Chapter 20
Chapter 20
sukayi ne ta fahimci haka. Tabbas a da taso ta rangwanta mata kodan albarkacin Baaba, amma a yanzu batajin ko iyayenta dake kabari ne zasu dawo rayuwa suce ta haƙura da satar Diamond ɗin nan ba zataji maganarsu, dole ta sake shiri domin tasan ta wannan hanyar ne kaɗai zata iya cimma burinta na rayuwa da Alpha a matsayin masoyi. Miƙewa tayi tare da share hawayen da ya ɓata mata fuska ta nufi ƙofar fita daga ɗakin saboda jin kiranta da Baaba keyi. "Gani Baaba". Ta faɗa bayan ta iso falon. "Yauwa Raliya kiramin direba na aikashi ya tahomin da Zara'u tunda naga batada da niyar dawowa." "A'a Baaba kinsan yanayin aikinsu fa, ki barta zata dawo yanzu idan yaje ma ba lallai su barshi ya ganta ba." "Shikenan amma tabbas zata gamu da fushina idan ta dawo, yanzu da ba ƴan gida bane ai kunyata mu zatayi kenan." "Ayi haƙuri Baaba, kina buƙatar wani abu ne." Raliyan ta faɗa tana mai sunkuyar dakai ƙasa. "A'a bakomai jeki kema ki huta kinyi aiki sosai." "Nagode" ta faɗa tare da nufar ɗakinta. ✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️ *SINGAPORE* Daddy ne zaune da wani kyakkyawan matashin saurayi a wanj keɓaɓɓen lambu mai cike da shukoki kaloli daban-daban, kallo ɗaya zaka yiwa saurayin kaga tsantsar kama da sukeyi da Zarah da kuma Rahama saidai ƙarin hasken fata da Zarah tafiso duka, hannun Daddyn na akan kafaɗar saurayin da idanuwanshi sukayi jazir saboda kukan daya sha, hankacif ya saka tare da ƙara goge mishi idanunshi yana faɗin. "Kayi haƙuri Son muma har yanzu haka mukeji a zuƙatan mu bayyanawa ne kawai bama yi, amma kayi hakuri ka biyoni mu koma gida." cewar Daddy "Daddy bazan iya zama a Nigeria ba alhalin babu waɗanda zan iya gani na samu farin ciki." "Kada kace haka As-Siddiq zaman ka anan bashine zai iya dawo da waɗanda suka rasu ba, idan kace baka da kowa toh mufa ko baka ɗaukemu a matsayin iyaye bane dama, ƴan uwanka mata fa, bawai ina nufin bazan iya riƙesu bane tamkar ƴaƴan da na haifa amma suna buƙatarka a kusa dasu a matsayinka na wanda zasu dinga gani tamkar ɗan'uwana da ya rasu, kaine kaɗai zaka iya rarrashinsu musamman Zarah da ita bata kukan fili saina zuciya wanda yafi ƙuna, kayi haƙuri ka shirya mukoma gida tare dan Allah ina neman wannan alfarmar." "Daddy kai ubane a wajena baka da buƙatar neman alfarma a wajena, umarni kawai zaka bani na aiwatar, insha Allahu zuwa ƙarshen shekara zan tattaro na dawo gida." "Me zaka tsayayi anan har ƙarshen shekara? Bayan haka ma bikin ƴan uwanka za'ayi nan da wata ɗaya da sati biyu ka shirya kawai mu tafi tare." Idanunshi da suka fara washewa ya waro wanda hakan yayi mishi kyau matuƙa, kafin yace. "Wasu ƴan uwan nawa kuma Daddy." "Ehh ƴan uwanka Zarah da Jawwad, insha Allah nan da wani lokaci za'a ɗaura aurensu." "Amma ita Zarah ce ta amince da auren Bro Jawwad ɗin? Ko dama suna soyayya ne ban taɓa sani.? Amma yarinyar nan batada hankali duk ana maganar nan shine bata taɓa faɗamin ba ɗazu ma fa munyi waya da ita amma take cemin babu komai, yanzu ina ita ina miskilancin M.J mut..." lura da yayi da wanda suke maganar ne ya sashi yin shiru batare da ya gama maganar ba tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cike da kunyar maganganun daya yiwa Daddyn. "Kada kaji kunyata Son, ko nine a matsayinka tambayar da zanyi kenan yanzu tamkar uba kake a garesu kanada damar yin bincike a duk wani lamari daya shafesu." "Kayi haƙuri Daddy, zan shirya mu wuce tare." "Toh nagode Son, Allah yayi albarka". "Ameen" yace kana ya tsiyayi ruwan dake ajiye akan teburin wajen yasha, nan suka zauna suna hira kafin daga bisani suka miƙe tare da barin wajen. 👩✈️👩✈️👩✈️👩✈️👩✈️👩✈️👩✈️👩✈️ Saida ta kammala duk wasu mahimman abubuwa da duka dace game da case ɗin kafin ta nufi gida cikin hanzari saboda jiran da ake mata . Da sallama ta shiga falon, ganin Baaba a zaune ta sha kunu ne yasata faɗin "Dan Allah ayimin afuwa Baabata aikine mai matuƙar mahimmanci ya tsayar dani." "Zaki wuce kije ki samesu ko yaya." "Haba ko wanka bazaki bari nayi ba, da kayan aikin zanje ne wai" "Wallahi idan baki wuce ba zan saɓa miki, yo menene ai gwara suka ganki da kayan aikin su san ba ƙarya na musu ba, ki wuce kafin raina ya ɓaci" Babu yadda ta iya haka ta nufi ƙofar falon Abban saboda batason tayi abin da zai ɓata ran Baaba tunda yanzu ita kaɗai ta rage musu. Abbdallah na kishingiɗe a doguwar kujera yayinda M.J ke zaune yana danna waya, sallamar da akayine tasa ya miƙe daga kwancen yana amsawa shikuwa M.J. ko ɗago kanshi baiyi. "Amaryar..." maganar Abdallah ce ta katse lokacin daya kalli Zarah lokaci ɗaya kuma ya waro ido, kallonta ya ƙarayi sosai tana sanye da abaya amma hakan bazai hana mutum ganin kayan Ƴan sanda dake jikinta, dariyarshi ya ƙunshe tare da amsa gaisuwar da take mishi. "Amaryarmu kin shanya mu har mun bushe." "Ayi haƙuri dan Allah aiki ne ya tsayar dani shiyasa ." ta faɗa tana zama a kujera. "Toh gaki ga angon dai domin yayi fushi kinga ko kallonki yaƙi." Kallon shi tayi kana tace "Barka da zuwa ayimin hakuri na barku kuna ta jira." Kusan second goma dayin maganar kafin ya ɗago da nufin kallonta, ido ya waro sosai domin tabbatar da abinda ya gani, miƙewa yayi tare da nufu inda take zaune yana tafa hannayenshi......✍️ _Tammat Bi hamdulillah! Nan na kawo ƙarshen free pages, ga maison cigaba da karantawa sai a tuntuɓeni. Nagode sosai da addu'o'in ku da soyayyarku a gareni, sakallahu khairan._ *By* *Jasmine*🌸🌸 07048961623 *ASP ZARAH* Tsayuwa yayi a gabanta na wasu sakonni kafin ya durƙusa a gabanta yace. "Naji mamaki matuƙa sannan nayi farin ciki da wannan zaɓin na mahaifina, a ɓangare guda kuma ina takaicin haɗani aure da karuwa da za'ayi, sannan mace mai fuska biyu. Albishir da shawara zan miki a yanzu.." Maganar shi ta katse saboda dafashi da Abdallah yayi yana cewa "Haba M.J wane irin magana kakeyi ne haka.?" "Kayimin shiru Abdallah bana buƙatar jin komai daga gareka, ka zuba ido kawai." Baice komai ba ya kuma ya zauna cike da takaicin abinda M.J din yakeyi. Sunkuyawa ya kuma yi tare da dafa kujerar ta take kai da hannunshi biyu ta yadda suna iya jiyo numfashin juna. "Ina baki shawarar ki shirya tarban kowani ƙalubale da zaki fuskanta a zaman da zakiyi a cikin gidana domin zai kasance tamkar maƙabartarki domin zakiso ki tsince kanki cikin kabarinki fiye da gidana, sannan ina miki albishir cewa bazan dakatar dake daga aikin naki ba wanda kike rufarufa dashi kina aikata saɓon Allah amma ki sani bazan lamunta ba ace kina aurena kina yawon karuwanci. Banza, ballagaza, karuwa kawai mazinaciya." Ba iya Zarah ba hatta Abdallah saida yaji zafin kalaman M.J akan Zarah, sunkuyar da kanshi yayi cike da jin kunyarta amma uban gayyar ko a jikinshi illa ma zama da yayi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da tsiyaya ruwa a kofi yana sha. Tun bayan rasuwar iyayenta bata sake tsintar kanta cikin baƙin ciki da ɓaci rai irin na yau ba, zuciyarta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29