Chapter 138
Chapter 138
mu jirata anan in dai zataje ita ɗayan". Kanshi ya dafe tare da cewa. "To wai Umaymah mu bayaninta ne da zamu tsaya muna jiranta". Ummi ce ta mishi alamun yayi haƙuri ya yarda. Shiru yayi tare da komawa gefen jerin bishi yoyin namiji kwanɗa ya zauna bisa kujerun silver dake zagaye da wurin wanda ko wani side akwaisu. Itama Umaymah da Ummi zuwa sukayi suka zauna. Ita kuwa Shatu a hankali ta fara taku ta nufi cikin farfajiyar, suna hangota har ta isa bakin ƙofar. turawa tayi ta shiga, kana ta maida ƙofar ta rufe. Bayan kamar 37 minutes ta fito. Cikin wani irin tafiya mai baiyana tsantsar jin daɗi, fuska cike da fara'a ta nufosu. A hankali ta isa gabanshi ciki ɗan ɗaga murya tace. "Na bata haƙuri ta yafe min, ta samin al'barka. Kaima kayi haƙuri ka yafe min". Da mamaki suka kalleta. Shi kuwa Sheykh Jabeer wari irin kallon tuhuma yayi mata, kana ya miƙe tsaye tare da cewa. "In ma ƙarya kikayi, ni ba'amin ƙarya". Sai ya kuma kalli Umaymah tare da cewa. "Umaymah kuje ki ƙarisa shirinki bari inje wurin Hajia Mama". To tace kana taja hannun Shatu suka tafi. Shi kuwa da Ummi suka nufi cikin Side ɗin Mama. Bayan sallan isha'i, cike suke a falon. Gaba dayansu, Umaymah zaune a tsakiyarsu da jakarta, Sheykh Jabeer na yi mata addu'o'in isa lfy suna amsawa da Amin Amin. Bayan sun shafa addu'o'in ne ta miƙe tsaye, tare da kallon su baki ɗaya, murya na rawa tace. "Jazlaan zan tafi, zan bar hankali na, a nan ko na koma banda nitsuwa, kullum ina cikin taraddadin abubuwanda yake faruwa, Jazlaan na sani kaine GARKUWAR yayanka da ƙanneka. Ga wani sabon nauyi ya ƙarun maka. Aysha baƙuwace bata san komaiba kam al'amuran Masarautar Joɗa, dan Allah in tayi abinda ba dai-dai ba kuyi mata uzuri. Ita komai a sabon abu zata ganshi abinda bata taɓa ganiba. Mun rabata da iyayenta yayunta ƙannenta mun kawota tsakiyarmu, mu kasance mata adalan masu masauƙi. Na sani Jazlaan ka fini sanin haka da kuma haƙƙoƙinta da suka rataya gareka." Sai ta kuma kalli sauran yaran yar uwarta ɗin tace. "Jalal, Jamil, Aysha matsayin yar uwarku take, yayarku ce, matar yayanku. Bana son raini especially kai Jalal, ban gamsu da irin mu'amalat ɗin ka da itaba. Babu wanda yake nuna min yadda nakeso a kanta sai Jafar, a duk sanda ya ganta zaiyi mata murmushi kamar yadda yake min, in yaga bata nan zaiyi ta dube-duben da nasan da yanada baki zai tambayeni lfyarta. Zan bar Hibba saboda itane, bana son taji kanta a matsayin bare." Shiru sukayi gaba ɗayansu sabida yadda take kuka da yin mgna tamkar mai bar musu wasiya, ko wacce wani tsohon damuwa ya taso mata. Sharce hawayenta tayi tare da cewa. "Ummin Jabeer zan tafi zan barki da sauran aiki, dan Allah ki kula da Shatu da mu'amalarta da Hajia Mama, ki nuna mata uwar miji ba abun rainawa bace". Sai kuma ta miƙowa Aysha da taketa kuka hannun ta jawota tsaye ruggume ta tayi cikin zubda hawaye tace. "I dan akaga damuna ana zaton yabanya zatayi kyau, kallon damuna nakeyi miki a cikin ahlin yar uwata. Ina jin zaki zamo mana haske mai yaye duhun daya maye ganinmu, tun kafin yau ni na sanki a mafarkina Allah ke nuna min ke a matsayin matar Jazlaan ɗin na, kuma Allah yana nunamin abubuwa da dama a kanki a cikin mafarkaina, wasu kuma sunma tabbata na gansu. dan Allah ki riƙe min Jazlaan amana, ki lura da ƙannenshi yadda zaki lura da naki ƙannen ki kula da Jafar kada ki tsoraceshi bazai cutar da keba ki ɗaukeshi a Matsayin wa". Cikin zubda hawaye Shatu tace. "In Sha Allah Umaymah zan kiyaye zan kuma zamo yadda kike zatonta, koda sanadin haka zan rasa jigo biyu na rayuwata rai da lafiya ta". Kalaman Umaymah da Aysha kuramen baƙine da su kansu ɗaya bata fahimci abinda ɗaya take nufiba, hakama ɗayar, bare su Jalal dake tsaye. Jawo Hibba tayi ta haɗa su ta ruggume, kana ta jawo Juwairiyya tace. "Ku duk yara nane ku zauna lfy". Gaba ɗaya da to suka amsa. Cikin sauri Umaymah ta sakesu kana ta miƙa wa Ummi hannu sukayi musababa, tare da bar mata sallahun yaran. Daga nan suka fita, gaba ɗayansu. Sai Shatu da Hibba da suke kuka, ganin hakane Ummi ta dawo ta zauna dasu. Jabeer da Jafar da Umaymah kuwa Side ɗin Mama sukaje, tayi sallama da ita, suka rabu suna hawaye. Daga nan Side ɗin Lamiɗo da Gimbiyar shi sukaje. Nan sukayi sallama dasu kana suka fito, inda suka samu Jamil da Jalal sun kawo musu motoci. Daga nan suka shiga suka tafi Airport tare da rakiyar motocin fadawa guda uku ya zama motoci biyar ne suka tafi kaita Airport. A gida kuwa, da kyar Ummi ta samu ta lallashi Shatu da Hibba da cewa in basuyi shiruba, zata, sa akai Hibba Airport ta tafi da Umaymah. jin hakane yasa Hibba tayi shiru. Ita kuwa Shatu dama ba kuka mai sauti takeyi ba, zubda hawaye takeyi. Ƙarfe tara dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi zuwa jihar Tsinako. A gida kuwa tuni Shatu da Hibba sun shiga kuma har sunyi bacci sabida kukan da sukayi. Ita kuwa Ummi tana falo, saida taga dawowarsu sannan taje ta shiga ɗakinta dan yanzu ta dawo da zama a nan kenan ɗakin da Umaymah ke sauƙa in tazo. Washe gari ranar asabar kuwa, haka suka wuni gidan shiru ba daɗi gaba e kewar Umaymah ta hanasu jin daɗin gidan. Ranar ne kuma duban forko na watan Ramadan. Tunda magriba tayi, al'ummar musulmai keta cekinta labarin ganin wata. Wannan ya tambayi wancan wancan ya tambayi waccan. Jira kawai akeyi aji lbri ko gani. Yayinda duk irin wannan rana duk inda yanki musulmai suke a faɗin duniya suna jimirin da tsumayin lbri. A wasu wuraren har matasa maza da dattawan kanyi dandazon da fuskanta yamma dan ganin watan Har dai akayi sallan magriba babu ƙaƙƙarfan lbrin ganin wata. Bayan anyi sallan isha'i ne, Sarki Nuruddeen Lamiɗo kenan ya tara hakima shi a fada suna jiran ko akwai ta inda labari zai riskesu. Kasan cewar ana yanayin damuna ne yasa ba ko ina keda yaƙinin ganin watarba. Sheykh Jabeer kuwa, wanda ranar bai samu yayi salla a masallacin Masarautar Joɗa ba. Sabida wata ƴar tafiyar da yayi, sai bayan Isha'i ya dawo. Kai tsaye Side ɗinsa ya wuce. Yana shiga falon wayarshi dake cikin al'jihunsa ta fara suwa a hankali. Gefen Ummi ya iso tare dayi mata sallama. cikin kula tace. "Sai yanzu?". Kai ya gyaɗa mata yana mai amsa wayar. Sannu da hanya tace mishi. Cikin sauƙe numfashin alamun gajiya yace. "Yauwa Ummi sannu da aiki". Sai kuma ya kara wayar akunnen shi cikin nitsuwa yace. "Wa alaikassalam". Ɗan jim yayi kana yace. "Alhamdulillah". ya ƙarshe mgnar yana shiga cikin falonshi. Shatu kuwa dake gefen Ummi shiru tayi tare da binshi da ido. A can falon shi kuwa zama yayi bisa kujera tare da fara zare al'kyabbar daka hannunshi, wayar na kunnenshi yake cewa. "Eh Jadda Alhamdulillah rahotanni sun nuna cikin Ɓadamaya al'umma da yawa sunga watan Ramadan. Kuma nima naga watan Ramadan da idona". Cikin jin daɗi Jadda yace.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185