Skip to content

Chapter 100

Chapter 100

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Sittin dan kulawa da so. Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake. Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai. Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura. A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman. Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi. Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin ɗan ƴar uwar tata ɗa mafi soyuwa a gareta sama da ƴaƴan data haifa a cikinta ma. Yau kwana biyar da faruwan abun. Sosai jikinshi yayi ras. Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo. Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba'ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin. Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani. Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes. Yakanji kamar ya faɗi ya mutu in ya tuna garin. Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar. Dai-dai lokacin kuma Hajia Mama da Batul suna gab da shiga sashin Jabeer, A tsakiyar falon sukayi kiciɓis dashi. Yana sanye cikin tufafin da sune suturarshi, al'kyabbar ruwan madarace, sai kayan dake cikin al'kyabbar su kuwa ruwan bonbitane, yayi wani irin masifar kyau, sai ƙamshi yake bazawa tako ina. Fuskarshi ta fito ras cikin hiraminshi ruwan madara, Wani irin ƙyalli da sheƙin kyau yakeyi. Duk da ba murmushi a kan fuskarsa amman ana iya gano tsantsar farin cikin da yake ciki. A hankali yake taku, Ya Jafar na biye dashi a baya, Cikin tarin kula da nuna soyayyarsa Hajia Mama tace. "Masha Allah, Ɗan Umaymah yayi kyau, ga farin ciki ya wadaci kekyawan fuskarnan taka". Kanshi ya ɗan kauda ya kalli Ya Jafar daketa jan hannunshi su fita, cikin nitsuwa yace. "Sun isoma". Cikin jin daɗi tace. "Eh haka dai Jamil ya gaya min". Ta ƙarishe mgnar tana juya baya tare da Batul da cikin sanyi tace. "Ya Jabeer ya jikin?". Cikin jan gajeren tsaki yace. "Lfyata lau". Murmushi tayi sabida jin zazzaƙar muryar shi. A tare suka fito su Mama na gaba shida Jafar suna baya. Suna fitowa harabar Side ɗin shi. Motarshi da Sheykh Abdulkareem yasa aka taho mishi da ita wacce bai taɓa hawantaba, asalima gani yake tamkar almozzaranci ne, sai yau ya bawa Haroon key ɗin ta yace a ɗauko mishi Umaymahnshi, shi bazai je ɗaukotaba sabida. Lamiɗo yace bazai fitaba. A hankali ya tsaya ganin hancin motarshi ƙirar Mercendes benz maybach Exelero wacce ta kai kimanin $8 million dollars. Da sauri ya ƙarasa jikin motor. Hajia Mama na biye dashi. Yana isa inda suke yasa tattausan hannunshi ya buɗe marfin motar. Karo na forko da naga murmushi a fuskarshi, cikin tarin shaƙuwa da kulawa yace. "Marhababuki ya Umaymah, ta faddal". Wani irin murmushi Umaymah tayi cikin tsantsar so tasa hannu ta kamo hannunshi daya nuna mata alamun ta fito. Wani irin yalwataccen murmushi mai nuna tsantsar jin daɗi ya kumayi lokacin da yaji tasa hannunta tsakiyar kanshi. Da sauri ya rusuna a bakin motar cikin sanyi ya manna kanshi da guiwowinta dake zuro woje, kanshi ta shafa tare da cewa. "Allah yayi maka al'barka ya kare mana kai da kariyarsa mai tarin yawa ya iya maka abinda idonka baya gani". Amin Amin, su Haroon da Jalal, Jamil, Hibba, ƙanwar Haroon, da kuma Imran, Sulaiman, Aunty Juwairiyya dake kusa da Umaymah. suka amsa tare da murmushi a fuskokinsu. Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya tashi kana ya buta hanya ta fito. Tana fitowa Hajia Mama ta ƙara so gareta cikin tarin baiyana jin daɗi ta ruggume Umaymah tare da cewa. "Ta ɗanki kawai kikeyi, mu har mun kusa mu bushe a tsaye". Murmushi Umaymah tayi tare da cewa. "Afwan ya Aunty kin san in Jabeer na yana wuri bana ji da ganin kowa sai shi". Haroon ne ya taɓe baki tare da cewa. "Uhumm ai mun saba ganin wariyar launin fata". Hannunta tasa ta ɗan zunguri Haroon tare da cewa. "Kishi". Jamil ne ya ɗan kallesu lokacin da suka ɗunguma suka nufi Sade ɗin Jabeer cikin tura baki yace. "Allah ko Mama kada ki bari Umaymah ta sauƙa a sade ɗin Hamma in dai ba sade ɗinmu zata sauƙaba Muda muke ƙanana sai ta sharemu saishi. Tunda hakane ta sauƙa side ɗinkin". Cikin dariya Umaymah ta juyo da sauri ta kalleshi tare da cewa. "To Jamil harda kai, wato kaima ɗan team ɗin Haroon ne ko? To sha kuriminka Aunty bazata shiga tsakanin uwa da ɗaba, ko Hajia Mama?". Ta ƙarishe mgnar tana kallon Hajia Mama daketa murmushi cikin jin daɗin tace. "Haka kuma ɗa bazai shiga tsakanin ya da ƙanwaba, Gaba ɗaya Jabeer ya kwace mana ke". Murmushi mai kama da dariya sukayi gaba ɗayansu lokacin da suka shiga cikin falon. Shi dai Jabeer sai murmushi yakeyi. Ya Jafar kuwa in yaga Jabeer na murmushi sai shima ya ɗanyi murmushi. Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Batul dake gaida Umaymah sakin fuska tace. "Matar ƙani yau tun safe ban jikiba". Wani irin murmushin jin daɗi tayi Allah yasani in Aunty Juwairiyya tace mata matar ƙani tana jin daɗi. Cikin happy tace. "Yau a kitchen na wuni inayiwa Umaymah girkinsu na larabawa". Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa. "Yo ai na rigaki, dama girkin bare bari kikayi mata". Kanta ta ɗan juya takalli Sheykh Jabeer dake zaune kusa da Umaymah, in zaiyi mata mgna sai ya juya harce zuwa larabci. A ranta take addu'o'in Allah ya nuna mata ranar da zata zauna kusa dashi haka a matsayin abar sonshi. Tattausan Lips ɗin shi masu kama da kunnen fure ta kalla. sunan jazir sai sheƙi sukeyi a cikin tattausan sajenshi da gemun tamkar an shafa musu mai. Allah ya sani randa ta samu lips ɗin nan a matsayin mallakinta, tabbas sai ta kusan haɗiyesu. Hajia Mama da kanta da ita da Aunty Juwairiyya ne suka rinƙa kawowa Umaymah abubuwan motsa baki yaran yar uwarta na zagaye da ita, Hibba ce yar autarta ta ƴar kimanin shekaru 16 kalli Jabeer cikin cikin sanyi tace. "Hamma Jabeer Aunty Jazrah tace in gausheka, wai yaushe zamuje". Kanshi ya juyo ya ɗan kalli Hibba cikin son yarinyar yace. "Hibba auta yaushe kikeso muje". Da sauri tace, sai na tambayi Aunty Jazrah". Murmushi yayi kana ya kalli Aunty Juwairiyya yace. "A shigar mata da kayanta, a ƙara gyara mata masauƙinta, yafi fadar Jalaluddin kyau". Dariya sukayi baki ɗayansu. Shi kuwa Sheykh Jabeer kamar ba shi yayi mgmar ba. Ita kuwa Umaymah da Hajia Mama hararanshi suka ɗanyi tare da cewa. "Ai babu fadar da zatafi fadar shi kam, shinefa gatanka". Murmushi ya ɗanyi tare da cewa. "A a kam Allah ne gatana, shi kuma da yake son ayi ta ɗimata". Juwairiyya kanta tayi mamakin sakewar Jabeer sosai Duk wanda ya ganshi zaiga tarin farin ciki tare dashi. Nan dai suka zauna akayi ta hira. Saida aka kira magriba ne, duk suka miƙe

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185