Skip to content

Chapter 118

Chapter 118

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

nuna alamun yana nan da rai daram da kuma haiyacinsa. Bayan wannan babu abinda yake motsawa a jikinshi, Cake ƙasar garin yakeyi da yatsar kafar tashi. yatsun hannunshi kuma, motsasu yake yana tasbihi dasu, wanda shima cikin zuciyarshi yake ambaton Allah dayi mishi kirari da kyawawan sunayenshi. Zafin da yakeji a jikinshi tabbas ya wuce zaton mai zato. Taune lips ɗinshi na ƙasa yayi da fararen haƙoranshi tamkar zai hudasu, sai dai har cikin ƙashin haƙoran nashi yake jin azabar dafin dake cikin wadannan bulalin masu masifar siddabaru, sai dai babu wani siddabaru da yayi tasiri a kanshi ko a jikinsa domin shi Allah ya riƙe, Ba'ana kuwa tsafi ya riƙe. Wannan gasace tsakanin gsky da ƙarya, bawai gasar caɗi bane kamar yadda mutanen wurin ke kallo. Haka yasa duk da safin wannan bulalin sam basu kai zafin da yakeji a ranshi na sashi ya tsaya gaban dubban al'ummar garin da ɗan guntun wonɗo a jikinshi ba. Allah ya sani shi mai kunya ne, kuma shi mai suturce kanshine, shida kanshi yana jin kunyar kanshi da kanshi. Baya zama haka ko a ɗaki sabida yana tuna in mafa ya kaɗaice yana tare da Raƙib da Atib Mala'iku makusantan ɗan adam, wanda in ka bar tsiraicinka ma su kauda ido sukeyi daga gareka. Shiyasa shima yake kauda ido daga kan kanshima bare wani. Allah ya sani babu wani abu da aka taɓa yi mishi a duniya ya ƙona mishi rai sama da wannan abun. Tabbas da an barshi hakama, yafi jin zafin hakan sama da waɗanan bulalin. A ranshi yake wani irin kuka mai cin rai yana mgnar zuciya. "Anci min zarafi an wulaƙantani an tozarta ni a gaban waɗan mutanen da wasun cikinsu zindigan kafuraine. An barni tamkar mara kima da galihu, wannan shine iya maƙurar zalumcin da akayiwa rayuwata a karo na biyu". Sam baya jin zuciyarshi tanada raunin da zai iya zubda hawaye kan bulalin nan shiyasa ko zafinsu bai zame mishi abin zubda hawaye ko ihu da bakiba ko gudu ko wani motsi. Zuwa yanzu hankalin kafuran ƙabilar ɓachama ya yi masifar tashi domin wannan shine karo na forko a rayuwar tarihin Ba'ana da ya zana mutun bulalin shaɗi har talatin da takwas baiyi ihuba bai zubda hawayeba, bai sumaba, bai faɗi ba, bai guduba. Kai wannan abun yayi tsamari wannan wanne irin mutum ne, anya kuwa mutun ne ko al'jan. Ya Salmanu kuwa, cikin tsanani kuka cur-cur da hawayenshi sabida yasan azabar da Sheykh Jabeer yakeji. Juyawa yayi ya fuskanci gabas, sujjada yayi tare da fashewa da wani masifeffen kuka mai cike da rauni murya na rawa yake cewa. "Ya Haiyu ya ƙaiyum, ya ziljalali wal ikram. Ya Allah ka ƙarawa wannan bawa naka dauriya da jarumta, ya Allah ka bashi ikon jure wannan azabar, ya ubangiji ka sanyaya mishi masifun dake jikin waɗanan bulalin, ya ubangijin taliƙai ka hana wannan mugun mushirkin bawa naka samun nasara, ya Allah ka kare musulminka kan wannan kafurin matsafin da baya salla". Kuka sosai ne yaci ƙarfin Ya Salmanu. Bappa ma wani irin raunine ya rufeshi tabbas kowa zaiyi tunanin Jabeer yana jin azabar duniya. Sai dai kasan cewarsa Jarumin namiji haka yasa babu wata alama da ya nuna na yana jin zafi ko ciwo. Sosai kuwa hakan ya tada hankalin kafuran. Lamido da Galadima kuwa kallon juna sukayi tare da yin murmushi irin nasu na manyan fada, murmushi ne mai manufofi. Jalal kam kife kansa yayi a cinyar Lamiɗo ya saki kuka mai sauti. Haroon ma hawaye yakeyi zuwa yanzu. Hankalin duk tawagar Lamiɗo yayi masifar tashi, ganin yadda wani irin azabebben zufa ya tsinkowa Jabeer tun daga tsakiyar kanshi, zufar nan take gangarowa har kan jikinshi gaba ɗaya, saida ya jiƙe yayi jilak tamkar an kwaza mishi ruwa bokati ɗaya. Wani irin karkarwa jikin shi, ya farayi yana tsuma yana ɓari, gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi. wanda duk fulanin wurin suka fahimci cewa tabbas. Zai iya cinye gasar zai kuma iya faɗuwa. Shi kuwa Sheykh Jabeer daga can cikin naman jikinshi yake jin jikinshi na rawa tamkar mazari. Zuciyarshi kuwa wani irin duka takeyi, wanda muddin kana kusa dashi zakaji yadda take bada sautin harbawa. Hankalin Ba'ana yayi ƙololuwar tashi, ganin har yayi mishi bulala ta arba'in da biyar. Baiyi ɗaya daga cikin ababen da zai hanashi cin gasar ba. Ganin hakane ya juya a fusashe, bulalin hannunshin ya wurgar kana ya sunkuyo kam ranɗar bulalin tsafinshi, bulali biyar ya zaro, ya haɗa su ya damƙesu cikin hannunshi. Cikin azaban ƙarfi ya ɗagosu ya yarfawa Jabeer su a tsakiyar kanshi. Wani irin azabane ya ziyarci ƙoƙon ranshi, wanda hakan yasa yaji wani irin fitsarin azaba yana cika mishi mara. Jinine ya tsinko ta kafaɗunshi, yana bin cikinshi, bai gama jin azabar waɗannan ba ya kuma zarma mishi su a cinyoyinshi. Da sauri Arɗo Bani ya miƙa tsaye daga sujjadar da yayi jin ihun mutane, suna cewa. "Ka karya dokar gasa ba'a haɗa bulali biyuma bare biyar kasheshi zakayine. Cikin wani irin isa ta jarumta da jinin sarauta Sheykh ya buɗe kwayar jajayen idanunshi, Barmuji da yayi kansu da nufin kama hannun Ba'ana ne, Ya ɗagawa hannunsa alamun daka dakatarwa alamun ya tsaya kada ya iso ya bar Ba'ana yayi komai ba komai. Cikin tsananin mamaki duk al'ummar wurin suka zuba musu ido ganin jarumta ziraran miraran tana tsaye da sawunta. Shi kuwa Barmuji cikin rauni yaci gaba da nufosu yana cewa. "A a Sheykh bazan barshi ba, ai ya karya ƙaida da dokan gasa". Ya ƙarashe mgnar yana isowa inda suke. Cikin tsananin takaici da firgicin ganin faɗuwa a karo na forko na rayuwarshi, Ba'ana Ya zargawa Barmuji bulalin da ƙarfi. Wani azabebben ihu Barmuji ya narka tare da fara tsalle yana yarfa hannunshi yana zagaya wurin hawaye na shatata mishi sabida azabar da yakeji, cikin ihun azaban bulalin da aka yarfa mishi sau ɗaya, fitsari na tsiyaya a sawunshi yace. "Arba'in da takwas!". Ta gabanshi ya dawo ya shauɗa mishi na arba'in da tara, wanda yasa Jamil yin tsalle yazo gabanshi cikin kuka yace. "Kasheshi zakayi ne?". Cikin tsananin azabar da yakeji ne ya buɗe jajayen idanunshi ya kalli ta inda yaji muryar Jamil. Hannunshi yasa ya ture Jamil gefenshi. Shi kuwa Ba'ana wani irin ihu yayi tare da buga tsalle yayi sama kana ya zabga mishi bulala ta hamsin kuma ta ƙarshe. Wani irin dogon numfashi Jabeer yaja tare da buɗe idonshi kan fuskar Lamiɗo daya iso hango dishi-dishinsa yana nufo inda suke. Wani irin ihu da karaji Ya Salmanu ya kurma da azaban ƙarfi, Wanda ya haɗe ya gauraye da busar sarewa da al'gaita da dukan gamgar jami, aka saki a tare. Wani irin sowa da ihu da hargowane ya cika illahirin gaba ɗaya Rugar Bani, Wanda mutane fulani suketa rawan farin cikin jarumtar Jabeer, Arɗo Bani da sauran dattawan rugar kuwa gaba ɗaya sujjadar godiya sukayi wa Ubangijinmu sarki gagara misali. Gaba ɗaya an zagaye Sheykh Jabeer. Wanda shi kuma ya juyawa Haroon baya alamun yasa mishi suturarsa. Da tsananin rawan jiki. Haroon ya wore al'kyabbar, ya zura mishi ita kan jikinshi daketa zubda jini. Yana jin Haroon ya saka mishi Al'kyabbar ya ɗago kafaɗunshi ya gyara zaman al'kyabbar. Jiki na rawa yasa hannunshi ya kama gefe da gefen bakin al'kyabbar ya hadesu

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185