Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Ladidin Kauye Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

to nimafa tafiya zanyi dan momy na jirana ,badan Khadija taso tafiyar Ummi ba 'amma tayi mata godiya sukayi sallama . Humaid ne yafito parlor lokacin 11:am na safe sanye yake da wani lallausan yadi mai ruwan coffee kasancewar shi farine ba k'aramin kyau yayi ba ,shafa bak'ar sumar datayi luf a kanshi yayi can kuma ya ciro waya kamar mai jiran wani abu ,Khadija ce tafito tana sanye da doguwar 'riga pink mai adon ston black tayi rolling kanta da mayafin rigar ,tana fitowa Humaid yakai dubanshi gareta cikin zuciyar shi kuwa ji yakeyi kamar yaje yai hugging d'inta tunda matsayin da 'a gurinshi yayi kawai sai ya had'e rai ,ya dubeta tana neman gurin zama yace"keee!!saida gabata ya fad'i tashi ki gyaramin d'akina baki iya gaisuwa bane ?"na iya tace"a tak'aice ,Humaid ne yace "to kullum zaki dinga zuwa gaisheni ko sau goma zan fita kuma in dawo ,to kawai tace" ganin yayi hanyar dining ne yasata k'arawa da gudu ta kwashe kulolin tayi d'akinta dasu ,key tasa ta rufe k'ofar.....✍️✍️✍️. *~MOM ISLAM CE~* *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 23_24 _____Saida ta tsince naman kaff tukun ta ci tuwon bayan tagama cine ta fito da ragowar parlor, bata lura da mutum a parlorn ba direct ta wuce dining ,saida ta 'ajiye kular ta hango shi yana kan doguwar kujera maicin mutun uku ,zata ruga da gudu ya daka mata tsawa yace"kee!!zonan zataci gaba da tafiya ya mik'e da gudu ya janyota ya wurgata gefe kana yace "wuce ki dafamin dambu,zaro ido tayi kana tace"me kuma mai suna haka?". " Cewa yayi ubanwa zaki rainawa hankali ¿"cikin jin tsoro da fargaba tace"ni ba rainama hankali zanyi ba ,gani 'nayi ban iya ba shiyasa nake tambayar ka, tsawa yakuma daka mata saida ta tsorata yace"kin zo bariki kin manta da shan garin kwaki ko ?"to kitashi ki goge gidannan kuma kar in dawo insami akasin hakan, haka ta shiga bedroom d'inshi tafara wanke toilet sanan ta dawo gyara bed d'inshi tayo kan TV da sauran kayan kallon ta gogesu kana ta dawo tafara shara tana gamawa tayi mopping, bayan ta gama ne kawai tad'an kishingid'e a gefen bed' d'inshi saboda wata gajiya da tayimata sallama ,bacci ne mai nauyi ya kwasheta 🤭nikuwa nace"anci an k'oshi zaki gane, jin shiru har tayi 1 hour bata fito ba yasashi kashe kallon daya kunna kana ya wuce bedroom, samunta yayi kwance tayi d'ai_ d'ai ,zaro ido yayi kana yafara tunanin irin muguntar da zaiyi mata." D'auko alurar malaria yayi wacce yake ajiyewa 'a gida saboda koda wata matsalar zata taso, bayan yagama zuba magungunan dayasan Khadija zata bada labari ,komawa yayi kusa da ita yana k'are mata kallo can kuma yaji muguwar tsanarta tana kuma baiyyana cikin zuciyar shi. Tunda 'akayi bikin Humaid 'da Khadija babu wanda yayi k'ok'arin kiran su momy gashi yau har kwana biyu da wuni saidai momy na 'aiko da 'abinci kullum ,amma hakan bai sata kwanciyar hankali ba , kiran Jalal tayi a waya yana d'auka tace" dan Allah kazo inason ganinka . "Cewa yayi momy lafiya dai ko ?"lafiya tace masa daganan ta kashe wayar ba'adau lokaci mai tsayi ba saiga Horn d'in motar Jalal nan kasan cewar baya gida ,yana shigowa tun daga parlor yafara k'walawa momy kira yana cewa momy gani na iso, sako tayi daga matatrakar dake tsakiyar d'akin tace"gidan Humaid nakeson kaje inasan kadubo su ko lafiya ,itadai Khadija nasan batada waya , dariya ce taso ku6ucewa Jalal ganin damuwa k'arara 'a fuskar momy sun kuyar da kansa k'asa yayi kana yace" momy lafiya suke saboda da babu lafiya 'ai dakinji , momy ce ta d'ake tana masifa tana cewa yanzu ka nuna ban isa dakaiba kenan ko?"to walhai tun wuri kaje ka dubomin su kokuwa ranka ya 6aci !!Dady dake saukowa daga bene yace"karka kuskura kaje gidan su , nagaya maka d'ago kai momy tayi tana kallon fuskar dady _dady dake magana cikin bada umarni yace "ka koma gurin aikin ka, to Jalal yace" batare da yakalli k'wayar idon momy ba." "Momy ce takalli dady can kuma tayi k'asa da murya tace"haba habiby maiyasa kayi hakan?" tana dad'a matsowa kusa dashi , dady ne ya kawar da kai alamun maganar da momy tayi d'azu nazuwan Jalal gidansu Humaid ya 6atamai rai, k'arasawa kusa dashi momy tayi kana tace"haba mana mijina banason fushinka ta kuma marai raice fuska kamar zatayi kuka tace" please afuwan habiby, hugging d'inta dady 'yai tare da janyota jikinshi a lokacin da yake k'ok'arin zama akan d'aya daga cikin kyawawan kujerun,dasuka haska parlorn ,dady ne yake rad'awa momy a kunne yana cemata walhai Aisha saboda salonki dakuma siye zuciyata da kyawawan kalamanki yasa nak'i k'aro aure amma badan hakaba da yanzu matana hud'u . Tunda ya gama had'a komai ya bud'e mata gefen hanunta jitayi abu na shigarta kamar'ruwa kasancewar ko a hospital ne kowa nason alurar shi saboda batada zafi,haka yayi mata 'alura tana bacci ,jin alamun kamar ana tsikarin ta yasata saurin motsawa, Humaid na ganin haka ya koma parlor saboda karta gane ,tun tanajin abin kad'an har tazo tanajin k'ai k'ayi sosai, inta Sosa k'afa saitaji a kunne inta sosa kunne saitaji a baya ,haka tadinga susa kamar mahaukaciya ganin lamarin yafi k'arfinta yasa tafara ihu tana tsalle tana cewa wayo Yadikko, da gudu ta fice a d'akin tayi d'akinta tana tsalle ,rasa 'abinda yake yimata d'ad'i tayi ganin batada mafita yasata d'auko farar hoda ta cire kayan jikinta duka ta shafe ko ina na jikinta ,ganin abun babu sa'a yasata cewa yaya Humaid!!, "Kazo ka temakeni walahi narasa inda na kwaso k'ai k'ayi ,shiko Humaid ganin tana magana tana soshe _soshe yasashi sakin killer small yace" to yanzu mekikeso inyi miki nikuma ?"kije wanda yafara ganin komai ,ya baki magani ,tana susa tace"bangane ba sokakeyi kacemin 'ni mazinaciya ce?!!! menayi ma dahar zaka k'ullamin wanan mummunan sharin oho yace"daganan yabarta tana soshe ssoshe. Tana kuka tana susa wani gurin har yayi rud'u rud'u tsabar susa tausayin da tabashi ne yasashi shigowa ya mik'o mata magani k'waya biyu yace"ta shanye duka ,babu musu ta k'ar6a tanasha ba'a d'au lokaci masu tsayi ba ,bacci ya kwasheta , said a ya koma d'akinshi yadinga dariya yana k'arawa saboda ya 'ajiye CCTV a bedroom d'inshi kuma bakowane zaisan akwai CCTV a d'akin ba ,kusan k'arfe hud'u na rana ta mik'e had'e da salati a bakin ta ,wata masifaffiyar yunwa takeji mik'ewa tayi ta nufi kitchen tana shiga taji k'amshin indomie jollof ,bud'e murfin tukunyar tayi ganin kayan k'wad'ayin da 'aka samata yasata zaro ido k'wai ne dafaffe sai karas ,abinka da gidan kwad'ayi ai dandanan taji ranta ya biya tuno mai girkin tayi wato Humaid tsaki tayi kana ta sunkuci tukunyar tayi d'aki ,bathroom ta shiga seda tayi wanka tayi brush sanan ta fito ta zauna 'a gaban dressing mirror tana shafa mai tana wak'a tunowa tayi ai bata kulle k'ofa ba ,dagudu ta mik'e taje tasa key tadawo taci gabada Kwaliya bayan ta d'au makeup mai kyau ta ciro shadda bugaggiya mai ruwan coffee tasa takuma ciro bra da pant da warwaro da

Table of Contents

Chapters

32 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32