Chapter 148
Chapter 148
maggi, tafarnuwa man gyaɗa, komai dai dai-dai misalin yadda zata buƙata duk ta ajiyesu kusa da ita. Fere dankalin tayi ba tare da ta daddatsashi ba. Ta wonƙeshi fes kana tasa a ƴar tukunya tare da tarfa gishiri da ruwa dai-dai misali, sannan ta tafasashi. Kwan ta ɗauka ta fasa ta kaɗashi da kyau tare dasa yankekken al'basa da Curry da maggi da tafarnuwa ɗan kaɗan. Ganin dankalin yayine ta juyeshi a ɗan kondo ta tsaneshi. Tare da ɗan barinshi yasha iska, kaɗan. Kana ta ɗaura Naman da maggi da gishiri da Curry da tafarnuwa da al'basa. bisa wata a ɗan tukunta. Sannan ɗaura man ta ɗauki dankalin ta tsomawa cikin kwan tana soyashi, saida ta gama ta ajiyeshi gefe. kafin nan naman kuma yayi lugub yayi laushin. saida ruwan ya kusa ƙarewa sai ta ƙara wata al'basar da tumatur suka nuna tare sannan ta kwashesu. Kabejin ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauki dafaffan kwai ta yayyanka shi da ɗan girma. Kana tasa Maggi da al'basa da Bama ta gauraya kana Ummi ta miƙo mata ɗan ƙaramin Foodflaks alamun ta amsa ta saka. Kanta ta jujjuya tare da cewa. "Bari in sa mishi a plate kawai tunda ya dawo". Da mamaki Ummi ta kalleta tare da cewa "Yaushe ya dawo?" Plate ta ɗauko tare da cewa. "Tun ɗazu". Da sauri ta sunkuyar da kanta ganin kamar Ummi na mata kallon Mamaki da tuhuma. Ita kuwa Ummi cikin Binta da ido tace, Ya akayi kika san ya dawo". Kai ta rausayar tare daci gaba da aikin kamar bataji Ummi ba. Plate ɗin ta ajiyeta, ta zuba Arish ɗin gefe kana tasa haɗin naman gefe, ta kuma zuba na Kabejin shima gefe. Ta shiryashi yayi kyau sosai. Ɗaya plate ɗin ta kife kanshi. Kana tasa spoon da Fork a cikin tray'n data ajiye plate ɗin. Ɗan madaidaicin flaks ɗin coffee ta ajiye gefe, kana tasa cup da tea spoon a ciki. Sannan turashi gefe. Zuwa lokacin kuma tuni Ummi da Saratu su gama aikin sahur ɗin har Saratu ta tafi. Sauran ta sako a wani plate ɗin tare da cewa Ummu gashi. Amsa Ummi tayi tare da cewa. "Ɗauki ki kai mishi to". To tace tare da ɗaukan tray'n ta fita. A tsaye ta sameshi cikin wani tattausan jallabiya da alamun wonka ya fito, Sai wani irin masifeffen ƙamshi yakeyi. Cikin nitsuwa ta wuce ta bayanshi, inda yake tsaye yana kunna Tv. Bisa santa table ɗin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon ta ajiye mishi. Kana ta juya a hankali ta fita. Kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Hibba tuni tayi bacci. Wonka tayi da ruwan ɗumi tare da shafa mai kana tasa wata tattausar rigar bacci gajera iya karta guiwa. Hibaji ta zura a jikinta kana ta haura gado ta konta tare da jawo blanket ta duƙunƙune a ciki. Sabida ita bata son sanyi, shiyasa takesa ƙaton hijabi kana ta shiga borgo. Badon Hibba Bama dake masifar son sanyi da kashe AC'n zatayi. Ƙarfe ɗaya dai-dai ta tashi bacci al'wala tayi kana tai ta nafila hakama Ummi. Sheykh Jabeer kuwa tuni ya tashi shima. Ya kira su Jalal ma a waya ya tashesu. Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta isa falonshi da tray'n abincin sahur ɗin shi. Ta ajiye ta juyo kenan shi kuma yana fitowa falonshi. Tazo tsakiyar falon kenan tana tafiyarta a hankali ba zato ba tsammani taji daram-dam ƙaran bindigar da kullum da asuba sai an saketa sau biyu, ta kuma kasa sabawa dashi bare ta daina tsoronshi. Wani irin tsalle da zabura tayi tare da ficewa a guje tana cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun". Bayanta yabi da kallo tare da taɓe baki kana ya nufi Dinnin area. Washe gari da safe yau Jumma'a kuma, yaune azumi na shida. Bayan sun fitone, Ummi ta kalleta cikin dariya dan tuno yadda ta fito falon Sheykh Jabeer a guje da asuba, tana jan Allah ya isanmata ana tsinka mata zuciya, Cikin murmushin tace. "Ummi dariyar me kikeyi ne?". Cikin gimtse dariyar tace. "A babu, yauwa tashi muje ɗazu Gimbiya Aminatu ta aiko, wai tayi kewarki kwana biyu azumi ya ɓoyeki bakije ba". Cikin murmushin tace to muje Ummi". Ta ƙarishe mgnar tanayin gaba Hibba na biye da ita a baya. Cikin sauri Ummi tace. "A haka zaki fita ba al'kyabba". Kai ta ɗan dafe tare da cewa. "Wayyo Allah na, Allah kuwa ni nauyi sukemin wannan tsarabe-tsaraben wuya gareshi". Murmushi Ummi tai tare da miƙewa ta ɗauko al'kyabbar. Tazo tasa kana suka fita. Da Side ɗin Hajia Mama suka fara, A falo suka samesu. Cikin fuskar ba yabo ba fallasa Hajia Mama ta amsa gaisuwar Shatu. Batool kuwa sai auna mata harara takeyi. Hira suka ɗan taɓa kana suka fito. Har sun fito Shatu ta ɗan kalli Ummi cikin sanyi tace. "Ummi jirani anan bari inje in isar da saƙon gaisuwar Ummey na wurin Hajia Mama". Da Mamaki Ummi tace to kana ta juya ta nufi ciki, ganin Hibba za biyota ne tace. "A a jirani ina zuwa". Haka suka tsaya suna jiranta. A hankali ta turo ƙafar falon. Da sauri Hajia Mama ta zuba mata ido fuska cike da tsana. Batool kuwa binta da ido takeyi ganin wani irin takun isa da ƙasaitar da takeyi. Kujerar dake fuskantar wacce Hajia Mama ke zaune a kai ta zauna. Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya. Kana ta jingina da kujerar, cikin tsare Hajia Mama da ido tace. "Uhummmm kin sanni sarai, kar tasan karne, duk motsinki a tsakiyar tafin hannuna kike, dan haka gwara kiyiwa kanki gada ki fita harka da rayuwar mijina! Da ƙannenshi da wanshi. In kuwa kikaƙi zakisha mamakin Shatu." Tana faɗin haka ta miƙe, tana kallon Batool da tun randa akace Shatu tazo ta bawa Hajia Mama haƙuri da ta shigo tayi wasu kalaman ya ɗaurewa Batool kai ta kasa tantance tsakanin aya da tsakuwa, shiyasa batayi gigin yin mgn ba, sabida tuno abinda Shatu tace mata a ranar cewa. "Mijina kike so ko, to kizo in ya amince ya kalli inda kike na daƙiƙi biyu rak zan sashi ya aureki". Da sauri Batool ta dawo daga duniyar tunanin da take jin ƙaran rufe ƙofar da Shatu tayi. Ido ta maida kan Hajia Mama dake gurnani kamar macijiya. Jim kaɗan ta fito. Cike da son gano wani abu Ummi ke binta da ido, amman ta kasa gano komai domin Shatu ta iye takunta, ta fito kamar ba itaba gaba tayi. Kana suka nufi Side ɗin Gimbiya Aminatu. Suna shiga ta miƙowa Shatu da Hibba hannu kusa da ita ta ajiyesu. Bayan sun gaisane ta kallesu tare da cewa. "Azumi ya boyeku da yake ku ragwagene". Murmushi sukayi tare da cewa. "Kai Gimbiya jiya nefa kawai bamu zoba". Cikin kula Lamiɗo dake shigowa yanzu zai sabunta al'wala zai wuce masallaci yace. "Shatu matar malam bauɗeɗɗe". Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai. Hibba ce tace. "Sai na gaya mishi". Dariya sukayi kana suka sallamesu suka tafi ganin lokacin sallan yayi. Har sunje bakin ƙofa Gimbiya Aminatu tace. "Yauwa Jakadiya kayan miyanku da saura ko ya ƙare?". Cikin rusunawa tace. "A'a da saura sosaima". Kai ta gyaɗa kana suka tafi. A hanyarsu ba komawane Shatu tace. "Ummi wanne kayan miyan ne?". Cikin sanyi tace. "To ba kince
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185