Skip to content

Chapter 175

Chapter 175

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ba'a aka rinƙa kiran yaro da Joɗa. Allah cikin ikonsa ta yaye yaro lfy lau. Ta kuma haihuwa na goma sha biyu. Yariyar watanta biyar ta rasu, sai aka rinƙa mata dariya ana cewa saura *Joɗa* shima ya *Dilli.* Wato wai saura Joɗa shima ya *tafi.* Cikin ikon Allah kuwa ya raya Joɗa ya girma. Ya zama shine ƙarami cikin ƴaƴan sarki Sule kenan. Bayan wasu shekaru, sai Sarki Sule yace to shi zaiyi murabus, a cikin yayanshi yace zai naɗa babban ɗanshi Madu. Ɗan Gimbiya Falmata. Sai ko sauran ƴan uba duk suka tashi akece to sai ayi zaɓen manyan. To akwai ɗan Madu wanda yake mai ilimin addini dana zamani sunanshi Bala, sai ya shiga cikin masu neman mulkin ya kafa hujja da cewa. "Babanshi Madu jahiline dan haka a bashi shine ya dace da mulkar garin. Haka kuwa akayi aka ba Bala mulkin masarautar Fulɓe. Dole babanshi Madu wanda shine Magajin gari ya ƙaura ya bar garin. Tunda kinga bazai yiwuba ace yana mahaifinshi ya rinƙa serving ɗan shiba da baƙinsa ba. Haka dai Bala yayi mulki tsawon shekaru arba'in inda Joɗa kuma yake matsayin Galadima tunda ɗan tsohon sarki ne. To shi kuma Sarki Bala sai Allah ya azirtashi da tarin ya'ya mata ɗan shi na miji daya ne, Sadik. Ya bawa Sadik sarautan Sardaun. Bayan wani lokacin sai tsoro ke rufe Sarki Bala kada fa abinda ya samu babanshi ya sameshi. Wato kar ɗanshi bai gaji mulkiba kamar yadda sarautar ta tsallake babanshi ta dawo kanshi. To shinefa ya tura ɗan shi Sadik wuraren sauran sarakunan ƙasar, cewa zaiyi murabus zai bawa Sadik mulkin. To dama bisa ƙaida dole sai sarakunan sun yarda. Cikin Sa'a kuwa duk sarakunan suka yarda sukasa hatimin amincewa a takardun. To a kan hanyar dawowanshi ne kuma Allah yayi mishi rasuwa. Wannan abu yayi masifar tada hankalin Sarki Bala. Da mahaifiyarsa Gimbiya Salame, da kakarsa Gimbiya Falmata. Saboda wannan pain ɗin mutuwar ɗan nasa, shene ya tattara yaranshi mata kab ya Aurar dasu. Harda ƴar shekara takwas duk ya kwashesu ya aurar. Sabida wai baya son ya mutu baiga aurensu ba. Ya musu aure ya kuma basu sarauta. Suka zama hakimai." Cikin sanyi Shatu tace. "Tirƙashi duk wannan don son mulki ne?". Kai Ummi ta jinjina tare da cewa. "Uhum ai akan sarauta babu abinda ba'ayi sabida matsalar sai kowa yace shi ɗan sarkine zai gada. Sabida in basu gadaba sarautar tabar hannunsu, Shatu Sarauta masiface a zuciyar masoyansa da zasu iya komai a kanta." Kai Shatu ta gyaɗa tare da cewa. "To Ummi ina jinki". Gyara zama tayi tare daci gaba da cewa. "To in takai ce miki a ƙarshe dai Joɗa shiya zama sarki wanda shine ɗan ƙaramin a ahlin Sule. A lokacin ne kuma sunan jihar nan ya dawo Ɓadawaya sabida. Nunawa duniya ba haka bane duniya Allah zai iya baka zai iya hanaka. Masarautar Fulɓe kuma ta zama masarautar *JOƊA.* Sabida sunan sarkin kenan. Kuna ya zama adalin sarki mai son baƙi duk inda baƙo yazo zai wuce. Sai Sarki Joɗa ya bashi wurin zama yace mushi Joɗa wato zauna ga wurin zama kayi kasuwanci kayi kiwo ki ciya ka ciyar kasha ka shayar." Shiyasa Jihar Ɓadamaya tayi zarra da tarin ƙabilu sabida son baƙi da basu muhallin zama a wancan lokacin kawai fili za'a yanka a baka ka zauna in Kai baƙone To babban ɗan Joɗa shine Bubayero wato kakan Lamiɗo. Bayan Joɗa ya rasune Bubayero ya hau kan karagar mulki masarautar Joɗa. Ahlin Gimbiya Falmata kuma suna yaɗuwa suma buri da kwaɗayin sarauta na jiƙa a ransu duk burinsu suga yadda sarauta zata dawo ɗakinsu. To koda Bubayero zaiyi murabus ya bawa ɗansa Nuruddeen mulki sai ya aurawa ɗansa yar bappan shi jikar Madu ɗanshi. Sukayi aure aka naɗa Sarki Nuruddeen da matarsa yakura. Bayan anyi aurene da shekara biyu. Ya auro wata ƴar masarautar su Gimbiya Sumaye. To itace tazo ta haifi Lamiɗo. Ita waccar bata taɓa haihuwa ba. To shima Lamiɗo sai ya auro yar masarautarsun Gimbiya Sumaye, wato Gimbiya Aminatu a matsayin matarsa ta biyu. To Galadima da kike gani yanzu bappan Lamiɗo ne ɗan autan su marigayi sarki Nuruddeen. To shi kuma Lamiɗo da aka bashi mulki sai aka aura mishi yar zuriyar Gimbiya Falmata itace uwar gida. Ta haifi Baba Basiru da Baba Nasiru da kuma Baba Kamal da kuma babban yayansu Marigayi Auwalu. Sai Dr Aliyu shi kuwa mamanshi daban itama ta rasu su biyu ta haifa da Gimbiya Surayyah. To Mamansu Baba Nasiru. Yanzu haka tana raye amman ta haukace babu mai shiga Side ɗinta, sai Lamiɗo da yaranta. Duk wanda yaje sai tace zatayi duka, ita da bakinta take bayanin Abbansu Sheykh da Gimbiya Aminatu da Gimbiya Aisha tayiwa asiri ya dawo kanta. Galadima da yaga ya tsufane kuma baida ɗa namiji da zai gajeshi shine. Yacewa Lamiɗo ya naɗan babban ɗan shi Auwalu mijin Gimbiya Saudatu a matsayin Galadima. To bayan ya naɗa shi da shekara biyu ne, ya rasu. To sai ya naɗa Ya Jafar ɗin nan da kike gani a matsayin Galadiman Masarautar Joɗa. Lokacin lafiyarsa lau yadda kikaga Sheykh haka yake da ibada addini ilimi nitsuwa tausayi. Kwananshi goma a kan mulkin washe gari za'a naɗa shi ne, ya dawo haka babu mgna sabida wani babban ibtila'i da tashin hankalin ɗaya samemu. Kuma a lokacin an kusa amishi aure sabida sarautar da za'a bashi. To wannan shine babban mafarin hargitsi da kitimurmurar dake masarautar Joɗa a yanzu. Dan ranar da Jafar ya zama haka akwai babbar masifar data fi wannan muni daya faru a masarautar Joɗa. Shine abunda yayi masifar girgiza mutane. Lokacin Sheykh yana saudia yana karatu a jami'atul Madina. Hankalin Hajia Mama yayi masifar tashi tayi ta suma tana sakewa Umaymah kuwa da Sitti mutuwace kawai da basuyi ba, dan baƙin ciki da tashin hankalin ɗaya samemu. To kuma tun daga nan sai duk magautan suka dena kiyayyarsu kansu Jafar da ƙannensa. Koda Jabeer yayi karatunshi a can yayi digirinsa na biyu da PHD dinsa duk a can. Wani sabon tashin hankalin da Jabeer ya dawo Lamiɗo yabashi mulkin GARKUWAn FULANI, nanfa Magauta sukace zasu mutu. Dan ma mulkin na gefen yaya mata aka bashi shine abin ya ɗanyi sanyi. To kuma ingiza gabar sunga ɗawisun masarautar Joɗa tayiwa Jabeer abinda sai sarki takeyiwa. To kinji lbrin a taƙaice sai a hankali zaki gane komai in kina bin komai a hankali." Numfashi mai sanyi Shatu ta sauƙe tare da cewa. "Ummi wacece Gimbiya Aisha?". Da sauri Ummi tace. "Baki santaba". Da sauri Shatu tace. "Toh ina take?". "Bata nan". Ummi ta bata amsa a gajarce. Da sauri Shatu tace. "Ta rasu ne?". Cikin zubda hawaye Ummi tace. "Bamu san halin da take cikiba shine babban burin Sheykh a duniya, sanin inda take". Cikin sanyi Shatu ta kauda waccar tambayar dan ko Ummi bata amsa mataba ita ta gane matsayin Gimbiya Aisha. Haka yasa a hankali tace. "Allah ya baiyana ta. Ya cika mishi burinsa." Amin Amin Ummi tace tana sharce hawaye. Cikin nitsuwa Shatu tace. "To Ummi mene kuma banbancin mulkin gefen yaya mata dana maza". Cikin jin bacci tace. "Da safe ki tambayi Hibba ko Jamil zasu gaya miki, yanzu jeki shiga dare yayi bacci nakeji". Da haka tatashi

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185