Chapter 98
Chapter 98
tsantsar fushi da tsana da zazzafan ƙiyayya ta fara mgna cikin ɗaga sauti tace. "Hegen yaro mai idanun mujiya, Ni kakeyiwa wannan iskancin dan kan uwar..!". Kasa ƙarisa zagin da tayi nufin yi tayi jin yana cewa. "Kan uwarki ko? Ki ƙara sa mana kikaga ikon wanda ya hana mata gemu ya baiwa maza! Maza tashi min kan kujerar zama tunda ba wancan jiɓeɓɓen tsohon akun bane seyota". Wani irin zabura Baba Nasiru yayi tare da ɗaga hannu zai kifeshi da mari, kamar a mafarki yaji an riƙe mishi hannunshi da sauri ya juyo. Ido ya zaro cike da mamakin ganin wanda ya riƙe mishi hannunshi cikin tafasar zuciya da ƙuna yace. "J....." By *GARKUWAR FULANI* Cikin wani zare ido na masifa yace. "Jalal ni ka riƙe wa hannu". Shima idon ya zare tare da cewa. "Ba iya rikeshi kaɗai zanyi ba, in dai zai taɓa lfyar ɗan uwana a gaban idona, datseshi zanyi gaba ɗaya in wurgar". Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da yarfa hannunshi. Wani irin asirtaccen murmushi Barrister Kamal, yayi tare da kallon ɗan shi Sulaiman hannunshi ya dunƙule ya jinjina wa Sulaiman ɗin. Kana suka koma suka zauna bisa kujera. Shi kuwa Jabeer hannun ya nunawa Gimbiya Saudatu alamun ta tashi. Mirtsitsi tayi tare da gyara zamanta. Wani irin firgitacen tsawan da Jalal ya danna matane yasa, ta miƙe tsaye ba tare datasan ta miƙa ɗin ba. Cikin ƙasaita Jabeer ya baza tattausar al'kyabbar jikinshi, Kana ya matso ya zauna bisa kujerar ƙafarshi ɗaya ya ɗora bisa ɗaya. Gyara hiramin kanshi yayi tare dayin gyaran murya kana ya kalli ƙannen mahaifin nashi kauda kanshi yayi ganin yadda suke wani irin cika da batse sun cika sunyi tamtsan da fushi. Ita kuwa Gimbiya Saudatu zama tayi a kujerar dake kallon tashi kujerar. Itama ɗaura ƙafa ɗaya tayi kan ɗaya. Cikin iya tijara ta watso sabbin jaridu gabanshi. Jaridar bankaɗa da kuma kamfanin jaridar hantsi wato leƙa gidan kuwa. Murmushin muguntan tayi tare da cewa. "Ga sakamakon sa insa da kayi dani jiya, na yau kuma shima yana nan tafe. Nayi maka murna darajar labarin ya kai matsayin da shine a shafin forko na jaridun". Da sauri Jalal ya sunkuyo yasa hannunshi ya ɗauki jaridar banƙaɗa. Jiki na tsuma ya ɗago ya kalli Gimbiya Saudatu cikin tashin hankali yace. "Wannan ƙarya ne, da babu jahilin da zai yarda dashi, wlh bazaku taɓa cin nasara ba." Hankali a tashe ya miƙawa Haroon jaridar tare da cewa. "Ya Haroon gani zancen banzan da aka rubuta kan hotunan Hamma." Da sauri Haroon dake sauƙowa kan stpes ɗin sauƙowa falon daga dinning area, ya ƙaraso. Hannuyasa ya amshi jaridar. Wani irin azabebben zufane ya fara keto mishin ganin abinda aka rubuta a jikin jaridar. Jin jikinshi na rawane ya sashi zama kusa da Sulaiman. Ummi kuwa dake tsaye a dinning area tana haɗawa. Jafar abin da zaici, gaba ɗaya ido ta zubo musu cikin taraddadin me aka rubuta. Ita kuwa Gimbiya Saudatu wata iriyar shaƙiyiyar dariya tayi tare da cewa. "Ya haka dai ƴan kanzagi, ku bawa shi uban gidan naku, jaridar yage me aka rubuta, daga nan sai inga bakinshi da baya mutuwa da bada amsa ko zai iya cewa wani abu." Baba Nasiru da Baba Basiru, ma fuska cike da farin ciki suka zauna. Laminu kuwa miƙewa tsaye yayi tsakiyar faffaɗan falon cikin ɗaga sauti yace. "To tunda bazaka iya bashi ba, bani ni in karanta mishi." Yana ƙarishe mgnar yasa hannunshi ya amshi jaridar. Cikin ɗaga sauti ya fara karanta rubutun dake rubuce a ƙasan hoton da gefe da gefenshi. "Abun kunya, ya baiyana jikan sarki Nuruddeen Bubayero ɗaga Habibullah, Yayiwa ɗiyar Fulani fyaɗen da yasa. Hanun Sarki Lamiɗo ya kama hannun Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero wanda yake limamin masalacin ƙofar sarki ya miƙa shi ga hukumar addini musulunci. Gashi anayi mishi bulalin haddi kamar dai yadda Musulunci ya wajabta. Wani irin murmushi Jabeer yayi, hannunshi yasa ya shafa tattausan gemunshi. Cikin rashin karaya ya kalli Haroon cikin nitsuwa yace. "Ɗan wannan abun ne kuke zaton zai kashe wannan bakin nawa da yake rayuwa da ambaton Allah!? Shin ko kun mance tsawon shekaru da dama ana fataucin rufe bakin Ya Jafar, shima har yau baku samu nasarar hanashi ambaton Allah ba, Duk sharrinku ya zame mushi al'khairi, tunda baya wani motsi ba tare daya kira sunan Allah ba, ikirarin ku na ya zauce, ya tabbata kune zautattun". Sai kuma ya ɗan kalli Gimbiya Saudatu, murmusawa yayi tare da cewa. "Baki nafa bazai mutuba sai in nufashina ya bar jikina, batun shiga ɗakin sirri kuma, nifa wannan abin da kuketa haƙilo a kai ba wani baƙon abun bane a wurina. sarauta a cikin jin jikina yake." Sai ya kuma juyo ya kalli Haroon da jikinsa yayi la'asar da lamarin su, miƙewa tsaye yayi tare da cewa. "Haroon wai ɗan wannan makircin nasune ya kashema jiki. To kontar da hankalinka. Ni nan Muhammad Jabeer ƙi gudune sa gudu. Tun kan suyi tunanin yin abu a kaina na nazarci abun." Juyowa yayi ya kalli Baba Nasiru cikin tsareshi da ido yace. "Kaje duk inda ake saida jarudu ka bada farashin one million akan ko wanne jarida kaga in za'a fito maka da wannan jaridar, in bada wannan ƙwaya ɗayar kaga dai itama kuma gata a gabana." Cikin tarin mamaki suka zuba mishi ido. Shi kuwa gaban Laminu ya isa cikin isa ya miƙa mishi hannunshi tare da cewa. "Bani shi nan". Cikin tsananin tsoro da firgici ƙarara. Jiki na rawa Laminu ya miƙa mishi. Sabida kwarjin Jabeer ya mishi nauyi a idonshi ya kuma san artabu dashi ba daɗi. Ita kuwa Gimbiya Saudatu wani murmushi tayi mai cike da taraddadi da al'hini da nazarin yadda zataga bayan wannan yaron mai bakin tsiya. Jaridar gabanta ta miƙa mishi. Kanshi ya girgiza tare da kaɗa mata yatsarshi manuniya cikin rashin tsoro da ƙasaita yace. "Ba kifa kai matsayin da zaki nuna min wani abin da idanuna basu rigaya sun ganiba ko basu san dashiba domin ke a makance kike rayuwarki, Ni kuwa nan da kike gani idona buɗe suke ras. Ita wannan itace tayi bayanin abinda ya faru na gsky a Rugar itace tai bayanin cewa bulalin shaɗi akayi min bana Haddiba to sai me kuma!?". Shiru sukayi gaba ɗayansu. Kowa da abinda yake nazarta a ranshi sai bugawar da zuciyoyinsu keyi. Buɗa al'kyabbar jikinshi yayi tare da kuma haɗe ta cikin fillanci yace. "In kun gama ihun ku ficemin daga Side ɗina Dan ba haɗamu akayi ba. Kuma ku sani (MOH ALLAH WUJI FURƊATA)." Yana faɗin haka ya juya ya nufi falonshi. Ita kam Gimbiya Saudatu ta cika tayi maƙil. Baba Nasiru da Baba Basiru kuwa, A kufule suma suka fita. Haroon kuwa ido ya zuba musu. Barrister Kamal kuwa murmushi yayi mai tarin ma'anoni kana shima ya fita Sulaiman na biye dashi. A hanyarsu ta komawa side ɗinsu ne, Gimbiya Saudatu ta kalli Laminu cikin takaici tace "Banza kawai me tsoron zuci me dan ya matso kusa dakaii ka wani firgita ka razana har ɓari jikinka keyi ka miƙa mishi jaridar, da zamu iya kaita a tallata". Wani irin wawan ajiyan zuciya Laminu yayi tare da cewa. "Uhummmm Umma kenan wato, fa duk wannan kumfar bakin da kikeyi abinda yasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185