Chapter 17
Chapter 17
a nan tasa drever ya tsaya ta sayi Junainah sweet. Biyar da mintuna goma dai-dai suka isa kwanar mashigar Rukarsu Rugar Bani. Cikin tsoron kada Ba'ana yaga wani yazo ya sauketa ya masa rashin mutunci, tace. Ya sauketa a nan ba musu ya sauketa dan ai inda sabo ya saba. Tana fita taja jakarta, ta rataya kana ta gyara tarhan da tayiwa kanta. Shi kuma ya juya ya tafi. A hankali ta zubawa yankin garin nasu ido, ko ina yayi kore shar, yabanya da ni'imar damina ta wadaci ko ina, wata iriyar sassanyar iska mai daɗin ke ratsa mata jiki da zuciya. Ajiyan zuciya ta sauƙe a hankali tare da lumshe idanunta kana ta buɗe hannayenta cikin begen gida tace. "Rayuwar ƙauye mu akwai daɗeeee". Ido ta buɗe tana kallon tako ina makiyayen rugarsune suketa dawowa daga kiwo, Dabbobi saffan-saffan sunata dawowa, garin yayi lum ga wani hadari mai ƙarfi daya keto, daga ƙasan dutsen da yayiwa Kyauyen ko ince Rugar Bani ƙawanya, a hankali take taku tana bin kan faffaɗan hanyan da makiyayan sukayishi bi ma'ana burtali kenan. Taku take yayinda gefen hagunta wutsiyar kogin Shikan ne konce iya ganinta, gefen dama kuwa Garden ɗinsune mai girma wanda yasa sanyin wurin yake yawaita, sauri ta ɗan farayi sabida akwai ƴar tazara kana kuma gashi magriba ta karato. Tana cikin tafiya tana rataye da jakarta, kamar daga sama taga wulgawar inuwan mutun, cikin sauri ta zaro idonta ta kalli gefen hagu da damanta, Ba kowa ganin hakane yasa taci gaba da tafiyarta cikin dakiya, taku uku tayi ana huɗu taji ansa hannu an amshi jakarta, da sauri ta juyo ta kalli gefen da aka amshi jakar. Babu kowa a wurin kuma ga jakarta a rataye ita ɗaya tana binta suna tafiya a jere. Cikin wani irin fargaba tsaro kaɗuwa da tsananin firgita ta....! By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 *GARKUWA* PAGE 6 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 *FREE PAGE* *Kada dai ku manta har yanzu Free page kuke samu, wanda zamu datseshi cikin ko wanne lokacin, hamzarta ku biya darinki uku kacal ko 1k ga mai dama da niya, domin samun cikekken labarin daki-daki cikin salama. Turo kuɗin ta asusuna na Jaiz. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidan biyanki ta layina 09097853276. In ya zama larura ba halin turawa ta ac turo katin mtn na ɗari uku, ko na 1k ɗin domin ci gaban lbrin GARKUWA. Sayan na gari maida kuɗi gida. Ina mai yi muku fatan al'khairi masoyana makaranta, ina sonku domin Allah ina fatan kyautata alaƙa ta da kowa sabida nasan ko ina raye watarana zan zama tarihi a duniyar marubuta, sabida yauda gobe ta wuce watsa, in ba mutuwa akwai tsufa. Kana dole watan wata rana gwanayen zasu zama tsoffin hannu kana yan koyo na yanzu su zama gwanayen, domin da babu yan koyo tabbas da gwanayen sun ƙare, inada fata da burin ganin al'ƙaluman Adabi sun inƙanta baki ɗayansu ba nawa kaɗaiba, tsarkake rubutu ki/ka domin kece madubin wata marubuciya da zata iya tasowa nan gaba.Ina mai muku fatan al'khairi🙏🏻🤝🏻🥰😘makaranta da marubuta* Cikin firgita da tsoron tace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani'imanwakil, lailaha'illalahu Muhammadurasulillahi sallahu'alaihi wasallam Auzubikalimatillahi ta'ammati min sharrin ma khalaƙa Allahum...". Da sauri ta koma da baya ba tare da karisa addu'ar ƙarshen data faro ɗinba. Ganin Ba'ana ne tsaye a gabanta cikin wata iriyar dariya yace. "Ke ki nitsu masoyinki ne ke gadinki, gsky *Mata* dole in rage miki wannan tsoron, domin matar Ba'ana bazata kasance matsoraciya ba, dole in ƙara tsumaki in dafaki da kyau, ta yadda idanunki zasu buɗe da kyau". Cikin karkarwar da bai bar jikintaba tace. "Bana so. Ni ka barnin da tsorona, nifa macece ba namiji irinka ba, kaine ke shiga daji da tsaunuka kake buƙatar wani abu ya kare ka". Da sauri Ba'ana farin kekyawan babarbare ya matso gareta cikin shigar fulanin da ya zame mushi sutura yace. "Mata ke bakya buƙatar kariyar ne?." Da sauri ta gyaɗa mishi kai tare da cewa. "Ni na yarda cewa addu'a'u saiful muminin ne, kuma shi na riƙe, so bana buƙatar waɗannan asirce asircen". Murmushi yayi tare da murza ƙafarshi ta hagu sai gashi ya zama kamar inuwa ba mutun ya ɓacewa ganinta ɓat. Da sauri ta rufe idanunta tare da cewa. "Bana so ina tsoro ka dena caccanza kamanni a gabana". Da sauri tayi baya ganinshi gab da ita, Dariyar ƙeta yayi tare da cewa. "Baga irinta nanba, idonki baya iya ganin komai, dole zan ƙara haɗaki irin haɗin da zaki ke banbance mai layar ɓata data zana da jingina bongo da dama duk mutun mai juyewa i zuwa wata halittar". Ya karishe mgnar yana nuna mata hanya alamun su tafi. A hankali suka jera suna tafiya a tare. Allah ya sani Ba'ana yana masifar son Shatu tun tana ƴar ƙaramar yarinya, yana sonto irin sonda ko ƙudane in ya sauƙa kanta in dai namiji ne to zai kasheshi, ganinta kusa dashi kawai yana sashi jin daɗi, duk muguntarsa baya yi mata, duk duniya babu wanda Ba'ana ya yarda da shi bare yasan sirrin makarin sihirurrukan dake jikinshi. Ba'ana mutunne da yake tamkar al'janu sabida yawan ta'ammali da sihiri kai harma da tsafi, Ba'ana riƙeƙƙen tantirin ɓarawone wanda ya buwayi Fulani al'ummar Afirka gaba ɗayanta, da sace-sacen dabbobinshi, muddin ya ƙella ido yaga garken shanunka yayi mishi, to tazarar kilo mita talatin da biyar yake tsayuwa da garken, yayi FITO ɗaya tak, wallahi duk sihirin kafiyar garkenka zai kunce kuma duk inda yayi shanayenka zasu bishi a baya da kuma wannan tazarar, da zaran kasa Hukuma cikin zancen kuma yana burza layar ɓatanshi dashi da dabbobin duk zasu ɓace. Duk garken da yaga yayi mishi to sai ya kwashesu tsan da wannan ya tara dukiyar dabbobin da shi kanshi baisan adadinshiba babu ƙasar da bashi da makiyayanshi kamar su. Chadi, Nijer, Cameroon, Ghana, Gabon, Maroco, Senigal, da dai sauran kasashen makusantanmu kuma masu dabbobi, hikimar da yakeyi, muddin ya saci shanayen ƙasar Niger to sai ya cillasu ƙasar Senegal, in kuma makiyayanshi na ƙasar Sanigal sukayi sata to sai ya turo shanayen ƙasar Gabon, haka dai yake banbance mazauninsu. Sai dai garin zamansa ɗaya ne Rugar Bani, inda nan aka haifeshi mahaifinshi Bukar wanda babarbaren Norba ne saye da sayar da kanwane ya ajiyeshi cikin rugar FULANI shiyasa ya zama dilan saida kanwa, sabida dole duk bafulatani makiyayi yana ta'ammali da kanwa dan ana zubawa dabobbi susha a ruwa ko asa musu a dusa ko harawa yana musu mgni. Ba'ana ya shiga cikin Fulani ya saje dasu. Yayinda hakan ya bashi damar da duk duniya ake ɗaukarshi matsayin bafulatani, koda yake hakan baya rasa nasaba, da kallon da mutanen duniya sukewa duk mutumin da akaga shanu, tumaki a gabanshi tofa ko wacce gabilace shi, ya zama bafulatani, wanda kuma sam ba haka abin yakeba. Mahaifiyar Ba'ana ɗaya daga cikin ƙabilar ɓachama ce, wacce Bukar ya aura tana a matsayinta na anniya, koda kuwa suka haihu ɗan su. Bukar ya rinjaye ta Ba'ana ya kasance musulmi, sai daifa a baɗini baƙar zuciyarsa da aiyikansa na kafuraine, sata kuwa a wurin babarsa ya gada. Ba'ana kekyawan mutun ne ajin forko wanda ya gaji wannan kyan ne a kakarshi mahaifiyar babanshi wacce take shuwa Arabce, koda maƙiyinshi yasan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185