Skip to content

Chapter 102

Chapter 102

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

da ido tace. "Ni bana iya yiwa iyayena musu. Jabeer tabbas na sani al'adace ba addiniba, amman ka sani duk wani abun da zakaga ya faru a duniya to akwai dalilin faruwarshi, kada kace zaka tsananta bincike tabbas lokacin zai baiya mana dalilin. Bana son gardama kawai kaje Dan ALLAH". Hannunshi yasa ya dafe kanshi, kana yayi shiru Umaymah ta gama dashi da tace dan Allah, ya sani tabbas da a madadinsa Ayyah ɗin da yace forkon mgnar da ya mata da ya rigata cewa Dan Allah da shike nan yasan zatayi shiru. Shi kuwa Lamiɗo murmushi yayi tare da kallon Umaymah cikin jin daɗi yace. "Allah ya miki al'barka". Da sauri tace. "Amin ya Allah". Galadima kuwa, murmushi yayi tare da jinjina kai. Jakadiyarsu ma cikin jin daɗin tasirin mgnar Umaymah akan Jabeer take murmushi sabida ta sani. Shi mutunne mai kaifi ɗaya, in yace eh tofa eh ɗince inko yace a a to a'ance. Especially baya son duk wani abu da zaici karo da addininshi. Kanshi ya jinjina Umaymah alamar shikenan idonshi yayi jazir alamun dole akasashi yin abinda baya so. Kana ya kalli kakarsa dake murmushi tsuke fuskarsa yayi tare da cewa. "Gimbiya Aminatu muje ki bani gashin da kikayiwa Lamiɗo". Cikin dariya Gimbiya Aminatu tace. "Iye gashinsama zan baka?". Da ƙarfi yace. "Eh shi zaki bani, ai in dukane kam ya iya zille kanshi ya turani. Shine dan gashinsa zakice iye". Murmushi tayi tare da bin bayanshi, ganin Lamiɗo na mata alamun taje ta bashin. Nan sukaci gaba da hira, suna tattauna wasu mahimman al'amuran da sirrine garesu iya su biyar. Wato Lamiɗo, Galadima, Sarkin Shaɗi, Umaymah, Jakadiyarsu. Bayan su babu wanda suke yarda da sanin sirrin Jabeer. A hakanma kuma a suɗinma akwai wani sirrin da babu wanda ya sanshi sai Lamiɗo da Umaymah. Suna zuwa har falonta suka wuce. Wani kekyawan akoshi mai masifar kyau ta ɗauko mishi. Ta ajiye a gabanshi. Inda yake zaune a ƙasa bisa carpet ya naɗe sawunshi. fork ɗin dake saman fefeyin ya ɗauka. Daddageggen gaseshen jan namane wanda yaji wuta ya gasu gashin tukunyar ƙasa yayi tiɓis. Sai wani irin ƙamshi na musamman yakeyi, A hankali yake sa Fork ɗin yana yagan tattausan tsokokin yana sawa a baki. Ita kuma tana zaune gefenshi. Tafashesshen madaran shanu mai ɗan ɗumi ta miƙa mishi a wata ƴar ƙwarya mai kyau. Taune naman yayi tare da haɗiyewa kana cikin zuba mata ido yace. "Dole sai na karɓa da hannun nane? Ki ajiye mana. Da wanne hannun zan amsa tunda inacin abinci dana daman". Murmushi tayi tare da cewa. "Dole sai ka amsa, bazan baka shi a ƙasa". Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa. "Allah ya nuna min ranar da za'a bar. Wannan tsare-tsaren shamfi na masarautar Joɗa. Komai da ƙaida da yadda ake yinshi". Ita dai miƙa mishi ƙwaryar takeyi dole ya ajiye spoon ɗin yasa hannunshi ya amsa. Nan suma sukaci gaba da hira. Sai kusan sha ɗaya Umaymah da Jakadiyarsu suna fito. A nan Gimbiya Aminatu ta ajiyesu suma saida sukaci gashin nata kafin suka tafi. Kafin su isa Side ɗinsa dai sha biyun dare tayi. Haka yasa suna isa suka samu ba kowa a falon. Sai Haroon da suke jiyo muryar sa, a falon Jabeer. Cikin nitsuwa ya matso kusa da Umaymah a hankali yace. "Sai da safe Umaymah kiyi bacci ki huta." To tace har ta juya zata tafi sukaji Muryar Haroon yana cewa. "Abba yazo wurinki zaku gaisa bai samekiba, nace mishi kun tafi wurin Lamiɗo yace, to saida safe ya gaidaki da hanya Hajia Mama ma yanzu ta fita, tace Lamiɗo ya riƙe mata ƙanwa". Murmushi tayi tare da cewa. "To Allah ya bamu al'khairi saida safen". Amin Amin suka ce. Kana shida Haroon suka wuce Side ɗinsa. It's kuma Umaymah da Jakadiyarsu suka wuce. Side ɗin da kullum in dai Umaymah tazo nan take sauƙa. Suna shiga suka samu, tuni Hibba tayi bacci, wannane ya basu damar tattauna wasu mahimman sirrukansu. Nisawa Umaymah tayi bayan ta saurari jawaban Jakadiyarsu Jabeer cikin tsantsar tafasar zuciya da tarin baƙin ciki tace. "Uhummm suyi dai Ni nan ina dai-dai- da ƙugun ko wanne shege da shegiya, In sha Allahu zasusha mamaki. Zasuga yadda Ubangiji ke ikonsa, ban cire raina ƴar uwarta zata sake rayuwar enci da salama, da izinin Ubangiji zataga sakayar waɗanda suka cutar da ita da yaranta a gaban idonta. Cikin zubda hawaye Jakidaya tace. "In sha Allah, sai farin ciki ya dawo, a sashinta, inata addu'a a kullum a cikin dukkan sallolina, Allah ya kare ahlinta, ya kuma baiya gsky tayi halinta kowa ya gani". Amin Amin Umaymah tace tare da share hawayenta. Washe gari ranar Alhamis. Ta kama yau kwana shida da faruwar gasar Shaɗi, kana gobene za'a koma dan ramuwa, A goben kuma zai cika kwana goma da kisan gilla da kafurai ƙabulun Ɓachama sukawa Fulanin Rugar Bani. Misalin ƙarfe sha biyu na safe. Fadar Sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa, cike take maƙil da tawagarsa kama daga. Galadima, Waziri, Wambai, Dan buram, Dan iya, Ɗan isa, Ɗan Kade, Sarkin fada, Sarkin yaƙi, Sarkin Dowaki, Sarkin Gabas, Sarkin Kudu, magayaƙi, Jarma uban doma, Makawa Ɗurɓi, Turaki, Da dai sauran members ɗin masarautar baki ɗayansu, an cika anyi maƙil. Sallama na tsaye can bakin ƙofar shigowa. Dogari kuma suna tsaye gefen hagu da daman Lamiɗo. Suna rike da mafici sunayi mushi fifita, ɗanzagi kuma yana gefe, Kana wasu fadawan duk suna gefen. Gyaran murya Lamiɗo yayi tare da gyara zaman shi cikin shugarsa ta sarakuna masu al'farma, a hankali yace. "To da farko dai fatan duk kowa na lfy". Da sauri Ɗanzagi yace. "Sarki ya gaisu yana yi muku fatan alkhaiy". Sai ya kuma juyo ya kalli Lamiɗo tare da cewa. "Godiya suke." Kanshi ya ɗan jingina da tattausar kujerarsa da masu son gadonta sunfi a ƙirga, cikin ƙasaita yace. "Kamar dai yadda muka tattauna, kwanakin baya akan sarkin Garin Shikan, to yanzu zan zantar da hukunci. Sarkin aike na bada umarni kaje garin Shikan ka karɓo min sandar sarautar Shikan ka kawo min shi, yau ɗin nan. Kaje da jagorancin Galadima, da Matawalle da Makawa, sai sarkin yaƙi". Da sauri duk suka runsunar da kayu kansu tare da cewa. "An gama". Nan take kuwa suka miƙa suka tafi. A cikin gida kuwa. Tunda asuba da Jabeer da tawagar ahlinshin suka dawo masallaci. Kai tsaye ɗakin Umaymah ya nufa, suna biye dashi a baya. Bisa sallaya suka sameta riƙe da al'ƙurani mai girma tana karatu cikin tsananin nitsuwa. Ganin hakane duk suka fito falo. Nan Aunty Juwairiyya taja Ummi suka tafi side ɗin ta da Hibba da ƴar aikinta suka shiga kitchen. Jalal kuwa shine yaje wurin Ya Jafar, don bashi mgni kamar yadda Jabeer ya umarceshi. Jamil kuwa waya yakeyi da sabuwar budurwarsa da ya samu. Wacce yake masifar sonta, Ko yaushe suna liƙe da juna a waya. Haroon kuwa a falon Jabeer ya zauna yana kallon lbrin CNN. Shi kuwa Sheykh Jabeer. A hankali ya wuce ta gaban Haroon. Gefen gabas ya fuskanta, inda labulaye sukayiwa wurin ƙawanya. A hankali yasa hannunshin ya yaye labulen. Wani ƙofa ya buɗe a . Sai ga wani ɗan siririn corridor. Shiga yayi, kana ya saki ƙofar ta koma ta mannu da ƙofar sai dai bata

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185