Chapter 31
Chapter 31
hira, sunzo dai-dai ƙofar gidansu Ahaji Umaru ne suka samu Ya Seyo da Hinde suna hirarsu. Koda suka wuce, murmushi Junaidu yayi tare da cewa. "Junainah sai yaushe zan fara zuwa muma muyi hira ne?". Cikin yin ƙasa da murya tace. "Sai na ƙara girma kafin nan Addana tayi aure". Murmushi yayi tare da cewa. "Ko dai bakya so nane". Da sauri cikin yarinta tace. "A a ina sonka mana". Dariyar jin daɗi sukayi baki ɗayansu, sun zo kusa da ƙofar gidansu. Ya Ba'ana ne sukayi kiciɓis dashi, murmushi yayi tare da cewa. "Yauwa Ƙanwaliya kuzo mu shiga in baki aike ki kaiwa Shatu". To sukace kana sukabi bayanshi, a tsakar gida suka samu, Iya Bultu majaifiyar Ya Ba'ana kena ƙatuwar mace baƙa ƙarin da ita, ga jajayen idanu, fuskarnan a haɗe ta kalli Junainah dake gaidata da fullanci cikin tsananin tsawa tace. "Ke tafi daga nan ƴan iskan fulani masu jajayen kunnuwa, dan uwarki Ni ba fillatace da zaki gaidani da fullanci, hegu kwarkwasa fidda mai gida a gidanshi yan iska masu kama da al'janu, in sha Allah ƙarshen zamanku a wannan yanki yana nan tafe". Da sauri Junainah ta koma bayan Junaidu, shi kuwa Junaidu wani irin tafasa zuciyarshi keyi akanme zata zagesu dan kawai sun gaidata da fullanci. Bukar ne mijinta wanda yake babarbaree ya kalleta tare da cewa. "Kuma dai al'barkacin fulanin kikeci". Ba'ana ne ya ɗan harari mahaifin nashi tare da waskewa yace. "Fulani kecin al'barkacin ta dai, tunda kowa ya sani wannan yankidai na Ɓachamawa ne, ba fulaninba". Cikin ƙarfin hali Junaidu yace. "Ato ai dai ba kyau aka bamuba da kuɗin mu aka bamu, kai kamma ya Ba'ana kaifa bawanmu ne tunda kai babarbarene". Wani irin suka kalawan yaron suka mishi a ƙahon zuciyarshi amman sai ya dake, ledan su ayaba da inabin ya bawa Junainah tare da cewa. "Uhu Junaidu kenan aini ba bakanuri bane ni ba Bachamene, Dan da in zama bawan fulani gwara in zama bawan karnuka". Haka nan kalamansu ke tafasa zuciyar Junainah da Junaidu, haka yasa fuska a hade suka juya suka tafi, har sunje bakin ƙofar fita Ba'ana yace musu. "Yauwa kuce mata ina zuwa yanzu bari inyi wonka". To sukace kawai suka fita suka tafi. A ƙofar gidansu suka tsaya gaban Ya Salmanu da Aysha, ledan Junainah ta ajiye a tsakiyarsu cikin jin haushi tace. "Addana gashi inji ya Ba'ana wai in kawo miki, yace kuma yanzu zaizo wai wonka kawai zaiyi". Tana kaiwa nan tayi cikin gida shi ma Junaidu Binta yayi a baya, har gabansu Ummey ya tsuguna suka gaisa kana yace. "To Ummey ga Ƙanwaliya na rakota Ya Ganin ne yace in rokata har cikin gida". Murmushi Ummey tayi tare da cewa. "Mun kuwa gode, ka gaida min Innonka kace mata, in Allah ya kaimu gobe ta turo min Hari tazo tamin kitso". Kanshi ya gyaɗa tare da cewa. "To saida Safe Bappa". Allah ya bamu al'khairi sukace baki ɗayansu. Daga nan ya fito, har ya wuce Ya Salmanu yace. "A a Junaidu zoka amshi tsarabar mana". Cikin girmamawa yace. "A a Ya Salmanu ya isheni". Cikin kula Salmanu yace. "Ni kam yaushenene zaku koma school?". Da sauri yace. "Saura kwana biyar hutunmu zai ƙare". "To Allah ya taimaka yanzu aji nawa kane". Murmushi ya ɗanyi tare da cewa. "Ina SS 3 ne fa, Ya Salmanu na kusa gamawa ai". "Masha Allah, Allah ya taimaka". Amin Amin yace kana ya juya ya tafi. Ita kuwa Shatu cikin tsoro ta kalli Ya Salmanu a hankali tace. "Ya Salmanu tashi ka tafi kada yazo ya sameka". Cikin harshen fillanci yace. "To shi mala'ikan ɗaukan raine? Ko dai so kike in guje masane Shatu, kina son ragon mijine?". A hankali tace. "A a Ya Salmanu zai cutar da kaine nake tsoro". Da sauri ya katseta da cewa. "Babu mai rayawa da kashewa sai Allah, ko yaya zaiyi bashi da ikon kasheni sai in kwana-nane ya ƙare. Ko ciwon kai bai isa ya samin ba". Shiru tayi tana kallonshi. Sai kuma tai maza ta miƙe tsaye ganin kamar daga sama aka jefo Ba'ana gabansu. Kallon kallon sukeyiwa juna shida Ya Salmanu, cikin wani irin mugun kallo mai cike da mugunta yayi kwaffa tare da cewa. "Uhummm Salmanu manyan gari, wato har an samu wani mai yar guntuwar jarumtar da zai iya haɗa so dani a kan Shatu, to bazan ce maka komaiba, amman ka shirya ranar litinin zamuyi shaɗi muddin ka cini na bar maka ita duniya da lahira, zan kuma bar garin Bani, da ƙasar nan gaba ɗaya zan koma ƙasar Cameroon, in kuwa na cika zaka bar duniya baki ɗayanta!". Cikin tsananin tsoro da kaɗuwa Shatu tace. "A a fa Ya Ba'ana wlh ba sona yakeyiba, karatu yake koya min". Da sauri Salmanu ya katseta da cewa. "Sonta nakeyi Ba'ana so kuma na aure, na kuma yarda zan shiga gasar Shaɗi da kai a ranar Litinin na amince". Wata irin muguwar dariya yayi wacce har tasa Aysha kowa cikin gida da gudu, shi kuwa saida yayi dariyar mai isarshi kana yace. "Lallai gidan Arɗo Yabani na gab da rasa motsin ɗana miji". Yana faɗin haka ya murza layar zananshi, sai gashi ya ɓaci. Cikin ƙarfin hali Salmanu ya nufi gida. Shi kuwa Ba'ana yana ɓacewa a tsakiyar dottawan Fadan Arɗo Yabani ya baiyana,. Wanda badon tsoffin makiyayene sun saba ganin abinda yafi haka ba tabbas watsawa zasuyi. So amman suka dake, cikin kamala Bappa ya kalleshi tare da cewa. "A a Ba'ana lfy kuwa?". Sunkuyar da kanshi yayi kamar mutumin kirki, cikin danne fushinsa yace. "Ku gafarceni Bappa nazone da batun neman al'farma fagen shaɗi, nida Salmanu ɗan Arɗo zamuyi gasa kan Shatu, na kuma yarda, muddin yayi nasara akaina na bar mishi Shatu zan kuma bar Rugar Bani baki ɗaya". Da sauri Bappa yace. "A a". Da sauri Arɗo Yabani yace. "A a Malam Liman ba komai, na amince na basu damar yin gasar Shaɗi mai nasara yaci gasar". Jin haka yasa dattawan nan duk sukayi shiru. Shi kuwa Ba'ana cikin tarin ƙeta jikinshi har tsuma yakeyi yana maganar zuci. "Uhumm zan kashe Salmanu kuwa kisa mafi muni zaku gane kurenku hegun fulani kunzo garin daba nakuba kun fisu dukiya zan kashe Salmanu irin kisar da ban taɓa yiwa waniba kisan da zaisa har abadan babu wanda zai sake cewa yana son Shatu". A zahiri kuwa, godiya yayi musu kana ya juya ya tafi. Nan dattawan kuma sukaci gaba da tattaunawa yadda Shaɗin zai kasance. Washe gari ranar asabar da sanyin safiya akayi shelar sanar da gasar Shaɗi da za'ayi jibi litinin, da kuma, waɗanda zasuyi gasar da sunan wacce za'ayi dan ita. Gaba ɗaya magarna ta cika Rugar Banin da kewayenta, duk wanda yaji yana firgici, Maman Salmanu kuwa tuni taketa kuka tana cewa ita kam so ake a ƙarar mata da yaranta an kashe mata Hashimu yanzu kuma ace da Salmanu za'ayi gasar Shaɗi da mutun da sun san ba'a taɓa nasara a kansa a., Mutanen sauran rugogin Fulani dake mutunci da Arɗo Yabani kab sai gudumowar magunguna suke kawo na dauri dan a tsuma jikin Salmanu. Sosai kuwa babanshi da yayunshi mata da maza da abokanshi keta tsumashi. Shi kuwa Ba'ana tun ranar ya ɗauki tunƙur ƙasar da yake tsuma bulalinshi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185