Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

damu duk sanda muka nemi ɓata masa suna ko ɗan shi. Yanzu haka yarinyar na gadon asibiti ana neman kuɗin aiki sannan bamu da halin biya." Ya faɗa yana mai fashewa da kuka inda matar ke taya shi. Sosai zuciyarta ta tsinke da lamarin musamman da taga manyan mutanen da suka haifeta a shekaru suna zubar da hawaye. "Amma meyasa baku kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa ba.?" Zarah ta tambaya a raunane. "Tun faruwa lamarin muka kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa damu, saidai bayan sun gana da mahaifin yaron suka fatattake mu tare da faɗin sharri mukeson ƙullawa ɗan sa. Wannan dalilin yasa muka garzaya ofishinki bayan wani maƙocin ya bamu shawarar yin hakan, tun kwanaki uku da suka wuce muke zirya a ofishin an hana mu shiga shine mai gadin wajen ya bamu adireshin ki." Matar ke wannan bayanin. Kai kawai ta jinjina tare faɗin. "Ina zuwa." kana ta miƙe ta fita. Bata daɗe ba ta shigo tare da Saleem da Jidda, zama sukayi tare da gaisa. "Wannan shine Bar. Saleem tare da matarsa Dr. Jidda, za muje asibitin tare domin ganin halin da yarinyar take ciki kafin shigar da ƙara a kotu." faɗin Zarah bayan tayi nuni da kujerar da Saleem ke zaune shida Jidda. Godiya su kayi sosai kana suka miƙe gaba ɗaya suka nufi waje. Motar Zarah suka shiga duka inda Saleem ke tuƙin. Mintuna kaɗan suka iso asibitin, kasancewar Zarah ƴar sanda shiyasa basu wani sha wuya ba wajen isa ɗakin da yarinyar take. Ita kaɗai ke kwance a gadon jikinta rufe da zani yayinda acan kusurwar dakin wata ke zaune kan dadduma da alama dai itace mai jinyar. Bayan sun mata ya jiki ne suka zazzauna inda Saleem ya ciro ƙaramar sound recorder tare da jan kujera ya ƙarasa bakin gadon yace. "Baiwar Allah da farko dai ina ƙara jajanta miki akan wannan lamari da ya afku dake sannan inason sanin ko ke wacece.?" "Da farko dai ni suna na Fahima ina zaune ne tare da iyayena a anguwar bakin kura dake nan jihar Bauchi. Sannan mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne." magana take a hankali alamum dai tana jin jiki. "Meya jawo afkuwar wannan lamarin a gareki." "Ina aikine a gidan wani ɗn majalisa dake nan anguwar mu wato Alhaji Nura Mai Riga. Tun lokacin da nafara aiki a gidan ɗan sa Kabeer ke yawan shigemin tare da nuna alamun yanaso muyi sabo sosai saidai ban bada damar hakan ba. To a ranar larabar data gabata ne bayan na kai masa abincinsa na rana kamar yadda na saba kowani lokaci bayan na gama girki ina kai masa nashi bangarensa. Bayan na ajiye abincin ne ya miƙomin kofin dake hannunshi wanda ke ɗauke da lemu ya umarceni da na shanye, naso nayi jayayya saidai yace idan ban sha ba bazai barni na tafi ba shiyasa na karɓa na shanye tare da miƙewa da nufin tafiya sai ya kuma cewa na share mai falon shi yayi ƙura. Tunda nafara sharar nakejin bacci na fizgata kafin nagama kuma bansan inda kaina yake ba sai farkawa nayj na ganni akan gadonshi ya ketamin haddi..." Ta ƙarasa faɗa tana mai fashewa da wani marayan kuka wanda ke nuni da ciwon abin da takeji. Kashe recorder ɗin Saleem yayi kana ya miƙe ya fita yana musu alama da ido. Zarah da Jidda ma miƙewa sukayi kana Zarah tace. "Insha Allahu za'a bi miki haƙƙinki sannan kafin mu tafi za'a sa hannu a shigar dake aikin da za'a miki na matsalar yoyon fitsari da kika samu." Godiya suka ƙara yi musu sosai. Sanna su Jiddan suka bar ɗakin. Saida suka biya kuɗin aikin da za'ayi wa Fahima sannan suka bar cikin asibitin. A hanyarsh da zuwa gida ne Jidda dake gaban motar ta waiwayo ta kalli Zarah data jingina kanta a jikin kujerar bayan motar tace. "Zarah kina ganin ba muyi ganganci ba wajen shiga cikin wannan case ɗin daya shafi Alhaji Nura Mai Riga.?" "Banason halinki na saurin karaya Jidda, kada ki manta Allah yana tare da msi mai gaskiya." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jinginawar da tayi jikin kujerar. "Waye ne Alhaji Nura Mai Riga.?" Saleem ya tambaya hankalinshi na kan hanya. *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ ... Jidda ce ta gyara zama tare da fara magana. "Wani sanannen ɗan siyasa a ciki da wajen Bauchi, anyi mishi shaidar rashin arziki da wulaƙanci gami da cin zarafin na ƙasa dashi, baya ragama kowa kasancewar yana da muƙami ga dukiya kuma daya tara, shiyasa yake taka kowa ya zauna lafiya daga shi har ɗan nashi. Ana faɗin cewa zai iyayin komai akan yaronshi ko da kuwa kisa ne. Shiyasa nake tsoron kar wani abu ya haɗa su da Zarah saboda baza'a haifar da ɗa mai ido ba." Kai Saleem ya girgiza kana yace. "Gaki a haka kamar Jaruma amma zuciyarki fal take da tsoro, ni a gani na wannan ba wani abu bane da za'a tsorata har ayi shakkun yin shari'a dashi. Insha Allah zamu zauna anan har sai munga an kwatar ma yarinyar nan hakkinta. Kuma ni zan zame mata lauya." "A zahiri bakai bane zaka zame mata lauyan amma a baɗini kai ne." Zarah ta faɗa idonta a lumshe kamar ba ita tayi maganar ba. Ɗan juyuwa Saleen yayi yana son fahimtar abinda take nufi. "Wani lauyan zamu nema yanzu a matsayin wanda zai kareta, saboda zai iya siye duk wani lauya da zamu ɗauka da kuɗi. Bayan mun gama yarda muna da lauya sai ranar da za'a shiga kotu mu rasa mafita. Shiyasa a yanzu dole mu ɗau wani lauyan na ganin ido, amma a baɗini zamu cigaba da gudanar da bincike tare da haɗa shaidun da zamu gabatar a kotu." Cewar Zarah Sosai suka ƙara mamakin fasahar ta wajen yin tunani abinda masu laifi zasu aikata. "Sam banyi tunanin haka ba da farko, kuma tabbas nasan Alhaji Mai Riga zai aikata haka." Faɗin Jidda tana mai haɗe hannayenta alamun jinjina ga Jidda. Haka suka cigaba da tafiya suna hira jefi-jefi har suka ƙaraso gidan. Ɗakinta ta wuce kai tsaye tare da shigewa banɗaki, wanka tayi sannan ta fito ɗaure da towel a jikinta. Zama tayi da nufin yin shafa amma ta kasa illa kwakwalwarta dake tariyo mata irin matsalolin da take dasu a gabanta, riƙe kanta tayi da hannu biyu bayan ta kifashi a jikin mirro ɗin. Saitin zuciyarta ta kuma dafewa da hannu ɗaya tanajin yadda take bugawa da sauri, tabbas tasan watarana matsalolin ƙasar nan zata haddasa mata bugawar zuciya saboda yadda ta ɗau matsalolin tamkar yadda take ɗaukan duk wani abu da ya shafeta ko danginta. Miƙewa take shirin yi ta nufin

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29