Chapter 7
Chapter 7
tare da bada umarnin lallai akai miki saboda abune mai mahimmanci. Dama yau nakeson kawo miki idan na tashi a aiki sai kuma gaki kinzo." Kaɗa kai Zarah tayi kafin tace" Sau sa dama Bala ina gayamaka ka koyi saka maganganu a cikin kalma ɗaya, basai kayita dogon sharhi ba a matsayinka na ɗan sanda. Anaso maganar jami'i ta banbanta dana sauran mutane, anfiso idan kayi magana sai mutane sunyi nazari sosai kafin su gane ainahin abinda kake nufi ba kamar yadda kake magana yanzu ba." Ƙamewa ya kuma yi kafin yace. "Ayimin afuwa ranki ya daɗe zan gyara." Bata kula da maganarshi ba tace. "Me takardar ta ƙunsa." "Ranki ya daɗe bani da damar buɗewa saboda a kulle take cikin envelop." Hannu tasa ta karɓi takardar tare da buɗe envelop ɗin ta cirota. Mintuna biyu ta ɓata wajen nazartar abinda ke cikinta. Ɗagowa tayi daga kallon takardar tare da maida kallonta ga Sergent Bala sa'an nan tace. "Taron ƙarawa juna sani a harkar aiki ne ake umartana naje wanda za'a gudanar a garin Abuja. Cikin sati ɗaya za'a gama gudanar da taron wanda zai fara ranar alhamis, sannan kaida Jennifer ne zamu kasance tare." Bata jira mai zaice ba ta bashi umarnin tafiya. Jingina kanta tayi da jikin kujerar sannan ta lumshe idanuwa. Haka ta wuni a ofishin sam takasa taɓuka komai bayan kuma da shirin yin aiki ta fito saidai ta danganta hakan da saƙon kwamishina daya risketa. Cikin kwana ukun ta kammala duk wasu shirye shiryen ta na tafiyar. A gefe guda kuma su Ammi na shirye shiryen tarban Muhammad Jawwad da shima zai iso ƙasar ranar Alhamis wanda rabonshi da ita tun yana ɗan shekara 14. Jirgin ƙarfe tara Zarah zatabi zuwa garin Abuja yayinda jirginsu Muhammad Jawwad zai sauka ƙarfe takwas da rabi. "Daddy ina jin ku wuce kawai zanbj ta ofishin kwamishina kafin mu wuce." Zarah kenan ke faɗi bayan ta gama amsa wayar da Sergent Bala ya bugo mata. "Babu rabon zaku haɗu da ɗan'uwan naki kenan saboda shima kwanaki biyar zaiyi ya koma saboda inaso ya dawo ƙasarshi ya cigaba da aiki." cewar Daddy "Banji daɗin haka ba gaskiya amma tunda zai dawo ƙasar gabaɗaya zamu ga juna." "Shikenan Allah ya kiyaye hanya." "Ameen Daddy." Sauran iyayenata ma addu'ar sauka lafiya suka mata kafin ta shige motarta ta fice a gidan. Daddy, Momi da Ammi sune sukaje airport tarbar ɗan nasu domin Baaba batada damar fita saboda halin takaba da take ciki. Basu jima da isa ba jirgin ya sauka, dubawa suke domin ganin ta inda zai ɓullo amma basu ganshi ba. Wani kyakkyawan bature ne suka ga ya nufo inda suke tsaye, basu ankara ba suga ya rungume Daddy tare da faɗin" Nayi kewarka Daddyna." Salati Ammi ta shiga rafkawa tana faɗin. "Jawwad kaine haka.? Shikenan masu jajayen kunnuwa sun canja ka, ka koma jinsinsu." Dariya sukayi gabaɗaya sannan suka nufi gurin da motarsu take, ita kuwa Momi kunyar fulani da kawaicin ɗan fari ne ya hanata magana. Mota suka shiga tare da nufar gida. A ɓangaren Zarah kuwa koda kwamishina ya gama zayyana mata tsarin yadda taron zai kasance saita miƙe domin tafiya, har ta kama hannun ƙofar da nufin buɗewa ta fasa tare da waiwayowa ta kalli kwamishinan da hankalin shi ya koma kan takardun dake saman teburinsa tace. "Yallaɓai nace ba." Kallonta yayi batare da yace komai ba. Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kafin tace. "Yallaɓai idan ba damuwa ka faɗawa wanda ya baka umarnin wakiltani a matsayin wacce zata halarci wannan taron cewa _Babu ma'ajiyar CCTV a ofishin ASP Zarah sannan baya buƙatar na'ura mai ɗaukan sauti domin sanin abubuwan da nake gudanarwa a cikin ofishina._ Bata jira mai zaice ba ta buɗe ƙofar tare da ficewa a ofishin........ ✍🏼 *Jasmine*🌸🌸 *TALLA*! *TALLA*!! *TALLA* *Uwargida!!! Shin ko kinsan zaki iya magance matsalolin da suka daɗe suna ci miki tuwo a kwarya cikin gidan aurenki.???* *Uhmm riƙe sirri sai mai sirri, shin kinada labarin shahararriyar matar nan wacce ta shahara wajen ganin cewa mata basu wulaƙanta a gidan mazajensu ba.!? Wacce ta kware wajen gyara amarya har ma da uwargida.? Ita ɗin dai dake siyar da kayan gyara na musamman masu sauƙin kuɗi amma akwai aiki, mai kawo muku sirrika da dabarun gamsar da miji ta kowani fanni.*😍 *Kardai na cika uwar gida da surutu, nice dai HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA. A wannan karon nazo ne da zafafan darussa da zan gabatarwa mata tare da kayan gyara na musamman. Bari dai na lasa muku zuma a baki, kaɗan daga cikin darussan da zan gabatar a wannan karon:* *Sirrin TomTom* _Shidai tom tom da kika sani uwargida, matsalar ki ta wajen kasa gamsar da mai gida ta ƙarw idan kika riƙe wannan sirri._ *Zuba ki lashe* _Bazance komai ba a wannan fannin idan kinason sani to ki kasance tareda ni a cikin sati ukun dazan gabatar da darussa_. *Kayan gyara na musamman zai iso ki har garin da kike idan kinyi odarsu, domin sanin kalar su da amfaninsu to ki kasance dani cikin zazzafan darussa na sati uku da zan gabatar a Special Group na ASP ZARAH FANS.* *Kada ki bari ƙaramin kuɗi ya saki zama mara gata gidan mijinki.* *Ki tuntuɓi wannan number 07048961623 domin samun damar shiga ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, Inda ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA zan kasance daku.* *Kada ki bari ƴar uwarki ta baki labari*. *SAI KUNZO* Ya kasa koda motsa yatsa ne saboda kaɗuwa da yayi da zancenta, yanzu kam ya fara zargin ko Zarah tana da aljanu masu faɗa matan idan anyi maganarta. Kiran wayar sirri sukayi da Alpha lokacin da yake shaida mishi ya tura Zarah garin Abuja domin halarta taron ƙarin ilimi a fannin aiki, hatta da wayar da yayi amfani da ita tana killace a ɗakin barcinshi na gida. Duk tunanin dayayi bai samar mishi da amsar inda Zarah taji labarin za'a sanya CCTV a ofishinta ba, yanke shawara yayi na kiran Alpha domin shaida mishi abinda ya faru. Saida ya kira sau biyu kafin aka ɗaga kiran. Cike da jimami kwamishina ya karanto mishi abinda ya faru a ofishin nashi kusan mintuna goma da suka wuce. "Ya akayi tasan da batun CCTV.?" Alpha ya faɗa cike da masifa "Kayi haƙuri Alpha nima bansan ina ta samu labarin ba." Ya faɗa kai a sunkuye tamkar yana gabanshi. Shiru ya biyo baya na wani lokaci kafin Alpha yace. "Ku bar batun saka camera ɗin tukunnan zanji da lamarinta a garin Abujan." Ya kashe wayar batare da yayi magana ba. Ƙayataccen ɗaki ne wanda yaji kayan alatu masu matuƙar kyau da tsada, tsaruwar ɗakin kaɗai zaisa mutum yayi tunanin na wani hamshaƙin shugaban ƙasa ne amma idan aka ƙurewa fitilun dake kawowa da ɗaukewa idon za'a gane mamallakin ɗakin sakamakon sunan Alpha da suke rubutawa a kowani kawowa da suke yi. A tsakiyar ɗakin wani haɗaɗɗen gilashi ɗauke da kyawawan kifaye a saman shi cikin ruwa suna ta shawagi yayinda ƙasan gilashin ke ɗauke da wasu kyawawan halittun ruwa da bazan iya tantance sunayensu ba. Maganganun ke tashi a cikin falon saidai banga alamun ta inda nake jiyo maganar ba, muryar namiji ne ke maganar inda yake cewa. "A matsayin marainiya mai neman aiki domin tallafawa mahaifiyarki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29