Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

kuma musulma.?" Dariya Abdallah yayi sannan yace. "Nikam naga abin burgewa sosai, ka dubi yadda tayi shiga cikin kamala ba kamar wasu matan dake irin aikinta ba, sannan maganar hotel da kaji tanayi ƙila wani aikim zai kaita can kasan su aikinsu babu inda bayakai mutum." Baki kawai ya taɓe batare da ya kuma magana ba.... *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.* *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍ Free Page Alhamdulillahi taro yayi kyau an watse lafiya bayan kyaututtuka da aka rarrabawa jami'ai tare da karrama wasu daga ciki inda Zarah ta kasance cikin waɗanda aka karrama. Saida ta ƙara kwana biyu cikin garin Abuja sakamakon jirginsu Jiddah dazai sauka ta garin bayan ya taso daga ƙasar Malasia. *_Jiddah ƙawace ga Zarah tun zamanin ƙuruciya, tare sukayi makarantar firamari da sakandire inda bayan sun kammala Jidda ta wuce jami'a yayinda itakuma Zarah ta wuce makarantar bada horo na ƴan sanda. Duk wasu sirrika na Zarah Jidda tasansu kamar yadda yake a ɓangaren Zarah itama._ _A shekarar data gabata ne Jiddah tayi aure inda mijin data aura ya kasance Barrister wanda yake aiki a ƙasar Malasia wato Bar. Saleem, dakyar aka rarrashi Jiddah tabi Saleem ƙasar a waccan lokacin bayan tayi iƙirarin ita bazata iya tafiya wata ƙasa batare da Zarah ba, shima dai Saleem ɗin bawai yana ƙaunar aiki a wata ƙasa bane illa dai kawai yanason ƙarasa yarjejeniyar aiki da sukayi da ƙasar. Tun bayan tafiyarsu kuma basuzo gida ba sai wannan karon da suka tattaro gabaɗaya suka dawo ƙasarsu ta gado._" Sallama tayi da ƙawarta ta tare da yimata godiya sannan ta wuce filin jirgi inda tanan zasubi wani jirgin zuwa Bauchi. Tana tsaye jirgin ya sauko daga sararin samaniya, bayan wadu mintuna kuma matafiya suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, sam bata kula ba sai ji tayi an rungumeta gam tamkar za'a tsaga ta. "Nayi kewarki sosai sahibaty.'' Jiddah wacce ita ke da alhakin rungumar ta faɗa cike da farin ciki, kana ta saketa tare da ƙamewa ta sara mata kana tace. "Na gaida ASP da kanta." Murmushi kawai tayi tare da maida hankalinta ga Saleem dake cewa. "Zan shigar dake ƙara fa Zarah, ganinki kawai yasa ta mance dani ma gabaɗaya." Dariya sukayi duka sannan suka nufi gurin da aka tana da domin zaman ma tafiya. Mintuna kaɗan jirgin dazai sadasu da garin Bauchi ya keta hazo. *England* Tsaki yaja a karo na ba adadi cike da takaici, tashinsa kenan daga bacci sannan kamar koda yaushe yau ma mafarkinta ya ƙarayi wanda ya haddasa wajabcin wanka ya hau kanshi. Ya rasa dalilin dayasa tun ranar daya ganta kullum dare sai yayi mafarkin yana wani abu da ita wanda hakan ke silar dole idan ya tashi sai yayi wankan tsarki. Wannan shine dalilin dayasa yake jin wata muguwar tsanarta a cikin ranshi. Miƙewa yayi tare da shiga banɗaki, bai jima sosai ba ya fito cikin shirinsa na farar riga da baƙin wando. Wayoyinshi ya ɗauka da niyar ficewa a ɗakin, saidai missed calls din Ammi daya gani a cikin wayar ne yasa shi dakatawa tare da zama a gefen gadonshi yana ƙoƙarin kiranta. Bugu biyu ta ɗauka tana mai sallama, amsawa yayi tare da gaisheta. "Har yanzu banga wani alert ba fa Jawwad." Ammi ta faɗa. Cikin son gane mai take nufi yace. "Ammi wani irin alert kuma na mene ne." "Zan saɓa maka fa, ka maidani sa'ar wasan kace. Ko ba dakai mukayi magana zaka turo kuɗi a fara haɗa lefen ba.?" Ta ƙarasa magana cikin hassala. Dafe kai yayi saboda tunawa da abinda take nufi, gaba ɗaya ya manta da batun aurenshi da Daddy yace zai haɗa da ƴar marigayi wacce bai ma santa a fuska. Shi a tunanin shi girman kai ne ya hanata zuwa ta gaidashi ko tabari su haɗu lokacin da yaje Nigeria, shiyasa yaji baya ƙaunar yin auren duk da matsalar da yake fama da ita na ƙarfin sha'awa. "Ayi haƙuri Ammi zan turo insha Allah." Ya faɗa cike da biyayya. "Toh ina jira kada ka sake na ƙara kiranka akan wannan batun idan ba haka ba kuma ranka ɓaci zaiyi." Ta faɗa gami da kashe wayar. Dafe kai yayi cikin damuwa, shifa yana da ra'ayin irin matar da yakeson aura, amma gashi yanzu Daddy ya ruguza mai duk wasu tsarin shi. Miƙewa yayi jiki babu laka ya fita domin yana a farkon sabuwar wata da za'a yakeson komawa gida gaba ɗaya, shi da ƙasar turawa kuma sai ziyara ko hutu ko kuma wani abu mai mahimmanci. ....................... A bakin gate su Zarah suka tarar da wasu mutane biyu da alama dai miji da mata ne sannan marasa ƙarfi. Ganin motar ne yasa su miƙewa daga durƙusun da suke a gefen gidan. Tsayar da motar Saleem yayi kamar yadda Zarah ta buƙata, buɗe ƙofar baya ta fito ta nufi inda suke tsaye. Da sassafar matar ta ƙaraso tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace. "Ranki ya daɗe ki taimake mu, kwana uku kenan muna zuwa gidan nan amma anƙi bamu damar shiga. Hatta ofishinku ma an hanamu ganinki dan Allah ranki ya daɗe ki sauraremu." Ɗagota Zarah tayi kana tace. "Kada ki bani kunya ta hanyar durƙusawa a gabana domin neman wata alfarma, hakan zai sa nayi tunanin ko baki ɗaukeni a matsayin ƴa ba. Ku tashi mu shiga daga ciki muyi magana a nutse." Ta ƙaramar ƙofa suka shige bayan su Saleem sun shige da motar tuni. Falon saukar baƙi ta kaisu kana taje kicin da kanta ta kawo musu ruwa da lemo. "Bismillah ga ruwa ku sha sai muyi maganar abinda ke tafe daku." Fadin Zarah bayan ta aje tiren dake dauke da gorar ruwa da lemu a kan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon. "Ranki ya daɗe ba zamu iya shan komai ba ahalin da muke ciki." Faɗin mijin "Meke faruwa ne.?" Zarah ta faɗa tana mai zama a kujerar dake fuskantarsu. "Ranki ya daɗe ƴar mu akayi wa fyaɗe, sannan mun tabbatar da wanda ya aikata laifin. Yaron wani ɗan majalisa ne dake maƙobtaka damu amma bayan mun sami mahaifin yaron da batun ya ƙaryata lamarin tare da faɗin zaiyi shari'a

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29