Chapter 5
Chapter 5
tunani na wannan matsala ce da zamu taro mu samu mafitar ta, matsala ce data shafi jaharmu da ƙasa baki ɗaya don haka muna buƙatar mu tattauna da sauran manyan jami'ai domin samun mafita.?" Kafin ya samu damar amsa mata wayarsa dake gefe tayi ƙara, hannu yasa ya ɗauku wayar tare da karawa a kunnenshi batare da yayi magana ba. "Zaka iya bata damar tafiya yanzu mun gama aikinmu sannan ka duba wayarka akwai saƙon kuɗi dana turama a asusun bankin ka." Abinda aka faɗa kenan daga ɗaya ɓangaren sannan aka kashe wayar batare da jiran amsar da kwamishinan zai bada ba. Kallon shi ya maida kan Zarah yace" ASP zaki iya tafiya. " Cike da mamaki ta miƙe tare da sara mishi sannan tafice a ofishin, jikinta taji ya mata wani iri ga zuciyarta dake bugawa da ƙarfi tamkar zata faso ƙirjinta. Shigarta cikin mota yayi daidai da katsewar kiran wayarta dake ringing kafin shigowarta, sai da ta zauna kafin ta sa hannu ta ɗauki wayar. Ido da zaro ganin anyi mata kira har 66, take ta duba domin ganin masu kiran, 35 missed calls daga Rahma, 6 missed calls daga Mustapha, 15 missed calls daga Daddy sai sauran kira 10 daga mutane daban daban. Da sauri ta shiga danna kiran Rahma saidai har ta gama ringing ba'a ɗaga, haka tayi ta kira ba'a ɗagawa kafin ya danna kiran Daddy sai dai wayarsa bata shiga. Ganin haka yasa ta canja akalar kiran ga wayar Mustapha. Bugu biyo ya ɗaga tare da faɗin" Zarah kina inane haka ake ta kiran wayarki bakya ɗagawa." "Na shiga ganawar sirri ne da kwamishina kuma wayar na cikin mota, meke faruwa ne.?" tafaɗa cike da zaƙuwar son jin abinda ke faruwa domin a lokacin bugawar da zuciyarta keyi ya ƙaru. "Babu komai ki taho gida anason ganinki." yafaɗa gami da kashe wayar baki ɗaya. Cikin sauri ta taɗa motar tare da harbawa kan titi bakinta ɗauke da kalmar hasbunallahu wa ni'imal wakil saboda yanayin da take jinta a ciki. Tun daga farkon shigowar anguwansu take ganin jerin motoci har zuwa gaban gidansu data tara cike da jama'a, nan zuciyarta ta ƙara tsinkewa gami da tabbatar mata lallai wani abu ya faru, horn ta danna a ƙofar gidan saidai a maimakon taga mai gadinsu sai taga Alhaji Sulaima na buɗe mata ƙofar. Bata ko gama parking ɗin motar ba ta fito da sauri, hannunta taji an riƙo hakan yasata tsaya wa daga tafiyar data fara tare da waigowa Daddy ta gani a tsaye. Kallo ɗaya ta mishi taga alamun kuka a fuskarshi. "Daddy meke faruwane dan Allah ka faɗamin." Batare da yayi magana ba yaja hannunta suka koma jikin motar, ƙofar baya ya buɗe mata tare da gyaɗa mata kai alamun ta shiga sannan shima ya shiga ya zauna. "Zarah." ya faɗa bayan ya zauna Cike da rauni ta amsa da" Na'am Daddy". "Nasan kinyi karatun islamiyya har zuwa matakin da kika sauke alqur'ani koh.?" Kai kawai ta iya gyaɗa mishi. "Inaso ki nutsu wasu tambayoyi zan miki." "Toh Daddy." "Inaso ki gayamin abinda Allah yace a cikin suratul Baqara a ƙarshen aya ta ɗari da hamsin da biyar zuwa aya ta ɗari da hamsin da shida(2:155-156) tare da ma'anar shi." Kai ta jinjina sanna tace" Allah maɗaukakin Sarki yana cewa و بشر الصبر ين(155) لَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوٓا۟ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيْهِ رَٰجِعُون(156) Fassarar shine "Kuma kayi bishara ga masu haƙuri(155) Waɗanda suka kasance idan wata masifa ta same su sai su ce _Lallai ne mu ga Allah muke, kuma lallai ne mu, zuwa gare Shi muke komawa._ A taƙaice ayar na nufin idan Allah ya jarabci bawa da wanu abu na baƙin ciki sai ya kasance mai yawan furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Murmushi yayi wanda iyakar shi fuska sannan yace" Masha Allah, to me Allah ya sake cewa a cikin suratul Ankabut aya ta hamsin dashi.?" Allah yace" كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ Fassarar ayar "Kowani rai mai ɗanɗanar mutuwane, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar daku."(Q29:57). "Alhamdulillahi tunda kin kasance mai ilimi, kinga kenan duk abinda yasamu bawa to ƙaddararre ne sannan da mutuwa da rayuwa duk na Allah koh.?". Daddy yafaɗa yana mai yimata kallo irin na tausayawa. "Ehh hakane Daddy." "Toh Zarah inaso ki kasance mai haƙuri tare da rungumar ƙaddarar data same mu duka, kiyi haƙuri ƴan fashi sun shigo gidannan sannan sunyi kisan kai kafin su tafi." A ruɗe ta kalli Daddy tanason gane inda maganarshi ta dosa. Tace" Ƴan fashi, kisan kai.? Wa suka kashe mana.?" Ganin tana shirin ficewa a hayyacinta ne yasa ya riƙo hannayenta biyu tare da faɗin" Ki nutsu Zarah sannan ki cigaba da faɗin kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Haka yayi ta maimaita mata har zuwa lokacin da ta ɗan nutsu kafin ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofar motar ta fito sannan yajata zuwa inda aka ajiye gawarwakin kafin a fita dasu a sallace su domin farfajiyar gidan bazata ɗauki mutanen da sukazo jana'izar ba. Dangin mamatan ne a gurin kowa yana karantu musu addu'a tare da kallon ƙarshe. Abinda ta hangone ya sata sulalewa a ƙasa batare da sun ƙarasa ba, da sauri Ammi data hango lokacin faɗowarta ta nufi inda butar Baba me gadi take ta ɗauko tare da watsa mata ruwan ciki a fuska. Shidai Daddy yana tsaye yakasa koda motsawa domin zuwa yanzu shima ya fara rasa jarumtar shi. Tsiyaya mata ruwan Ammi ta farayi ganin bata farfaɗo ba. Cikin sa'a kuwa taja numfashi mai ƙarfi. _Cigaban labari_. Zuwa ƙarfe bakwai na dare gidan ya ƙara cika sosai saboda ƴan uwa da abokan arziki na nesa da suka ƙaraso, domin hatta dangin Babansu Shahid dake Taraba duk sunzo kasancewar dayawa daga cikinsu jirgi suka bi. Haka akayi ta koke koke kafinan suka saurara aka cigaba da karɓan gaisuwa. A daren ranar dai babu wani daga cikin wannan ahalin daya samu damar runtsawa, kwana sukayi suna raya wannan dare da yiwa matattun addu'o'i tare da fatan Allah ya basu juriyar rashin da sukayi. Daddy ne ya hana a sanar da Sadiq dake ƙasar Singapore yana rubuta jarabawarshi ta ƙarshe na zama cikakken likitan zuciya wato *Cardiologist Consultant* sakamakon asarar shekaru da zaiyi inhar baici jarrabawar. Muhammad Jawwad kuwa sai ranar da akayi sadakar uku Daddy ya sanar dashi, shima dai kuka yayi tayi saida Daddy ya rarrashe shi. Nan yace ma Daddyn zai nemi biza ya taho bayan yayi ƙorafin rashin faɗa mishi da ba'ayi da wuri ba. Bayan kwanaki ukun ne baƙi suka rago a gida amma kullum wuni suke karɓar gaisuwa daga mutane daban daban, masu kwana ne dai babu. A cikin kwana ukun nan duk wanda yaga halin da suke ciki saiya kuka, Baaba kawai mai ƙarfin hali a cikin su. Ga Rahma da har yanzu bata farfaɗo ba. Gabaɗaya suna zaune a falo a daren ranar ukun harda Daddy da Mustapha da shima kullum baya rabo da gidan. Zarah na kwance saman dogowar kujera yayinda tayi filo da ƙafar Baaba. Lokaci ɗaya ta miƙe a firgice. Kallonta Daddy yayi tare da faɗin" Lafiya kuwa Zarah.?" "Daddy CCTV , na jona CCTV a duka falon dake gidan nan." Ta faɗa lokacin da ta miƙe sannan da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29