Chapter 15
Chapter 15
waje gurin motar shi , ya tayar ya mik'i hanya". Tanajin fitarshi ta fito da gudu tayi d'akin shi ganin kayayyakin daya siyo tayi zaro ido tayi tace"shiyasa ko ya nemi abubuwan dana d'ebo tabb aikuwa saina kwashe wa in an ma ,fara jidowa tayi tana haki ta kwashe kayan abincin dukka harda su carton d'in maltina dana madara dakuma k'wai duka ta kwashe tana dawowa taga wani kayan ganin jikin kwalin anrubuta golden ai kawai ta loda takai d'aki a ranta ko tana cewa shikenan 'na huta da girki ko lemon kwalba ma ya isheni, kitchen taje ta d'auko tukunya da wuk'a dakuma mangyad'a da kayan miya tadawo d'aki tasa key . Misalin k'arfe biyar na yamma yadawo a gajiye ya shige toilet ya watsa ruwa yana fitowa kwai yaji yana sha'awar shan golden beer zuwa inda ya 'ajijiye kayan yayi ganin baiga komai ba yasashi zaro ido ,cikin kunar 'rai yace "wato wanan tsinanniyar bacin zina har giya takesha?" zama yayi a bakin gado yadinga girgiza k'afa yana bala'i arayuwa bayason a d'auki abinshi ba'a tambayeshi ba ,cikin masifa yafice daga d'akin 'nasa yana zage zage kuma ya kudurta 'a ranshi ko k'ofar zata 6alle yau saiya ci uban Ladidi ,yana zuwa yaji kamar kullum k'ofar a rufe take da key dukan k'ofar yakeyi kamar mahaukaci amma tak'i bud'ewa itako tana tsoron karfa ya 6allah k'ofar nan yazo yakusa kasheta dan yau kamar yasha ya bugu,shigewa cikin drower tayi tanata zaro ido kasancewar akwai gurin sa sak'ata ta ciki kuma tanada zurfi ba lallai mutum ya bud'eta da garaje ba....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 27_28 _____Cikin k'arfi ya bigi k'ofar har saida ta bud'e tsayuwa yayi yana maida nunfashi kasancewar k'ofar bata ra'go bace ,kutsa kai yayi cikin d'akin yana haki yana cewa inakike dan ubanki yau saina karyaki ,dube dube yakeyi amma ina baiganta ba bud'e toilet yayi nanma bata nan rik'e k'ugu yayi kamar mace yanason yaga ta inda zata bullo amma inna ko alamun ta baigani ba, wata muguwar tsawa ya daka, Khadija dake cikin kaya saida ta firgita 'amma dayake tasan tayi lefi ko k'ok'arin guduwa batayi ba , ficewa yayi da gudu yaje ya d'auko wani key a d'akinshi yazo ya kulle k'ofar a tunaninshi ta fice yawo ne, yana fita ta fito.daga ma6oyar ta sai gumi take sharewa ,zuwa gurin kwalayen data d'ibo tayi ganin golden beer dama tasa biyu a fridge ta bud'e ko karantawa batayi ba ta hau sha jin zak'i zak'i yasata lumshe ido ,tanagama sha ta wurgar da gwangwanin ." Luuu tafara gani wata zabura tayi tafara maganganu tanacewa wai naga kamar duniyar tak'ara haskene tabb naga ta kaina yaukuma gashi goma na dare amma basai ankunna fitillah ba tafara layi tana surutai ,gyatsa tayi tace"sweet lemu kamar nasha zuma kai firig zonan kabud'e in k'ara ,ganin dai fridge bashida niyar zuwa yasata mik'ewa tana layi ta bud'e zata d'auka tafad'i k'asa tana cewa to wane mugunne kuma yake k'ok'arin ganin bayana?"can kuma tasa dariya tace"ni wallahi nagaji da wannan duniyar kuzo ku kaini duniyar ku. Jin alamun bud'e k'ofa yasata zubawa da gudu yana bud'e k'ofar yad'n matsa yana so ya kamota aikuwa ta fice da gudu tayi kitchen tasa sak'ata lokacin tafara dawowa hayyacin ta ,baibi takan d'akin 'nataba bare yaga 'abinda tasha hannu ya buga'a bango yanacewa kokuma 'ajanun k'auye sun shafeta ne shiyasa take 6acewa?"can kuma ya mik'e yayi d'akinshi jin ana kiran sallahr mgrib , bayan yayi alwala ne ya kulle gidan ta baya ya wuce masallaci ,Khadija najin fitarshi taja jiki tana tafiya tana layi tayi d'aki ,ganin gwangwanin madara yasata bud'ewa ta saida ta shanyeta tass tukun ta kuma kwanta 'a gurin bacci mai nauyi ya d'auketa ... Jin wani sanyi mai kamada ruwan k'an k'ara ya tashe daga baccin da takeyi duka taji ko ta ina tarasa waye mai dukan 'nata ihu takeyi 'iya k'arfinta 'amma innaa bbu halin tashi bud'e idanuwanta dasukayi mata nauyi tayi ganin Humaid a tsaye kamar wani soja yasata cewa to Allah ya isarmin mugu kawai buge bakin yayi ya cire bell d'in wandinshi yana dukanta ta ko ina ganin babu mai ceton ta yasata juye juye tananeman abinda zata buga mai ,ganin babu komai yasata dai daitar saitin wandonshi ta murd'e gabanshi ta zura da gudu wani wahallalen k'ara yasa mai wuyar fassara wa yarasa maiyakeji ,jiyayi kanshi na juyawa rike da mararshi ya fad'i k'asa sumamme, Khadija ko kitchen tanufa ta fere doya ta wanke ta dafata daganan ta soya da mai tanayi tanacewa kafin ya tashi naci nak'oshi mugu kawai ,tana gamawa ta soya miyar k'wai kasancewar akwai kayan miya batasha wuyaba seda taci ta k'oshi dak'yar take iya tafiya da ruwan gora 'a hannunta ta k'arasa d'akin ,ganinshi kwance yarik'e gurinda ta murd'e kumfar yawu na zuba 'a bakinshi yasata rugawa d'akinshi da gudu cikin tashin hankali wayarshi tagani a kan gado duba number tahauyi ,ganin doctor Umar yasata danna kira ring d'aya ya d'auka 'a zatonshi Humaid ne ,jin muryar mace yasashi cewa madam barka dai, cikin firgici Khadija tace "Umar dan Allah kazo ka duba Humaid dan Allah kayi sauri ko motsi bayayi ,a tsorace Umar yace " karki damu ganinan zuwa to tace"kawai domin hankalinta yafi na 6arawo tashi. Ba'a d'au wasu mintuna ba saiga horn d'in motar doctor Umar yana zuwa ya nocking d'aga murya tayi tace"shigo doctor ,da y'ar jakarshi a rataye ya k'araso yana haki'i tsabar kukan daya ku6ce mata bata iya magana ba nunamai d'akin da Humaid yake kwance tayi , shigewa yayi da sallama Doctor Umar ganin halinda Humaid yake ciki yasashi rik'e kai yana cewa innalilahi wa innailahirraji'un ya Allah help me,idonshi cike da hawaye ya kinkimi Humaid kamar gawa yasa 'a mota cewa Khadija ta kulle gidan ta biyoshi yayi to kawai ta iya cewa kasancewar gani takeyi kamar Humaid ya mutu ne." Rufawa doctor Umar baya tayi dole ta shige gidan gaba saboda 'an kwantar da Humaid a back side ,tun doctor Umar na hanya yake waya akan a tanadar musu d'akin saboda Humaid babu lafiya kuma yana buk'atar temakon gaggawa kasancewar hospital d'in akwai nisa saida sukayi tayi maid'an 'nisa sannan suka iso a keken tura marar lafiya 'aka turashi direct d'akin da 'aka tanadar musu suka tafi likitoci biyar ne akanshi amma kowa sai share gumi yakeyi ,itako Khadija sai safa da marwa takeyi a harabar asibitin ,likitoci sun shafe wajen awa 1 hour suna bincike akan suma samu nunfashin ya tsaya 'abin ya citura sai da suka kuma shafe mintuna talatin sanan sukayi sa'a ceto rayuwar shi ,ba'amayi batun gurinda 'akayiwa illa ba tukun ganin ya bud'e ido yasa likitocin cewa Alhamdulilh Allah mun gode maka ,jin ana hamdalah yasa Khadija saurin k'arasowa tana kuka tana ganin Humaid ya bud'e ido takama dariya tana yiwa Allah godiya. Likitocin'ne sukace to yanzu saimu koma kan inda yaketa nunawa tun d'azu a kunyace Khadija ta fice daga d'akin ganin ana k'ok'arin duba gurin bayan sunyi y'an bincike ne suka gano cewar yasami matsala 'agurin kuma indai ba fita dashi k'asar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32