Skip to content

Chapter 174

Chapter 174

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

bayan sun gaisa ne yace. "Uhumm Umaymah wai me kika sani ne ya faru da wannan yariyar shekaran jiya?". Cikin tsoro da son kauda batun Umaymah tace. "Wacce yarinyar kuma?". Fuska ya ɗan tsuke yace. "Waccar yarinyar dai". "To bata da sunane ita". Ta kuma ce mishi. Cikin gajiya da batun yace. "To ni ba sanin sunanta nayiba, baku gaya min sunanta ba." Wani irin murmushi Umaymah tayi tare da cewa. "Ban gane bafa Jazlaan". Hannunshi yasa ya ɗan shafi sajenshi. Yana mai son yasan meya sameta, meya faru da ita, shiyasa a hankali yace. "Yarinyar dai da kike cewa ɗiyarki!." Kai Umaymah ta jinjina tare da cewa. "Laah ni nama mance bamuyi mgnarba, ran sallane tayi aiki ta gaji tunda safe bataci komaiba to ashe tanada olsa shine fa, ta shiga ɗakinka zatayi maka shara ta faɗi ta suma, da kyar aka samu ta farfaɗo suanta kuma Aysha". Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa. "Shirme in banda sakarci da raki mutun ya bar kansa da yunwa da gajiyan aiki mutun har ya suma". Ya ƙarashe mgnar yana jinjina darajar sunanta a ranshi. Cikin jin daɗin bai tsananta bincike ba tace. "Akwai wani abune?". Gyara zamanshi yayi tare da cewa. "Wannan mahaukaciyar Gimbiya Saudatunce tazo take cewa wai taji lbrin ta haukace". Daga nan ya kauda zancen. A hankali ya miƙe yana riƙe da wayar a kunne shi. Dinning area ya nufa. Murmushi yayi gano tabbas akwai abinda Umaymah ke ɓoye mishi. Hannunshi yasa cikin zirin zirin igiyoyi masu duwatsu masu daraja sheƙin Daimond da sukayi Dinning area ɗinshi a madadin labule. A hankali yasa hannunshin kan na'urar CCTV camera dake liƙe a gefen inda yake ajiye key, wanda duk abinda za'ayi a falon zai gani. Cikin sanyi yace. "Uhummm Umaymah kiyi mata faɗafa, ta dena hawan ƙawara kan mutanen masarautar Joɗa, ta kiyayi kanta da faɗa da magautana zasu ilatata. Bata san komaiba a kaina ta tsaya matsayin baƙuwa Umaymah zafa suyi mata illa". Ya ƙare mgnar a hankali. System ɗinshi dake kan Dinning table ɗin ya jawo. kana yaja kujera ya zauna ya fara haɗa na'urar. Ita kuwa Umaymah a hankali tace. "To ya zatayi tunda ƙaddara ta kasantar da ita matsayin matarka, ko ita kurmace dole sai sun nemi yi mata illa sun sabautata. Dole kasata cikin jerin mutanen da ka zame musu GARKUWA a masarautar Joɗa, tunda ita dai matarka ce, amanarka kuma". Shiru yayi yana jinta yana mai kallon fuskar System ɗinshi date ɗin shekaran jiya ya shiga. ai kuwa Shatu ya fara cin karo da ita tana share falon da goge ko ina. Sai kuma lokacin da suka shigo ita da Jamil da Hibba suka nufi bedroom ɗin sa. A hankali yace. "Uhmmm Umaymah sai anjima zan kiraki". To tace kana ya katse kiran. Ido ya zuwa System ɗinshi. tsaki yaja karo na forko da yaji da ya haɗa na'urar da cikin ɗakinshi. Gashi yanzu baya ganinsu sai dai ihun Hibba, da fitowa da tayi da gudu ta kira Ummi da yadda suka shigo da Aunty Juwairiyya. Kanshi ya gyaɗa lokacin da yaga sun fito a hankali ya rufe System ɗinshi. Dafe kanshi yayi yana nazari. Ya dade a nan sosai kana ya koma ɗakin shi. Da dare misalin karfe sha ɗaya na dare saura. Shatu ta kalli Hibba dake konce tuni tayi bacci. Yasa ta miƙa a hankali ta nufi ɗakin Ummi. A bakin ƙofar ta tsaya a hankali tayi sallama. Cikin mamaki Ummi dake zaune bisa sallaya ta idar da shafa'i da wutri kenan taji sallamarta. Juyowa tayi tare da amsawa tace. "Shatu". A hankali tace. "Na'am Ummi". Cikin mamaki tace. "Lfy kuwa shigo mana". A hankali ta shigo tare da cewa. "Lfy lau Ummi, nazo wurinki ne." "To". tace tare da nuna mata wurin zama bakin gadonta. A hankali ta ƙaraso kusa da ita, Gabanta ta zauna kan sallayan cikin nitsuwa tace. "Ummi kiyi haƙuri ko zakiyi bacci na hanaki". Da sauri ta girgiza mata kai alamar a a. Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa. "To Alhamdulillah". Sai kuma tayi shiru. A hankali Ummi tace. "Kina buƙatar wani abune?". Cikin nitsuwa tace. "Uhum Ummi dama tambayarki nake son yi". Gyara zama Ummi tayi kana tace. "Ina jinki". Itama zamanta ta gyara a hankali tace. "Dan Allah Ummi in ba damuwa, dan Allah da Manzonsa ki sanar dani abinda Allah ya sanar dake a kan masarautar Joɗa mana. Ummi kaina na kullewa da mutanen masarautar Joɗa, ban gane banbanci su da dankantakarsu da kuma. Alaƙarsu ba". Wani irin dogon ajiyan zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa. "To Shatu ai kin gama komai tunda kika haɗani da Allah da Manzonsa. Kuma dama nace miki ki tambayeni duk abinda baki gane ba, zan gaya miki. To amman akwai wani abun sirrine garesu masarautar in na faɗa kamar cin amarsu ne, wani abun kuma nima kaina ban sanshi ba. Hannun Ummi ta riƙe tare da zubda hawaye tace. "Ummi gaya min yadda masarautar Joɗa take ko zan san irin zama da takun da zanyi da mutane da ɗaukar mataki kan abinda ke faruwa". A hankali Ummi ta gyara zamanta. Ta jingina da jikin gado. Kana itama Shatu ta gyara zamanta ya zama suna fuskantar juna da kyau. Cikin sanyi Ummi ta fara bata lbrin. *Masarautar Joɗa* tsohuwar masarautace. wacce tun kafin zuwan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ƙasashen Afrika tana kafe da ƙafanta. Kuma masarautar Fulɓe ce tun a wancan lokacin. Lokacin da Shehu Usman Ɗanfodiyi ya iso nan ƙasashen hausa ya basu musulunci ya kafa tutocinsa tako ina tako wacce masarauta. A lokacin Masarautar Joɗa sunanta masarautar Fulɓe. Kuma lokacin Sarki Sule ne a kan karagar mulki. Baban Joɗa kenan wanda yake shi Joɗa shine kakan sarkinmu na yanzu wato Lamiɗo. A lokacin sarki Sule yanada ƙarfin mulki yana da mata huɗu ƙwar-ƙwara biyar. Allah ya azurtashi da arzikin yara a ƙalla sunfi hamsin a cikin matansa huɗu na aure. Akwai wata ɗaya da ake kira Gimbiya sumaye ƴar sarkin kal'anace. Gimbiya Sumaye inrin matannane da Allah ke jarabta da haihuwar wabi. Bima'ana tana haihuwa kuma yaran na rasuwa. A haka har ta haifi yara kusa goma kuma bata da rayeyye ko ɗaya. Cikin ƙwar-ƙwaran sarki Sule ne ɗaya ta ɗauki ɗanta na miji ta bata halak malak kwanan yaron uku a hannunta ya rasu. Wata cikinsu ta kuma bata still shima kwananshi uku ya rasu. A haka duk ƙwar-ƙwaran sarki Sule saida suka bata yara suna rasuwa. Daga nan uwar gidan Sarki Sule wacce take babarbariya ce. Tasa mata suna cikin wasa na tsakanin Fulani da bare-bari amman a zahiri da gaske takeyi. Gsky mai tafiya da wasa kenan. Sai ta sawa Gimbiya Sumaye suna da fillanci wai *Ɓadamaya* ma'ana wai duk wanda ya matso kusa da ita zai mutu, ko wanda ya bata riƙon ɗa kowa kwana uku ne mutuwa zaiyi. Kamar da wasa sunanta ya zama Gimbiya Ɓadamaya. Mutanen masarautar akayi ta mata izgili da habaici. Takan zauna tayi ta kuka. babu mai rarrashi dan ita masarautarsu nada nisa a lokacin kuma babu ko Radio bare waya. Anan Allah ya bata wani ciki ta haifi ɗan ta namiji. Akasa mishi suna Umar faruq. Sai Gimbiya Sumaye take kiranshi da Joɗa ma'anar Joɗa shine zauna. Da haka sai aka maida abun

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185