Chapter 22
Chapter 22
kai mai tsanani har taji bazata iya fita gurin aiki ba, tana kwance akan sallayar da tayi sallar asuba ta kasa miƙewa ta koma kan gadon. Ganin har ƙarfe takwas Zarah bata sauko ba yasa Baaba miƙewa da kanta ta haura saman domin duba lafiyarta, da sallama ta shigo saidai duhun dake ɗakin bai barta ta hangi komai ba, lalubawa tayi har Allah ya bata sa'ar samun switch ɗin ta kunna haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta farayi ganin bata ganta kan gadon ba har Allah yasa ta hangota acan kusurwar da take sallah. Da hanzari ta ƙarasa inda take tare da tattaɓa jikinta ganinta a duƙunƙune. "Subhanallahi Zara'u baki da lafiya shine baki faɗa ba tuntuni a kaiki asibiti, saiko zauna da ciwo a jikinki haba sai kace ƙaramar yarinya." Cike da juriya da ƙarfin hali tayi ƙoƙarin miƙewa zaune tare da jingina bayanta a jikin gado tace. "Ba wani abu ke damuna ba fa Baaba, kawai ɗan ciwon kai ne daya haddasa min zazzaɓi amma yanzu zanyi wanka nasha magani." "A'a Zara'u ban yarda da wannan ba ki lallaɓa kiyi wankan sai a rakaki asibiti, ko kuma zaki jira su Muhammadu suzo ne saisu kaiki naga kamar zaifi." "Baaba nace miki karki damu ba wani abu bane fa zansha PCM yanxu zai sauka." "Tunda haka kikace ai shikenan Allah ya baki lafiya, dama naga baki sauko bane nazo faɗamiki cewa ɗazu Babanku ya kirani wai sun fasa bari sai wani sati saboda Sadiku ya matsa sai sun dawo shine yau zasu biyo jirgin yamma su dawo." Wanj irin zabura tayi kamar ba mai jinya ba tace. "Da gaske Baaba.?" "Mtsww! Iskancin banza, ni ina nan na ɗaga hankali na baki da lafiya ashe ƙarya kike yi tunda har zaki iya wannan zaburar." "A'a fa Baaba, kinsan daɗewar da nayi banga ɗanuwana ba dole nayi ɗoki yanzu da naji zai dawo." "Shikenan ai kiyi wanka kizo ki karya saiki sha maganin." "Toh yanzu zan sauko." "Karma ki sauko yanzu inkin so." Ta faɗa tana mai ficewa daga ɗakin. Miƙewa tayi dakyar saboda sarawa da kanta keyi ta shige banɗaki, ruwa mai ɗumi ta tara ta shiga ciki, ta daɗe a kwance cikin ruwan kafin ta canja shi ta tare wani kana ta ɗauki sponge ta fara murzawa jikinta a hankali har ta gama ta ɗaureye jikinta kana ta fito a ruwan ta ɗaura towel tare da ficewa a banɗakin. Zama tayi gaban dressing mirro tana ƙarewa kanta kallo ganin yadda damuwar dare ɗaya ke neman ramar da ita, ya zama dole tayiwa kanta alƙawarin cire duk wani damuwa dake ranta akan wannan auren ta maida hankalinta wajen binciken inda zata nemo _Alpha_ domin zuwa yanzu tanajin wani irin kwarin gwiwa akan binciken da take a kanshi, tana iya gudanar da komai batare da tsoro ko shakkar wani abu zai faru da ita, hakan na ƙara bata tabbacin cewa lallai ta kusa tozarta Alpha a idon duniya. Abu ɗaya yanzu takeson sani shine haƙiƙanin inda yake rayuwa, zata iya riskar kowani haɗari matuƙar zata gano inda yake, hanya ɗaya gareta yanzu, hanya ɗaya tak! Wato Raliya. Ta hanyar Raliya ne kawai zata iya gano inda Alpha yake, dole tasan yadda zatayi ta samu duk wasu bayanai a gurin Raliyar. Tunanin damuwar Alpha da tayi ne ya mantar da ita badakalar auren dake gabanta, mayukanta ta shafa tare da wadata duk wata gaɓa na jikinta da turare, gaban wardrobe taje ta tsaya tare da kallon tulin kayanta dake ciki, idonta ne yakai kan kayan sports ɗinta dake can gefe a ninke, zaro su tayi tare da ƙura musu ido tana tuna lokacin baya da kowace ranar lahadi sai sunyi wasanni kala-kala da yayarta Rahama saboda haka ma Abba ya saka aka ƙawata musu wani sashi na cikin garden dinsu da kayan wasanni, wasu lokutan ma hatta Abban yakan kasance tare dasu domin shima yana matuƙar son wasan Table Tennis. Wasu marayun hawaye ne suka zubu daga idonta, hannu tasa ta share tare da yiwa iyayen nata addu'ar samun Rahamar ubangiji, kayan ta mayar ma'ajiyarsu kana ta ciro wata material kalar blue da golden, ɗinkin riga da skirt ne wanda ya matuƙar karɓan jikinta. Wayarta kawai ta ɗaukan sannan ta fice a ɗakin. "Ya jikin dai" Baaba ta tambaya bayan saukowarta cikin falon. "Da sauƙi." ta faɗa a hankali. "Allah ya ƙara afuwa, ga kalaci akan dinning idan kin gama saiki sha magani." "Toh" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dinning ɗin da Raliya ke gurin tana ƙara ƴan goge-goge, kujera ta jamata ta zauna tare da cewa. "Ina kwan Anty." "Lafiya" ta amsa a taƙaice kana ta kuma cewa. "Jeki kawai." ganin Raliyan na ƙoƙarin zuba mata abincin. Tea kawai tasha sha sai dankali da ta ɗan tsakura, sannan ta miƙe ta koma cikin falon ta kwanta a doguwar kujera, tana daga kwance take ƙarewa Raliya dake zirga-zirga kallo, tabbas akwai abinda take ɓoyewa domin tun zuwanta gidan bata taɓa ganinta babu hijabi ba kullum cikin saka hijabai take kowani irin aiki da takeyi ko yanayi da ake ciki. Toh mene ne Raliyan bataso a gani??? Ta tambayi kanta, shiru tayu na wasu mintuna kafin ta saki wani murmushi mai sauti wanda har saida ya jawo hankalin Raliyan dake moping, tabbas ta samu amsa. Lallai akwai tatto ɗin Alpha a wuyanta wanda batason a gani shiyasa ko da yaushe take cikin hijabai. Wayarta da tayi ringing ne ya katse mata tunanin da takeyi, da murmushi a fuskarta ta ɗaga tare da karawa a kunnenta. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Jidda ta faɗa daga ɗaya ɓangaren. "Dama nasan idan bake ba babu mai kirana da sanyin safiyar nan." "Saboda baki da aurene yasa kike ganin yanzu yayi safiya, toh yakike ya angon namu? Kun gana dai koh?" "Yanzu wace tambaya zan fara amsa miki maganaɗisu." "Duka nake buƙatar sani." "Alright to duka lafiya lau." "Hmm to ya angon kun sasanta dai koh." Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan yasa Jidda cewa. "Wato ɗan iskan maganganu yazo ya faɗa miki koh? Kuma shine kika zuba mishi ido batare da kin ɗau mataki ba, wai ke wace irin mace ce habibaty." Batayi mamakin jin abinda ya fito a bakin Jiddan ba domin idan da sabo ta saba da wannan halin nata, sau da dama ko bata faɗa mata abu Jidda na iya fahimtar hakan a yanayinta, da fari tayi tunanin ko Jidda nada aljanu akanta ne masu gayamata sai daga baya ta gano nature ɗinta ne hakan da kuma tsantsar ƙaunar da takeyi mata shiyasa take iya karantar ko wani yanayi nata, ƙwafa tayi kana tace. "Toh madam mai gani har hanji ya kikeso nayi idan ba shirun ba." "Wato abinda ya faru kenan dai, ke kuma saboda gaki mai biyayya kika zura ido kina kallonshi yana gasa miki maganganu, toh wallahi ki kiyayeni tun kafin nakai maƙura na shiga lamarin da bai shafeni ba." "Kiyi hakuri Mama" Zarah ta faɗa cike da zolaya. "Toh na haƙura ƴar nan, yanzu ya ake ciki wasu event zamu shirya ne naga alaman idan aka biyewa ra'ayinki bazamu gwangwaje." Dariya tayi sosai kana tace. "Kinsan nifa ustaziya ce." "Matar uztazu koh, shikenan ma bazan kuma yi miki magana ba zanjira
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29