Skip to content

Chapter 106

Chapter 106

Garkuwa Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

shima da kolliyar Golding color a jikinshi, ya ninkeshi kamar yadda muke ninke dankwali, bayan ya gama ne. Ya ɗaurashi a kanshi ya dai-dai-ta zamanshi kana, ya ɗauki baƙin abin wanda shima an zagayeshi da Golding color ya sakashi a akanshi, ya fito ras tamkar a Saudia. Allah ya sani yana masifar son wannan shigar da jin daɗinta a jikinshi babu takura babu matsi gashi ka suturtu da kyau mayu masu kallon tsiya irinsu Jazrahda Batool duk basa iya ganin komai a jikinshi ba. Da sauri ya nufi wurin aje takalma shi wanda yake na glass ne marfin ya buɗe kana, ya ɗauki wasu takalma irin nasu na sarauta Golding color ne kuma half cover ne, zura jajayen sawunshi yayi a ciki, kana ya koma gaban mirror, wani kolba turaren OudKareem mai masifar ƙamshi mai sanyi, ya fesa a duk sashin jikinsa. Kana yasa hannunshi ya ɗauki carbinshi. Farin galashi ɗan siriri ya manna a idonshi. Kana ya juyo da sauri zai fita, sai kuma ya tsaya cike da mamakin ganin. Haroon tsaye ya zuba mishi ido. Ya buɗi baki zaiyi faɗa sai kuma yayi shiru jin Haroon na cewa. "Kada kace zakayi faɗa Lamiɗo ne yace inzo in kiraka, lokaci na tafiya fa." Bai kulashi ba kawai yayi gaba, da sauri Haroon ya bishi tare da cewa. "Wannan baza ƙamshi haka sai kace wurin amarya zakaje, gsky kayi kyau sosai masha Allah". Bai kula Haroon ba sabida addu'o'in da yakeyi. Amman duk da haka saida ya bawa Haroon amsa a zuciyarshi, yake cewa. "Akwai wani wuri da yafi cancanta da ɗan adam yayi shiga ta tsabta da kyan shiga da ƙamshi sama da masallacin ne? Innal masajida lillafa, duk duniya da babu wurin da Allah ya keɓanta yace dakinshine sai masallatai. Nan zamu gana dashi. Domin idan mu bama ganinshi ai shi yana ganin mu". Murmushi Haroon yayi, dan Jabeer bai san mgnar da yakeyi a zuci ta fito filiba. A haka dai suka shiga Masallaci. Dole yau a gaggauce yayi Kudbar jumma'a dududu 15 minutes yayi yana kudbar kan halaccin mace ta kalli mijin da yakeson aurenta, kamar dai yadda yayi al-ƙawari a wancan satin. Daga nan aka kabbarta sallah. A can Rugar Bani kuwa. A hankali Shatu ta ɗago kanta ta kalli Ba'ana jin tunda suka tsaya baice mata komaiba, ganin yadda ya zuba mata idone yasata, saurin yin ƙasa da kanta, cikin sanyi muryar tace. "Ya Ba'ana zamu tafi rana tanayi fa!". Wani dogon numfashi ya ja ya sauƙe da ƙarfi, kana a hankali ya ƙara matsowa kusa da ita da sauri tayi baya cikin tsoro, hannunshi ya ɗaga mata alamun karta gudu, kai ta jujjuya tare da ƙara matsawa cikin rawan murya tace. "Ba kyau ina tsoro". Kanshi ya jingina da jikin bishiyar gamjin da suke ƙasanta, ido a rufe yace. "Da dai inada niyar cutar dake, da bamu kawo zuwa yau ban cutar dakeba Shatu, kadafa ki mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki kuma nake tare dake, dare da rana, kada ki mance kullum sai kinje gidanmu da dare da asuban fari kin amsowa Ummey mgninta, da har ina son cutar dake da tun wancan lokacin zan cutar dake. To amman bani da niyar cutarki, ina sonki ne sabida Allah, da kuma gsky da zuciya ɗaya, Shatu koda zaki ƙi yarda dani a kan komai dan Allah ki yarda dani cewa ina sonki, na kuma soki a baya zan soki har gaban abadan, wlh babu ƙarya a cikin soyayyarki a zuciyata, Shatu sonki shine babban raunina a duniya. Har yau babu wani abu dake firgitani da bani tsoro sai rasaki. Babu wani abu na duniya daya taɓa sani zubda hawaye sai soyayyarki, dan Allah ki dena zaton dan na matso kusa dake zan cutar dake, ki amince dani in baki abinda idonki zai buɗu da gane sihiri duk ƙanƙantarshi". A hankali take juya mishi kai cikin sanyi tace. "Na sani Ya Ba'ana wlh na yarda da kai akan soyayyata, na sani bazaka cutar daniba, tunda baka cutar dani a bayaba, nasan kana sona, na kuma yarda da son gsky kakemin, to amman ni bana son wadannan abubuwa asirce-asircen sabida haramun ne. A hankali ya zame jikinshi ya zauna kan jijiyan bishiyar. Ganin haka itama tayi sauri ta zauna bisa guiwowinta ta durƙushe a ƙasa. Cikin mamaki tace. "Dan Allah ya Ba'ana meyasa kwanan nan duka sai kayi ta zubda hawaye a gabana, hankalina yana tashi." Kanshi ya ɗan ɗaga ya kalli sama, a hankali yace. "Shatu ina sonki zan kuma soki har iya numfashin na, bazan bari wani abu ya rabani da keba, in kuma akasamu wani ya zama ƙaddarar rabani dake, to shi kuwa tabbas zan rabashi da rayuwarshi, kiyi haƙuri in dai a kanki ne zan iya yin komai, na kuwa san duk duniya babu wanda yasan hanyar da za'abi a kamani ko aci galaba a kaina, sai ke ranki ke ɗaya tak ce kikasan duk wani sirrina ban saniba ko zaki iya min halacci ki sirranta min rayuwata". Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa. "Ya Ba'ana ai rayuwa a hannun Allah take, wata ƙilma in rigaka mutuwa, kuma in dai nice in sha Allah bazan baiyana sirrinka dan a cutar da kaiba, ko ba komai kana soma kuma kace dan zaka nemo su ya Gaini ne kayi wannan tsarin gudun kada mugaye su cutar da kai, Ni na sani Ya Ba'ana waɗannan layun bazasu kareka ba, sabida ba hanyar Allah ka biba amman ni zanyi ta maka addu'a". Ido ya zuba mata a zahiri da baɗininta gsky ta faɗi dan yaga hakan cikin ƙwayar idanunta. A hankali ya jawo tandun duma dake rataye a kafaɗunshi, cikin sanyi yace. "Ga ruwa kisha". Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa. "Bana jin ƙishi". Tura mata tandun yayi gabanta tare da cewa. "Eh ba mgnin ƙishi bane, kishi dan kiji sanyi a zuciyarki naga kina kuka". Cikin share hawayenta tace. "Ba kai bane ka sani kukan kana ta barmin amanar sirrikanka bayan kuma shi amana rikeshi nada girma da nauyi da wuya". Murmushi yayi tare da cewa. "Zaiyi wuya ki riƙe kenan?". Da sauri tace. "In sha Allah zan riƙe". Kanshi ya gyaɗa tare da cewa. "Bazaki sha bako?". Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh. Kana ta miƙa tsaye, gaba ta ɗan yi kusa da Rafi'a, tace. "Rafi'a mu tafi". Murmushi yayi tare da cewa. "Rafi'a ku tsaya". Cikin tsoronshi Rafi'a tace. "To Ya Ba'ana". Da sauri ya ƙara so gabansu, tare da cewa. "Mata ɗago hannunki mu gani kinada zobene?". Kai ta girgiza alamar a a babu. kana ta ɗaga hannunta na dama, Yatsarshi ya karkaɗa mata tare da cewa. "Lalala ɗago hannun hagu mu gani". Cikin gajiya ta ɗago hannunta, fararen tausasan zara-zaran yatsunta suka zubawa ido gaba ɗayansu. Babu zobe ko ɗaya a yatsunta, Murmushi yayi kana yace. "To bari in baki zoben ziyara, koda bakya tare dani, duk lokacin da na nake kusa dake kawai zakiga zoben a yatsunki". Da sauri ta buɗe baki da nufin cewa a a. Kawai sai tayi shiru ganin wani irin zoben azurfa mai masifar ƙyalli da sheƙi sai ɗauke ido yakeyi. Ta juyo zata ce mishi a a Ya cire sai kuma tayi shiru ganin ya ɓace daga

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185