Chapter 111
Chapter 111
lfy. Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako ɗaya tak. Wannane ya ƙara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki. A hankali Bappa yace. "Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi". Idonshi ya ɗan ɗago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace. "Amin ya Allah". Bukar ne ya ɗan kalleshi tare da cewa. "Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka". A daƙile Jabeer yace. "Inuwa tace". Galadima ne ya ɗan kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna. Kwaffa yayi tare da murtuke fuska. A hankali su Arɗo bani suka koma wurin zamansu. Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba'ana a tsakiyar fili. Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi. Haka yasa cikin karsashi da buɗa ƙwanji yayi wani irin tsalle ya faɗo tsakiyar taron. Juyi ya farayi da ihu da ɗaga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji. "Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar ƙasar nan, zan koma ƙasar Cameroon nida ƙasar nan sai dai ziyara, Dan ba'a yin jarumai biyu a gari ɗaya kamar yadda ba'a sarakuna biyu a gari ɗaya." Wani irin ihu da shewa gaba ɗaya mutanen suka ruɗe dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba'ana. Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa Arɗo Bani dasu Bappa kamar su haɗiye haƙorinsu dan daɗi. Arɗo Bani ne ya ronƙofo kusa da Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku yace. "Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira." Kai ya gyaɗa mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al'farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips ɗinshi ke ɗan motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi. Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska Lamiɗo yace. "Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu." Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buɗe idonshi. Shi kuwa Galadima hannu ya miƙa ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai miƙar dashi tsaye. Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga Lamiɗo, in banda ƙarfin hali inashi ina iya ɗaga Jabeer. Muryar Lamiɗo yaji yana kuma cewa. "Jabeer DAN ALLAH KA TASHI". Tsaki ya ɗan ja kana ya yunƙura ya miƙa a hankali. Cikin jin daɗi Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron. A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu. Al'kyabbar shi ya ɗan gyara mahaɗinta. Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaɗa duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al'gaita kana da kaɗe-kaɗen. Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al'kyabbar shi. Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace. "Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raɗaɗin marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaɗi da kashedi na ba!". Ya ƙarishe mgnar da tafasar zuciya, cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa. "Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za'a dakaba". Ba'ana kuwa wani murmushi jin daɗi yayi sabida yasan yin duka da ƙatuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage ƙarfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba. (Allah sarki Ba'ana bai san zafin hannun Sheykh bane. Sarkin Shaɗi ne, ya miƙe tsaye tare da tanɗun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu. Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa. Yasa hannunshi ya zaro bulala ɗaya daga cikin bulalin ya miƙa mishi. Hannun yasa ya amshi bulalar. Kana ya gyara al'kyabbar jikinshi. Shi kuwa ba'ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buɗa sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya riƙe ƙugunshi, ya buɗa ƙwanjinshi da kyau. Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raɗaɗin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin. Busar sarewa da akayi azaban ƙarfi ne, tabbacin an bada dama a farane. Yasa Jabeer gyara riƙon da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi. Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani. Yasani in sha Allah daga kanshi baza'a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan ɓarakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai ƴan uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin ɗaya fushinsa na ranar ya dawo. Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaɗan, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana ɗagata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya ɗaura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba'ana ita a tsakiyar bayanshi. Gaba ɗaya hankali da idon kowa bisa fuskar ba'ana yake. Shi kuwa ba'ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar. Arɗo Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba'ana babu ƙaƙƙautawa. Shi kuwa Jabeer wani bulalan ya kuma shimfiɗa mishi a tsakiyar bayanshi tare da sunan Allah. Still murmushi yayi sai dai wani irin masifeffen bugawa da zuciyarsa tayi ya tsinke ras. A karo na uku ya tabka mishi bulalar a tsakiyan kafaɗunshi wannan karon baiyi murmushi ba, ƙebta idonsa yayi, tare da gyara tsayuwa sai kace dutse ake tabkawa bulalin. Fargabane ya fara dukan ƙirazan dattawan Fulani, yayinda ƙabilar ɓachama kuwa, suketa ihu da tsalle da fito da kiran ba'ana suna ƙara mishi ƙarsashi. Bulala ta biyar Jabeer ya kuma tsula mishi, still babu sauyi. Cikin sauri Arɗo Bani ya juyo ya kalli Lamiɗo dake zaune. Ko ajikinshi dashi da tawagarsa, Sarkin Shaɗi kuwa murmushi ma yakeyi. Cikin fargaba, Arɗo Bani yace. "Allah rene Lamiɗo wannan yaron bai iya duka da ƙarfi bane? Ko dai ba bulalin masarautarku bace!?". Wani irin kallo mai cike da mamaki da kuma tuhuma Lamiɗo yayi mishi. Sai kuma dai ya kauda kanshi. Ɗanzagi ne yace. "Hattara dai Arɗo , Masarauta Joɗa sun wuce aro, zuba ido kaga ikon Allah". Bulala ta bakwai ne, Jabeer ya ɗago ya tsulala mishi ita a gadon bayanshi. Da sauri Ba'ana ya rufe ƙwayar idanunshi sabida wani irin tashi da yaji tsikar jikinshi yayi. Tsikar jikinshi bai gama konciya ba, yakuma jin Jabeer ya rausa mushi wata bulaliyar, da sauri ya buɗe idonshi sabida. Wani irin Yar-yar da yaji tsikar jikinshi tana zubawa duk gashin jikinshi ya miƙe tsaye. Bai gama dawowa nazarin meyasa yakejin hakaba ya kuma jin wata bulaliyar. A hankali yaji zufa ya fara keto mishi duk ta inda hudan gashin jiki yake a fatarsa. Murmushi yakeyi har yanzu sabida bawai zafi yakeji ba, sai dai fargaba ta rufeshi, sabida jin alamun sihirurrukan jikinshine ke fecewa. A haka Jabeer yayi ta tsula mishi bulala har zuwa bulala ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185