Chapter 15
Chapter 15
kuwa Baaba tana zaune a falo tana kallon wa'azi a sunna TV, ɗaya daga cikin masu tsaron ne ya shigo tare da shaida mata cewa tana da baƙuwa, batare da dogon tunani ba tace ya shigo da ita. Jim kaɗan ya dawo tare da Raliya wacce ta ɓadda kama sosai tamkar ba ita ba, wasu tsofaffin kayane a jikinta wanda a kowani lokaci zasu iya yagewa sai wata ƙaramar Ghana-Must-Go itama ta tsofa sosai. Da sallama ta ƙarasa cikin falon sannan ta zauna ƙasa nesa da inda Baaba take. "Ki hau saman kujerar mana baiwar Allah." Inji Baaba. "A'a nan ma yayi Hajiya, ina wuni." Faɗin Raliya. "Lafiya lau sannu da zuwa, sai dai ban shaida fuskar taki ba kodai gurin Zara'u kika zo ne." "A'a Hajiya dama nazo neman aiki ne." "Wane irin aiki kuma daga ina kike.?" "Ni marainiya ce a garin Tilden Fulani nake, iyayena sun mutu ne sanadiyyar gobara da ta cinye gidan mu tun daga lokacin kuma na rasa masu taimakamin. Toh akwai wata Mata a can gurin namu da take shigowa birni tana aiki shine ta bani shawarar na shigo na zaga gidan masu hali na nemi aikin yi saboda nasamu abinda zan dinga rufawa kaina asiri dashi." "Duniya ta lalace mutane basason taimako, ai shi maraya idan ka taimaka mi shi tamkar ka zuba adashe ne da zaka kwashe ranar lahira. Kada ki damu insha Allahu za'a baki aiki koda na goge-goge ne." "Nagode Hajiya Allah ya saka da alkhairi." "Amin babu komai ai hakkin maraya ne mukeson saukewa."Inji Baaba. Sun ɗan jima suna taɓa hira kafin Baaba ta miƙe ta shige ɗaki bayan tabar Raliya a falo tana kallo, da sanɗa tabi bayan Baaba dan ganin mai zatayi a ɗakin, ganin shigewarta banɗaki ne yasa tayi saurin komawa falo tare da buɗe jakarta ta ciro wani abu kamar bead na kitson yara ta nufi saman bene. Bata sha wuyar gane ɗakin Zarah ba saboda taswirar gidan da ta haddace a kanta, ɗakin a buɗe yake dan haka tana shiga ta nufi gaban durowar kayan Zarah, wannan abun ta ajiye acan saman durowar ta yadda babu wani mahaluƙin dazai iya cewa akwai wani abu a gurin idan ba anfaɗa ba. Komawa falon tayi cikin sanɗa tamkar ɓeran dayayi sata yana tsoron a kamashi. A can kotu kuwa bayan mintuna talatin sun cika aka koma aka cigaba da fafatawa tsakanin ɓangarorin guda biyu, domin dai da alama shari'ar ta kwana ɗaya ce. Shiru ya ratsa cikin kotun bayan shuɗewar wasu mintuna, duk wannan abu dake faruwa Alhaji Mai Riga lokaci zuwa lokaci yake ɗagowa ya kalli ɓangaren da Zarah take yana yi mata murmushin ƙeta domin dai zuwa yanzu ya gama tabbatarwa kanshi cewa shi ɗin mai nasara ne sannan baza a yankewa ɗansa hukunci ba. Ita kuwa Zarah zancen zuci take a duk lokacin daya kalletan sai tace. "Shi dai mutum mara basira ko ina yake ana ganewa." Alƙali ne ya fara magana kamar haka. "Bayan sauraron shaidu da ɓangare biyu suka gabatar tare da hujjoji wanda suka gamsar da kotu da kuma kundin tsarin shari'a na ƙasa, kotu ta yankewa Kabeer hukuncin zama a gidan kaso na shekaru goma tare da aiki mai tsanani sa'an nan zai biya tarar miliyan biyar domin nemawa Fahima lafiya, Alhaji Nuhu Mai Riga kotu ta kama shi da laifin yunƙurin baiwa ɗan sanda cin hanci, dan haka kotu ta yanke mishi hukuncin zama gidan horo na wata biyar ko kuma tarar miliyan ɗaya." yana gama faɗin haka ya buga gudumarsa wanda ke nuna alamar ya gama aikin shi na wannan rana. Kotu fa ta rikice inda Alhaji Mai Riga keta zage-zage tamkar mai taɓin hankali ana riƙeshi, nan fa ƴan jam'iyun adawa da ƴan jaridu suka samu inda sukayi ta ɗaukan hotonan shi, wasu harda yi mashi video. Haka yana ji yana gani aka wuce da ɗanshi ɗaya tilo tamkar rai zuwa gidan kaso, take kuma ya zube a ƙasa tare da sakin kuka mai tsanani. "Jidda mu wuce gida kawai ki rabu da Saleem ɗinki da ƴan Jaridun nan." cewar Zarah bayan ta janyo hannu Jidda zuwa wani keɓeɓɓen waje a bayan kotun. "Mene ne haka wai Zarah ki barni mana a haskani a jarida tare da hubby na." "Mtssww mu wuce Jidda banason dogon zance, jikina na bani wani yanayi da ban gamsu dashi ba." ta faɗa tana tura Jiddan cikin motar ta, wuta ta baiwa motar bayan ta shiga itama, nan suka bar farfajiyar kotun zuwa gida...... ✍🏼 *By* *Jasmine*🌸 *ASP ZARAH*👩✈️ _Second to the last free pages._ _Paid book._ _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Ku tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *M*. *W*. *A*. Gudu takeyi tamkar zata tashi sama, yayinda Jidda ke mata ƙorafin karfa tayi sanadin tafiyarta lahira bata shirya. Ko kulata batayi ba har suka iso bakin gate ɗin gidan, horn tayi aka buɗe mata ta shigar da motar ciki, sai a lokacin ta samu nutsuwa amma duk da haka tanajin wani irin yanayi a tattare da ita. ''Haka kawai kin rabo ni da mijina, toh wallahi garin ma zamu bar miki tunda mun gama yin abinda ya tsaida mu." Inji Jidda. "Ba iya garin nake so ku bari ba, dan Allah ku bar ƙasar ma baki ɗaya." Zarah ta faɗa cike da tsokana lokacin da take fita a cikin motar. Da gudu Jidda ta bita suka nufi hanyar babban falo tamkar wasu ƙananan yara. "Allah ya shirye ku, wannan ai sai kusa nima na ruga da gudu, manya daku kuna wasan guje-guje, ke Hauwa idan ita bata rigada ta gama girma ba ai ke kam kin girma saiki daina biye mata." Faɗin Baaba wacce ke zaune a falo lokacin da suka shigo da gudu. "Kai Baaba kin manta wai nafi Jidda shekaru ne.?" Inji Zarah. "Yo idan kin fita shekaru ai yanzu kam ta fiki tunda a ɗakin mijinta take." "Saboda kawai tayi auren.?" "Ehh mana ai ko ƴar shekara 14 tayi aure yanzu dole za'a kirata da yayarki." "Faɗa mata dai Baaba ko zata daina raina ni." Jidda kenan ta faɗi. "Nima dai auren nan na kusa yinshi na huta." Ta faɗa tana zama a kujerar da Baaba take kai. "Ahh lallai da bamu yi shawarar aurar dake ba gaba bamu san abinda zaki dinga furtawa a gaban mu ba." Faɗin Baaba tana tafa hannayenta. Bata kulata ba saima plate ɗin dake gaban Baaban data janyo wanda ke ɗauke da lafiyayyen dambun shinkafa da yaji haɗi. "Baaba yau kin tuna da gargajiya ne haka, shiyasa kika kasa jira mu dawo muyi girkin." Zarah ta faɗa tana ɗebo dambun a cokali da nufin kaiwa baki. "Allah sarki bama nina dafa ba, baƙuwa mukayi shine nace ta shiga kicin ta girka mana gudun kada ku dawo a gajiye, kin ganshi nan yanzu aka gama shine na ɗebo naci." Harta buɗe baki da nufin cin dambun da ta ɗebo, amma jin abinda Baaba ta faɗa yasata dawo da cokalin tare da maidawa kan plate ɗin. "Wacce baƙuwa kuma.?" Ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29