Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

wuƙa ko bindiga basa shigarsa bare banzan abu shi bulalan Shaɗi shiyasa kullum shine da nasara a rayuwarsa". Shiru sukayi suna kallon ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance malamin da suke sawa yana bincikar musu jikin Ba'ana wato Chubaɗo yana cewa. "Akwai bulalin da zasu shigeshi su kuma karya duk wasu manyan sirrukan dake jikinshi, ta kuma sashi yayi kuka,cur-cur da hawayenshi, to amman bazasu taɓa samuwaba bamu da hanya ko damar samunsu, domin bulaline da a ƙalla sun shekara ɗari biyu a murde kuma suna cikin tsumin ma'jiya mai cikar tarihi da girma bulaline da tsawon shekara ɗari da ashirin da biyar kenan rabon da ayi amfani dasu, kuma an killacesu, killacewa mai tsauri, shi kanshi Ba'ana yana neman bulalin ruwa a jillo domin babban dodon tsafin Bonon ya sanar mishi saida bulalin zai samu nasarar da yake so, to amman bai san bulalin ina bane baisan a ina sukeba bai kuma san ta ina yake nemansuba an dai bashi yaƙini a hannun Fulani yake wannan dalilin ne yasa ya baza jakadunshi duk ƙasar da takeda Fulani." Da sauri Suka zuba mushi idanu baki ɗayansu cikin zaƙuwa sukace. "To Chuɓaɗo kai kasan inda bulalin suke e?". Kanshi ya jinjina musu tare dayin ƙasa da murya yace. "Eh na sani". Cikin sauri sukace. "Bulalin inane a wacce ƙasar suke?". Cikin tsoro yace. "Bazan fadaba bazaiyiwu in faɗaba". Magiya suka fara yi mishi amman fir yaƙi yace mutanen jikinshi sun hanashi faɗa, dole haka suka haƙura suka tashi daga taron ganin dare ya raba tsakiya kowa ya koma gidanshi. Washe gari da Asuban fari Rasuwar Chubaɗo ya zagaya garin Rugar Bani wanda akayi hira dashi lfy lau kawai washe gari aka riski ya rasu da alamun kuma ɗaure mishi wuya akayi ya rasu har lahira. Wannan rasuwa ya jijjiga zuƙatan dottawan nan huɗu da suka rage Arɗo Yabani da Bappa, da kuma Alhaji Ja'eh da kuma Malam Umaru. Sun shiga jimami mai yawa. A haka dai akayi mishi sutura aka binneshi akayi zaman makoki na tsawon kwana uku, randa akayi sadan uku duk hankali mutane huɗun nan ya ɗan konta ganin ba'a sake kashe wani ba a cikinsu. Yau tun da yamma Ba'ana ya matsa aka kira mishi Shatu wacce dolece tasa taje, inda yake har rugar shanunsu bata damuba sanin bai taɓa koda yunƙurin cewa zai taɓa koda ƴar yatsartace, Cikin sanyin jiki ta sallami aminiyarta Bintu ƴar gidan malam Umaru, sannan ta tafi bakin rugagen. Zaune ta sameshi cikin ƴar bukkarshi da yayi a cikin tsakiyar turken garken nasu, A hankali ta ƙaraso wurin ta sunkuya zata zauna ne a saman farin yashin dake wurin yayi maza yace. "Mata a ƙasa kuma? A a gskiya kada ki zauna a ƙasa. Ga buzuna zauna a kai". Kanta kawai ta jinjina shi kuwa shimfiɗa mata buzun yayi, a hankali ta zauna tana fuskantar cikin ƴar bukkar da yake zaune a cikinta ɗin. Shima gyara zama yayi tare da fuskantarta, Kwaryar dake gabanshi ta zubawa ido, shi kuwa. Cikin yin murmushi ya sa hannunshi yana gauraye magungunan dake ciki tare da cewa. "Matar dafaki nakeso inyi, irin dafar da muddin mutun ya tuna zai miki sihiri, misali ya miƙa hannu zai amshi mgnanin da zai samiki to zai kuturce in kuma baki ya buɗe zaiyi mgna kan a miki sihiri to zai kuramce". Cikin sanyi ta kwaɓe fuska tare da cewa. "To ni kuma wa zaimin sihiri a duniya wayama damu dani?". Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace. "In an nemi mijinki ba'a sameshiba dole kanki za'a dawo shiyasa nake shiryaki sabida kar Ni in an jefeni bai sameniba ya sauƙa kanki". Ya ƙarishe mgnar da miƙo mata ɗan ƙaramin korya yace. "Ingo ki fara shan wannan". Kai ta gyaɗa ganin madarar shanuce da aka tatsa da ɗuminta. Cikin takaicin halinsa tace. "Me wannan kuma?". dariya yayi tare da cewa. "Baki da yarda ki yarda dani wata rana zaki tuna nayi miki gata, wlh bazan taɓa cutar da keba mata, kisha madarace da zuma nasan kinaso". Cikin sanyi tace. "Sai dai in na koma gida zansha". Murmushi yayi tare da zuba mata ido kana a hankali yace. "Fulaku ko? Nasanku fulanin da kunya wato irin bazakici abu a gabana ba, to ai kafin ki koma gida zaiyi sanyi, bari in tafi can bayan bishiya in barki ke ɗaya kisha abunki da ɗuminshi". Ido kawai ta zuba mishi domin tabbas badon halin banza da Ya Ba'ana yake dashiba ya cancanci ta soshi tabbas tasan ko ba yayi mata alherin da bazata taɓa mancewa ba a rayuwarta. Ko komai nashi na duniya mara kyau ne to soyayyarta kekkyawace a zuciyarshi ya sota tun tana yar mitsitsiyarta kuma bai taɓa yunƙurin cutar da itaba ya kuma yi mata halacci. Murmushi yayi tare da cewa. "Mata nayi miki kyau ne?". Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh, cikin jin daɗi ya juya ya tafi, can nesa ya ɓuya, ita kuwa a hankali ta fara shan madarar nonon da yaji zuma mai daɗi, kasan cewar nonon ɗan kaɗanne a take ta shanye. Saida ta goge bakinta tace mishi. "Na shanye kazo". Da sauri ya fito ya dawo gareta cikin bukkar ya koma ya zauna wani nonon ya ɗibo ya miƙa mata amsa tayi cikin sanyi yace. "Me kika gani a ciki?". Murmushi ta ɗanyi tare da cewa. "Nono fari ƙal mana". Amsar ƙoryar yayi ya koma cikin bukkar dashi, jin kaɗan ya kuma fitowa ya miƙa mata tare da cewa. "Me kika gani?". Tura baki tayi tace. "Farin nono mana". Kanshi ya jinjina tare da cewa. "Da kyau, yanzu kiyi kamar zakisha ki gani". Ido ta zuba mishi tare da cewa. "Sha kuma?". Kai ya jijina mata kana yace. "Eh amman ba shan zakiyiba kiyi dai kamar zaki kaishi bakinki da niyar sha zakiga wani abu". Jim kaɗan tayi jin yana ce mata sha mana, yasa ta ɗan ɗago kwaryar ta nufi bakinda kamar zata sha. Wani irin wawan zabura tayi jiki na tsuma da karkarwa cikin tsananin firgita da tarin tsoro ta sake kwaryar....! By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 *GARKUWA* PAGE 8 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 Kada dai ku mance Free page ne, yana kuma gab da karewa. *Ga mai buƙatar saya ga number ta, 09097853276 turo ɗari uku ko dubunki ɗaya kacal domin samun damar karantawa cikin salama, Ga Ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin biya sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in ba halin turawa ta ac bisa dole turo katin mtn.* Ta saki kwaryar, a sorace, da sauri yasa tafin hannunshi, biyu ya tare kwaryar. Cikin tsoro jiki na rawa ta zazzaro idanunta woje kana murya a hargitse tace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun, Ya Ba'ana mekabani? Me ka shayar dani? Na shiga uku me kasa nasha?". Gaba ɗaya ta gigice tana rawan jiki da murya, ga hawaye kuma tuni suke shatata. Ganin yadda ta firgitane ya sashi matsowa gabanta cikin ɗaga murya yace. "Ba komai ba abinda na shayar dake Mata, wallahi Allah ki yarda dani wancan da kikasha babu komai a ciki". Da sauri taja da baya tare da cewa. "Ban yardaba me ka shayar dani?". Sai kuma ta fara kakarin amai da ƙarfi, ganin kamar aman bazai zo bane yasa ta tura

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185