Skip to content

Chapter 179

Chapter 179

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

falon ya zauna kan kujerun dake falon, a hankali ya kwantar da kansa jikin kujerar yana furzar da numfashi mai zafi, lumshe ido ya yi, saboda ƙugin yunwa da cikinsa ke yi, zaman da ya yi, so yake ya ji dama-dama ya ci abincin ya kwanta, tun yana iya jujjuya jikinsa har ya gagara yin hakan saboda ilahirin gaɓoɓinsa sun amsa da zazzafan zazzaɓin ji yakeyi gaba ɗaya gabban jikinsa kamar allurai ake sokawa mushi, yana nan kwance har wajen ƙarfe ɗaya na dare jikinsa na karkarwa. Cikin rawan sanyi daƙyar ya lallaɓa ya samu ya shiga bedroom ya kwanta a kan gadon a gicciye, hannunsa na rawar ɗari ya janyo blanket ya rufe dukkan jikinsa, shi kansa yana jiyo hucin numfashinsa da zafi, yana yi yana ɗan nishin azaba ƙadan, a haka ya samu yayi baccin wahala mai cike da rikitaccen mafarki mara kan gado. Kiran sallan farko ne ya tashe shi, cikin yanayi wanda bai saba tsintar kansa ciki ba ya miƙe, kasala-kasala gajiya-gajiya, ga mamakinsa zazzaɓin ya sauka, don yana ga ɗumin da jikinsa ya fitar da gumi alamun sauƙan zazzaɓi duk da akwai sanyi ac, addu'a ya yi ya miƙe a hankali ya shige toilet sai da yayi wonka da ruwa mai sanyi sannan yaji jikinsa ya yi masa daɗi. Da sauri ya fito ya fara shirin zuwa masallacin masarautar don har sun fara kiran assalatu. Bayan sun idar da sallan acan ya yi zamansa don gabatar da azkar da sauran addu'o'in da yake gabatarwa a dai-dai lokacin, sai da gari ya yi washe sannan ya dawo ya wuce falonsa kai tsaye. Da hantsi ya fito daga falon. Cikin shigarsa ta yau da kullum. A nan ya taradda su ita da Ummi suna zaune. Da alamun Ummi nata lallashinta akan ta yi breakfast ne. Tsayuwa ya ɗan yi gefensu tare da cewa. "Ummi yunwa". murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Dama yanzu nakeso Aysha taci, sai ta kai maka nakan." A hankali ya ɗan yi taku biyu zuwa uku, ya kana ya zauna bisa kujerar dake fuskantar tasu. Ido ya ɗan zuba mata, tare da jingina kansa jikin kujera. Cike da wani irin mayataccen shauƙi. Ita kuwa Aysha yatsun sawunshi ta zubawa ido, tare da shaƙan ƙamshin turaren jikinshi dan tun da ya shigo daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika wajen har sai da Aysha ta lumshe ido, Allah ma ya sani tana masifar son ƙamshin turarensa. Idonshi ya ɗan buɗe tare da ƙanƙancesu kana ya tsira mata su yana kallonta, a nutse sai kuma yayi wani gajeren. Murmushi cikin nutsuwa da jera kalami yace. "Me zai sa ace ba za a ci abincin safe ba? bayan kuma shi ya fi kowanne amfani a jikin ɗan adam?". Kallon shi ta yi tare da kwaɓe fuska kana ta ɗan tura bakinta tare da fara magana ƙasa-ƙasa can cikin maƙoshinta. "Dama ba dole kace haka ba, tunda kai ne sanadiyyar ciwon, kuma ba ajikinka yake ba." Ummi dake gefenta ta jita sarai duk da ba kalmomin duka ta ji ba amma tasan abinda take nufi. Shi kuwa Sheykh Jabeer lumshe ido ya kumayi tare da sauke sassayan numfashi kana ya buɗe idon ya zubasu kan bakinta. Kallon bakinta yayi ba tare da ta gama haɗe lips ɗintaba yace. "Kika ce kin yi yajin cin abinci?". Ya faɗa da zolaya duk da ba halinsa ba ne, ba kuma ɗabi'arsa bane. Shima kanshi bai san ya aka yi zuciyarsa ta raya masa faɗin hakanba. Lips ɗinsa ya ɗan laso da harshensa lokacin da yaji tana cewa. "Uhmm ni ba haka na ce ba." Gyara zamansa ya yi yana mata wani irin kallo mai cike da fassara, kallon nasa ne ya sa mata mutuwar jiki da kasala, don sai da ta ji wani iri a jikinta sabida wani irin kallone mai tsada da masifar ratsa jiki da zuciya. Shi kuwa cikin tsareta da idon yace. "Uhumm to muna jinki Aaaaishhh!". Kiran sunanta da yayi da wata siga haka ya sa ta ɗago kai ta zuba mishi ido. Sai kuma ta kauda kanta da sauri tare da sauƙe numfashi, kwarjininsa ne ya cika mata ido sai wani Murmushi mai tsada da yake mata. Cikin narkekkiyar murya tace. "Cewa na yi na ƙoshi." Ta ƙarashe mgnar tana kauda kai aranta tana jinjina kwarjini da haiba irin ta shi. "Yarinyar goye a ke yiwa dole ta ci abinci fa, ko kema sai Ummin ta goyaki zaki ci? Tunda naga nima mancewa sani takeyi sai ke". Dariya Ummi tayi tace. "Idan zata ci sai na goyata". Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai ƙasa tana nanata zancensa wai agoyata. "Yi haƙuri ki ci abincin kin ji." ta kuma jin muryarsa a bazata. Janyo flask ɗin yayi gabanta, flask ɗin ta ɗan kalla tana jujjuya kwayar idanunta, cikin ranta take jin kwarjininsa ke yi mata barazana da ta ji shakkarsa, ban da haka ba zata iya shan da ruwan zafi acikinta ba sabida ɗazu da sassafe Ummi ta sata cin sauran naman ji data ɗumama mata. Sama-sama a haka ta ci abincin da ɗan yawa duk da bata so cinsa ba. Tana gamawa Ummi ta kwashe kayan kwanukan, shi kuma Sheikh ya wuce falonsa. Yana shiga Jamil ya shigo, shi da Juwairiyya, zama suka yi suna hira Ummi ce ta ɗan kalli gefen da Aysha ke zaune tare da cewa. "Yauwa Aysha tashi ki kaiwa Sheykh abincinsa". Cikin sanyi tace. "Ayyah Ummi bawa Jamil ya kai mishi". Sai kuma ta kalli Jamil tare da cewa. "Jamil ɗauki ka kai mishi". Ta ƙare mgnar tana ɓoye ainihin tsoron sake shiga inda yake da takejin. Murmushi Ummi tayi dan ta ganota, tray'n ta miƙawa Jamil dake cewa. "Ummi kawo dai in kai dan ke". Murmushi sukayi, kana shi kuma ya kai mishi sannan ya fiti. ba su daɗe ba Yah Ja'afar ya shigo shi ma ya zauna kusa da Jamil nan suka ɗan ci gaba da hirarsu Haka dai sukayi wunin wannan. Ranar cikin farin ciki suka yini don anan falon suka ci abinci dukansu. Da daddare ba yanda Ummi ba ta yi da Shatu ba akan ta kaiwa Sheikh abinci ta ƙi, sai da kanta ta kai masa. Don Aysha tsoron zuwa ɓangarensa take, saboda har yanzun tana jin jiki. Washegari ma da safe Ummin ce ta bawa Jamil ya kai masa, don fir Aysha ta ƙi zuwa. Bayan yayi wanka ya fito, ya shafa mai ya kimtsa cikin wani tattausan yafi boyel mai taushi da kyau, Sky blue ne sai aikin da akayi mishi da farin zare sosai yayi kyau sai ƙamshi yake zubawa. A haka ya fito falonshi breakfast ɗinsa Wanda yana kimtsawa ya jiyo muryar Jamil ɗin na ce masa ga breakfast ɗinka Hamma Jabeer. Zama yayi bisa kujera, yana mai mgnar zuci. "Rabon Aiiish da side ɗinna tun shekaran da safe yau kwana biyu kenan ana na uku rabon data shigo nan". Murmushi mai yelwa yayi wanda bai san dalilinsa ba. "Uwar raki da tsoro". Ya faɗi a fili lokacin da ya fito babban falon ba kowa a falon haka yasa ya wuce yana girgiza kai ya wuce dan sauri yake Asibitinshi zaije. Bayan ya shiga asibitin ɗaki ɗaki ya bi duk marasa lafiyan ciki suna gaisawa tare da basu taimako na musamman yana

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185