Chapter 8
Chapter 8
sara ɗaya da zaiyima mai wasa da salla har ya mutu bai canzaba zai nitse cikin ƙasa anayi mishi azaba, bazai gusheba anai mishi azaba har tashin al'ƙiyama. Allah ya tsaremu. Uƙuba uku lokacin fitowarsa daga ƙabarinsa itace. Na ɗaya hisabi mai tsanani. Na biyu. Fushin Ubangiji. Na uku. Shiga wuta. Allah ya tsaremu ya bamu ikon kiyaye salla da tsaidashi a kan lokacinsa, yaku taron matasa kune shagala tafi auranku, mu dage mu tsare salla duk rintsi". Ya ƙarishe maganar cikin rauni da kushu'i. Gaba ɗaya kowa jikinsa yayi la'asar musamman matasa masu wasa da salla, Jin ya juya yayi gyaran murya ne. Yasa gaba ɗaya kowa ya mike ya fuskanci gabas masamar lada. Cikin nitsuwa da tattausan harshe yake rare karatun al'ƙur'ani mai girma. Lokacin da yake limancin sallan jumma'ar da a ƙalla yana samu halartan mutun sama da Dubu biyu. Bayan anyi salla raka'a biyu kamar yadda yazo a nafsi, akayi addu'a aka shafa kana, mutane suka fara firfita daki-daki. Bayan 30 minute shal cikin masallacin. Dan gaba ɗaya kowa ya nufi wurin lamuran yau da kullum ɗinshi sai mutanen da ba'a rasaba wanda su sai dare zasu bar cikin masallacin. Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, ne tafe a hankali cikin irin takunsu na sarakai, Yayinda Jikinsa mafi soyuwa a garesa ke gefen damanshi, fadawane ke biye dasu a baya, sun zagayesu, Sai kuma bayansu can kuma Ayarin fadawan Jalal da Jamil ne wanda suke tagwaye ƙannen Sheykh Jabeer. shi kuwa Malam Jabeer taku yakeyi a hankali cikin rashin nuna ɗagawa a kan doron ƙasa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar yayinda mutane kuwa ke kallon hakan a matsayin ƙasaitace da jinin sarauta dake yawo a sasan jikinshi. Suna tafene a tare yayinda bakin Sheykh Jabeer ke motsawa a hankali hankali, wanda sai ka lura kake gane, tasbihi yakeyi a zuciyarshi wanda hakan ya zame mishi abin ci da sha a rayuwarshi. "Astagafirullaha wa'atubu ilaik, Astagafirullaha! Astagafirullaha!! Subahanallahi! Walhamdilillah wa lailaha'illalahu Allaahu akbar. Astagafirullaha". Waɗannan sune kalamen da basa rabuwa da bakinsa, dama wasu masu tarin yawa. Ta ƙofar dake shiga masarautar daga jikin masallacin sukabi. Masarautar Joɗa babbar masarautace mai tarin girma tarihi. Ginin Masarautar ginine mai masifar kyau da ɗaukan hankali. Kana shiga daga asalin babban gate ɗin fadar, zaka samu wata shimfiɗeɗɗiyar hanya mai girma irin mai guda biyun nan, gefe da gefen hanyar duk wasu irin dogin fulawowi na mijin kwanda ne masu tsawo da kyan gani, sai kuma tsakanin titunan, shima jerin dogayen bishiyoyin ne. Tafiya mai ɗan tsawo, zakayi kafin, ka isa wani babban Round about mai masifar kyau, wanda cikinsa ke ɗauke da babban kwarya a ƙasa, sai kuma ƙananan kware, guda uku, sai kuma ginin mutum-mutumi na kekyawar saniya fara mai ɗigo-ɗigon baƙi, wanda mace ke tsugune a gefe kamar tana tatsan nono sai kuma ɗan saurayi matashi na riƙe da sanda ya coge da ƙafa ɗaya. Sai kuma korayen ciyawi masu masifar kyau da sanyi wanda akayi alamun manomi na ciki. Daga nan ne hanyoyin cikin masarautar suka rabu huɗu, ɗaya yayi gefen dama ɗaya yayi gefen hagu ɗaya yayi gabas ɗaya yayi yamma wanda ta nanne ake shigowa. In ka miƙe ta yamma daret itace titin da zai sadaka da asalin sashin Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda nan sashin matanshi da hadimanshi yake da sashinshi dama faɗar duk nan take. In kayi gefen dama kuwa wasu irin tsala-tsalan gine gine-gine masu tsananin kyau da ɗaukar hankalin wanda suna nan part-part ne masu girma da tsaruwa, an ƙawata tsakiyarsu da wani sassanyan Garden mai girman gaske. Inda part ɗin sun kai goma, mafi kusa da sashin mai martaba sarkin Nuruddeen Aliyu Bubayero, shine sashin GARKUWAN FULANI, wato Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero. Sai kuma na gefen daman Sheykh Jabeer shi kuma na Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero ne, da matarsa Juwairiyya. Sai na gefen hagunshi kuma na Jalal, ne na kusa da Jalal da kuma na Jamil ne sai dai Jamil yafi zama a sashin Jalal duk da korarshi da yakeyi wasu lokutan kuma lokacin kuma yana sashin Sheykh. Sai sashin baya kuma sashin Affan. Daga gefen hagun Masarautar kuwa wasu tamfatsa-tamfatsan plat ne masu girma har guda huɗu, sai kuma wani babban bene dake tsakiyarsu mai tarin girma wanda nanne sashin babban ɗan sarki Habibullah da matanshi. Sai ta gefenshi can kuma wasu manyan part- part ne kimanin guda biyar wanda duk ƙanne shi ne da iyalansu da ƙananan yaransu a ciki. Yayinda duk manyan yaransu kuwa kowa nada part ɗin shi a gefen da part ɗin Sheykh yake a ƙalla dai Part ɗin cikin masarautar Joɗa sun kai hamsin da biyar. Can wurin mashigar kuma wasu ƴan saffan-saffan part-part ne wanda bisa dukkan alamu duka na bayine da hadimai da matansu. Tsayuwa fasalta cikin ko wanne sashi na masarautar bazai yiwuba, sai a hankali. Sai dai ko wanne part yanada Garden mai ɗan girma, wannane yasa gaba ɗaya masarautar ke zagaye da korayen fulawowi da bishiyoyi masu kyau. Fentin masarautar gaba ɗaya iri ɗaya ne, Sky blue and white, mai ɗan karen kyau, a mahaɗar sashukan kuwa wani irin tamfatsetsen sweeminpool mai girma wanda ruwansa ke sky blue. Can bayan sashin Mai martaba da Sheykh kuwa wani ƙaton filine mai cike da dawakai, da sashin mai rainonsu, gefe ɗaya kuma raƙuma da shanaye ne da makiyaya su, kana ga tumaki, a gefen Sheykh Jabeer ne kuwa akayi wani ɗan madai-daicin gidan zu ta bayan ɗakunan shi wanda yake da tarin tsuntsaye kamarsu, Ɗawisu, jimina, mikiya, agwagin ruwa, tolo-tolo, tattabaru, kana sai Aku. Da sauran tsuntsaye carki, kurciya, hasbiya, caccagi da-dai sauransu, shiyasa sashinsa ya kasance namusamman, don Garden Park ɗin ciki yafi na sauran part ɗin duka girma da kyau, sabida shine asalin Garden ɗin tarihin masarautar Joɗa. Daga nan mashigar masarautar kuwa akwai wani babban filin sukuwa mai girma. Daga masallacin Masarautar kuwa akwai miƙeƙƙiyar hanya har cikin masarautar wanda za'a iso gab da fada sannan kowa zai samu hanyar sashinsa. A tsakiyar cikin masarautar ma kuwa akwai wani masallaci mai girma. Wannan kenan sai a hankali zaku san mutanen masarautar da sunayensu halayensu dama nasabarsa da danƙantarsu da manufarsu. A hankali Sarki Nuruddeen da Sheykh Jabeer suke takawa. Suna shiga cikin gidan waɗannan fadawan suka tsaya a bakin Gate ɗin. Kana wanda suka samu a wurin suka miƙe da azama wani dogon carpet mai azabar kyau da taushi, ɗaya daga cikin fadawan ya zo ya ajiye gabansu kana ya rinƙa yin baya-baya yana worwore musu carpet ɗin. A hankali Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa yasa hannunshi ya kamo hannun kekyawan matashin jikan nashi da kab cikin jikokinshi ya fita da ban, hannunshi yake murzawa cikin nasa hannun a hankali a hankali. kana suna tafiya a hankali, cikin takun sarauta, Gefen mai martaba Nuruddee bayine da dogarai a ƙallah sun kai Ashirin da biyar, gefen Sheyk Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kuwa, Ƴan saffan-saffan fadawane da basu kaishi shekaruba, a ƙalla sun kai goma. Wanda wannan tsarinsa ne yace bazai iya ganin sa'an mahaifinshi ba ko sa'an Ya Jafar ɗinshi ba suna mishi bauta Babban Yayansu Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero suke kira Yah Jafar. Kanshi ya ɗan murza ya juya a hankali da gefen ido ya kalli Kakan nashi dake magana cikin yin ƙasa da murya dan ko sarkin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185