Chapter 136
Chapter 136
Hibba da tun ɗazu ta shigo tana gefenta ne, ta ɗan kalleta cikin sanyi tace. "Aunty Shatu, meyasa kikace bakya jin daɗin zama a gidan nan? Munayi miki wani abune?". Cikin zubda hawaye ta jujjuya mata kai. Hibba bazata fahimci halin da take ciki ba, bazata gane matsalar rayuwarta ba. Ita kuwa Hibba cikin sanyi tace. "Aunty Shatu nima ƙanwarki ce, duk abinda zakisa Junainah tayi miki nima kisani zan miki kinji ko". Cikin share hawayenta tace. "To Hibba ngd". Murmushi Hibba tayi tare da cewa. "Yauwa kuma Umaymah ta aika Ya Jamil ya sayo miki sabuwar waya iPhone". Cikin sanyi da son tsaida hawayenta tace. "Ngd". Haka yammacin ranar ta yishi a bedroom ɗin ta. Sai Hibba dake ɗebe mata kewa ne. Da Umaymah taga basu fito bane itama taje. Washe Gari yau Jumma'a, kuma yaune ta cika sati ɗaya cib a gida. Kuma tunda yazo gidan sau uku taga Sheykh Jabeer, tun randa ya wucesu, suna batun abinci bata sake ganinshi ba, koda a gilme ne. Yanzu ta saba da Umaymah Sosai hakama Ummi Ita da Hibba kuwa shaƙuwa ta fara ƙarfi a tsakaninsu. Tana jin Hibba kamar Junainah. Jamil da Jalal Haroon suna ɗan zama asha hira dasu. Yau ne kuma Haroon zai tafi Leddi julɓe, sabida yayi masifar kewan Jannart ɗin shi, wacce taƙe ƙanwace ga Aunty Juwairiyya, kuma ƙawance ga Ibrahim. Ƙarfe ɗaya dai-dai, Sheykh Jabeer, ne tsaye gaban dreesing mirror yana fesa turare bayan ya gama shirin jummarsa tsab. Yau shigar baƙar Al'kebbar da farar jallabiya yayi. Yayi wani irin kyau mai cike da sheƙi. Kusan a tare suka jero da Haroon wanda yake cikin shigar ƙananan kaya. Su kuwa suna falon suna, zaune. Jamil da Jalal da Ya Jafar kuwa suna tsaye alamun fitowar Sheykh suke jira. A hankali Shatu ta ɗan ɗago kanta jin wani irin masifeffen ƙamshi mai daɗin shaƙa. Da sauri ta janye ƙwayar idanunta, Sabida idonta da suka faɗa cikin ƙwayar idanunshi. Wanda shi kuwa Jalal yake kallo ganin wani shegen wondo wai shi crezi ne ko meye ne oho, duk yana ɓuɓɓule har kana iya ganin farar fatar cinyarsa. ga saɓulellen wonɗo ga kafurin aski. fuskarshi ya tsuke tare da jan gajeren tsaki wanda shiyasa Jalal juyawa, ya nufi hanyar fita yana cewa. "To Ni banifa da manyan kayan nan, yanzu bari inje in duba ko inada jallabiya sai in saka a kai zan biyoku daga baya." Da ido suka bishi. Haroon da Jamil kuwa murmushi sukayi. A haka suka fita suka tafi. Har sunje bakin ƙofar fita ba tare da ya juyoba yace. "Umaymah ku tashi lokacin salla yayi". Ya ƙarishe mgnar suna fita To tace. Kana suma su Ummi suka nufi ɗakinsu. Aunty Juwairiyya kuma ta wuce Side ɗinta. Ita kuwa Shatu da Hibba suka tafi ɗalinta. Hibba ce ta fara shiga tayi al'wala. Sannan itama Shatu ta shiga. Tana fitowa daga bathroom ɗin tayi wani irin....! Uhummmmmm tuni mun gama shimfiɗan lbrin GARKUWA yanzu dai muna cikene dumu-dumu . By *GARKUWAR FULANI* Ta kamo hannun Jalal da ya miƙe tsaye da nufin yarfa mata mari. Cikin wani irin masifeffen tsana, Hajia Mama takalli Shatu. Kana da sauri ta juya ta nufi hanyar fita. Sheykh da tunda ya fito yake tsaye tamkar an dashi ne, yayi saurin bin bayanta tare da cewa. "Hajia Mama! Mama!! Mama dan Allah kiyi haƙuri, kizo karki fita Please Mama karki fita, babu wata halitta da zata miki iyaka da sashina, in kin tafi kenan kinbi umarninta." Cikin tashin hankali yake waɗannan kalaman yana mai binta a baya. Jamil kuwa miƙewa tsaye yayi ya zubawa Shatu idanu tamkar zasu faɗo ƙasa. Aunty Juwairiyya kuwa, wani irin kallo mai sarƙafe da ma'anoni takeyiwa Shatu. Ya Jafar kuwa wani irin kallo mai surke da murmushin jin daɗi yakeyiwa Aysha. Ummi kuwa tuni jikinta rawa yakeyi da abinda ya faru. Imran, Ya Hashim, kuwa ido suka zubawa sarautar Allah. Hibba kuwa kuka takeyi tare da riƙo hannun Shatu tana ja tare da cewa. "Aunty Aysha ki bari, Mamace fa! Kizo mu tafi ɗaki". Tanayi tana jan hannun Shatu da ƙarfin tsiya, dole yasa Shatu ta bita a baya. Umaymah kuwa wani irin tashin hankali da tafasan zuciyane ya dirar mata lokaci ɗaya. Da wani irin kallo tabi bayan Aysha dashi. Duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali. Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi. Sun daɗe a haka, da kyar dai Cikin wani irin tafasan zuciya ta saki hannun Jalal. Tare da komawa ta zauna. Da yatsa ta nuna musu hanyar fita daga falon. Murya a hargitse tace. "Kul kada ka sake tunanin gigin ɗaga kayi nufin taɓa lfyar Aysha, bana so kul. Maza Ku tafi masallaci". Sai lokacin suka jiyo sautin muryar Jabeer yana Hudba. Wanda daga jin muryarsa kasan yana cikin baƙin ciki. Wani irin numfarfashi Jalal ya sabke tare da yin koffa kana ya juya ya nufi hanyar fita shi matsalarsa meyasa Umaymah na mgn Aysha na mgn Umaymah na hanata abu tanayi. Haka su Jamil da su Imran da ya Hashim da Ya Jafar suka fita. Ita kuwa Aunty Juwairiyya wani irin tashi tayi ta fita ta nufi Side ɗin ta. Ya zama Ummi da Umaymah ne kaɗai suka rage a falon. Shiru sukayi tamkar ruwa ya cin yesu. "Uhuhhmmmm". Umaymah ta fesar da wani zazzafan numfashi mai ɗumi. Hakama Ummi tagwayen numfarfashi masu nauyi ta sauƙe. Kallon juna sukayi, cikin shiga al'hini wannan al'amari cikin tsoro da karaya Umaymah tace. "Toh wai meye hakan? Meke faruwa ne? Me hakan yake nufi? Kaina ya kulle. Wani zagon kasan kuma aka shirya tsakanin Shatu da Hajia Mama ko dai dama da zagon ƙasan ne?. Wake saƙa gadar zare, muna na bi ta kai ya rubta da mu". Wani numfashin Ummi ta fesar tare da cewa. "Tabbas akwai babban al'amarin dake faruwa wanda bamu saniba Ni tsorona ɗaya kada a juya ƙoƙwalwar yar mutane." Shiru sukayi cikin ta'ajjudin al'amarin. A hankali suka miƙe a tare suka nufi ɗakinsu jin har an idar da sallan a masallacin. Al'wala sukayi kana sukayi salla daga bisani suka, fara tattauna wani abu na sirrin masarautar Joɗa. A cikin ɗakin Shatu kuwa, tunda suka shiga ta kwanta bisa gado. Bacci tayi bacci, hakama Hibba. Sai ƙarfe uku dai-dai Shatu ta tashi. Cikin kasalan baccin da bai gama isarta ba, ta miƙe ta shiga bathroom. Wonka tayi tare da al'wala. Bayan ta fitone, ta tada Hibba, ita kuma ta kabbarta sallah. Kafin ta idarma Hibba ta fito, gefenta tazo itama ta kabbarta sallan. Basu tashi bisa sallayan ba, sukaji kiran aallan la'asar. Haka yasa sukayi sallan. Suna idarwa Hibba ta miƙe ta nufi ɗakin Umaymah. Ita kuwa Shatu ninke sallayar tayi kana ta dawo gaban dreesing mirror. Mai ta shafa tare da ɗan murza fauda a fuskarta, kama ta shafa man baki. A cikin sanyi taje gaban drower'nta, hannu tasa ta buɗe drower'r, wata tattausar doguwar riga mai masifar kyau ta zaro. Kalar rigar Black blue mai sheƙi, saman rigar a ɗan tsuke daga ƙasan ƙugunta kuma a buɗe, yanada wasu duwasu kamar na Daimond daga sama har ƙasan gaban rigar. Hannunta kuma masu faɗi. Tayi kyau sosai cikin rigar, dogon gashinta ta haɗa ta tubke wuri ɗaya ta kitse jelar kana ta nannaɗe jelar a ƙeyarta, sannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185