Allah godiya ,itama fitowa tayi suka nufi cikin gidan ,kowannensu d'auke da sallama a bakinsu ,da shigarsu parlor suka yada zango Humaid ne ke dariya yana kallon Khadija yace ”baby kingaji ko farr tayi da idonta tace ”yaya mungaji dai cikin sigar tsokana yace ”to gafa tsaraba na kawo miki dan nasan bakya bata kunya tasowa tayi tazo kusa dashi ta zauna wata leda ce mai kyau ya ciro mata gasashiyar kaza ,murna takeyi tana godiya Humaid ne yace ”to yanz mekuma kikeso ,rufe fuska tayi tace ”nakasa tashi d'auko ruwa zansha yana dariya ya mik'e ya d'auko ruwan ,bayan ta cika cikinta ne humaid yace ”to muje muyi alwala yaukam 'zamuyi nafila a sa'a lol." Hhh wata nafilar aka kumayi akayi adu'oi sosai daganan 'naga Humaid ya sunkuci Khadija yana harara ta ,garin gudu har nakusa fad'uwa 'asbha tagari amarya da 'ango. Bayan komai ya lafa ne na hango Khadija nata kuka tana cuno baki ,Humaid da fitowarshi daga wanka kenan yace ”haba baby kiyi shiru mana ya marai raice murya

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32