Chapter 119
Chapter 119
a jikinshi ya suturce kanshi ya kare kanshi. Barmuji na shirin kamo hannunshi yayi maza. Ya ɗaga mishi hannunshin kana ya juya ya nufi inda motoncinsu ke jere. Jalal da na ganin haka yayi maza yayi gabanshi. Marfin motar ya buɗe mushi tun kafin ya iso. Cikin taron kuwa, tuni Ba'ana da matasan ƙabilar ɓachama, sun ɗauki ranɗar bulalin tsafinshi sun nufi Bonon da tarin baƙin ci dan ganin Sheykh Jabeer bai faɗi gasarba, kuma ga mutanen fulani daketa yi musu dariya da ihun rashin nasarar su. Hakan yasa suka tafi dan sun sani a ƙa'ida sai Jabeer yayi jinya ya worke da azabar da Ba'ana ya shayar dashi kafin ya dawo ɗaukar fansa. Cikin taron kuwa cikin kukan rauni Arɗo bani ya rusuna gaban Lamiɗo da tawagarsa murya na rawa yace. "Sauran ɗaukar fansar da zaiyi a duk sanda ya worke a duk sanda yaga dama, fatana kuyi shirya bulalin tarihin masarautarku, domin ramuwa akan wancan taƙadirin da baya jin koda harbin bindiga baya shigarsa. Ina yakun farin cikin nasarar da Jabeer yayi a yau, ina kuma fatan yayi nasara a ramuwar da zaiyi a wannan kuma in yayi nasarar mu zaku taya farin ciki, ko ba komai zamu rabu da wancan taƙaɗirin." Cikin wani irin tarin ƙuna Lamiɗo ya gyaɗa kanshi. Kana ya juya yayi gaba Dogari na rike masa da laima ɗanzagi na cewa. "Gyara kimtsi, a bada hanya, sarki ya barku lfy". Waziri da Wambai Ɗan buram Ɗurɓi Da iya duk suka mara mishi baya. Hakama Arɗo Bani da sauran dottawan wajen sukayo musu rakiya. Sheykh Jabeer kuwa. Yana tafe Galadima na biye dashi a baya. Haroon kuma na gefenshi. Suna isa yasa kai ya shiga cikin motar, kana Haroon da Hashim suka mara mishi baya, da sauri sarkin mota ya maida ƙofar ya rufe. Kana ya buɗewa Lamiɗo motar, gefen bayansu Jabeer ya shiga, kana Galadima ya shiga kusa dashi, sannan aka rufe motar saura duk kowa ya shiga motar da yazo ciki. Sannan duk suka rurrufe motocin. Kana suma Fadawa da dogarai suka shiga nasu motoci biyun. Ɗaya tayi gaba, sauran motocin suka bisu a baya, ta Lamiɗo na tsakiyarsu, kana ɗaya ta fadawan ta biyo bayan uku da ke bin bayan ta Lamiɗo. A haka suka ja motocin a jere a jere suka bar cikin Rugar Bani. Cikin Rugar kuwa kowa ya tafi cikin al'ajabi da farin ciki. Da yawa gani sukeyi kamar dai Jabeer ba mutun bane. Sauran dottawan kuwa, zama sukayi cikin fadar bayan sunyi sallan la'asar ne, Bukar yazo ya tsaya tsakiyarsu cikin rashin mutunci yace. "Kuyi kuka da kanku akan duk abinda zai faru gaba". Kafin ma su bashi amsa tuni ya juya ya tafi. Su kuwa nan sukaci gaba da al'ajabi da tuanjidin Jarumtar Jabeer. A cikin motocin kuwa, mutanen ko wacce mota da abinda kowa ke tunawa. Wani irin azabebben gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama, sabida bin umarnin Lamiɗo wanda shi kuwa ya bada izinin gudun ne, dan ganin yadda Jabeer keta zubda jini, ga wani irin masifeffen karkarwa da jikinshi keyi. Gudu sukeyi a 360 musamman ma da suka samu suka hau kan babban titin Shikan wanda zai sadasu da cikin babban birnin Ɓadamaya. Shi kuwa Sheykh Jabeer, wani irin karkarwa jikin shi keyi, idanunshi jinsu yakeyi tamkar zasu zazzago su faɗo ƙasa, sabida wani irin masifeffen azaba da yakeji. Ji yakeyi tamkar ya haɗiyi zuciyarshi sabida masifar fushi da harzuƙa da zafin rai, babban abinda ya tsananta fushinsa shine yadda yaga lokacin sallan la'asar ya gota musu, akan shirmen banza da wofi da zalunci an hanashi yin salla kan lokacin ta. Hannunshi yasa ya fizge rigarshi da ke hannun Haroon dake ta sa hiraminshi yana tare jinin dake zubomishi ta ƙeyanshi. Taune lips ɗinshi yayi tare da sa hannun shi, ya kama wuyan rigar cikin ƙarfi yaja ji kakeyi, Fasss sautin yagewar sabon saddan. Ido suka zuba mishi gaba ɗayansu, Ya Hashim kuwa jiki narawa ya kira Dr Aliyu wanda yake ƙanine ga mahaifinshi da kuma Abbansu Jabeer ɗin. A can baya kuwa inda Galadima dake zaune gefen Lamiɗo ne daya bashi umarnin ya kira sarkin gida ya sanar mishi ayi tanadin jinyar Shaɗi cikin gaggawa. Da sauri Galadima ya zaro wayarshi ya kira sarkin gida. Cikin tashin hankali yake mgna a woya bisa alama duk da sarkin gida yake mgn. "Ladodo, kayi maza yanzu ka sanarwa tsohon sarkin Shaɗin masarautar Joɗa yayi maza ya haɗa tsumin igiyar bulalin shaɗi, ya kaiwa Jakadiyarsu Jabeer, A shirya duk wani abun buƙata, domin Jabeer yana zubda jini sosai." A can masarautar kuwa Sarkin gida yana jin haka ya miƙa ya nufi, sashin kananan sarakuna kai tsaye gefen Sarkin Shaɗin ya nufa, ya sanar mishi umarnin da aka bada, ai nan take Sarkin Shaɗin da sarkin Gida, suka shiga bayan sashin mai martaba Lamiɗo, inda bishiyoyin tarihi dana gargajiya da magunguna suke. Forko bishiyar Goruba suka fara sassaƙan jikinshi. Wanda shine babban makarin dukan shaɗun. Sai kuma suka haɗa da wasu tsirran,. Koda suka gama kai tsaye gefen Jakadiya da sauran ma biyanta suka nufa, Nan suka bata dukkan abinda suka ɗebo, suka kuma yi mata bayani. Kana sukace maza ta haɗa su ta dafa, Sauran kuma sai sun dawo Lamiɗo ya shiga ɗakin sirri ya ɗebosu. Cikin tsananin tashin hankali da rawan jiki Jakadiyarsu ta amshi magunguna, ta nufi sashin Jabeer ɗin. Cikin gaggawa ta shige kitchin ɗin shi, ta fara harhaɗa magunguna tana dafawa. A can cikin motar kuwa cikin tashin hankali Ya Hashim yayiwa Dr Aliyu duk bayanin abinda ya faru da halin da Jabeer ke ciki. Ya ƙara da cewa, a shirya komai na bashi taimakon gaggawa. Jin hakane yasa Dr Aliyu tada motar Ambulance wanda take nan cikin asibitin dake cikin makarantar nasu, tazo bakin asalin babban gate ɗin masarautar nasu. Kana ya kira babban abokinshi Dr Sanju wanda ba indiyene wani aikine ya kawoshi ƙasar, tuni suka iso bakin gate ɗin, cikin motar Ambulance ɗin suka shiga suka zauna tare da haɗa duk wani abu na taimakon gaggawa da za'ayi mishi. A cikin motar kuwa, gaba ɗaya ya gama yage rigarsa ya fizge wonɗonma ya yageshi fata-fata. Ganin wani irin kallo da yayi Haroon ne, yasa Haroon yin maza ya matsa tare da yin mgnar zuci. "Ka gani ko Lamiɗo hegen tsoho kai ka dace ka zauna kusa dashi. Inma yagawarne ya yage ka". A zahiri kuwa fuska ya ɗan haɗe tare da cewa. "Kafa gama yaga kayanka yanzu nawane suka rage a jikina, naga ji kake kamar ka yagamu, yaseen to bamu muka kar zomonba". Dai-dai lokacin kuma, sarkin ƙofa ya buɗe musu ƙofar babban gate ɗin. Kana suka kutsa kai. Suna shiga ko parking basu gama dai-dai tawa ba Jabeer ya sa hannu ya buɗe marfin motar, ƙafarshi ya zuro woje, wanda ganin haka yasa Dr Aliyu ya fito da sauri. Sai dai kafinma ya fito tuni Jabeer ya fito cikin motar ya nufi asalin ƙaramin gate ɗin da zai sadaka da asalin cikin farfajiyar. Kusan a tare suka fito daga motocin gaba ɗayansu. Cikin tsananin tashin hankali Ya Hashim ke ƙwalla mishi kira, amman ina bai ko juyo inda sukeba. Baya kuma jinsu sosai sabida duhu da jirin da yake gani. Da gudu Haroon da Jalal Jamil suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185