Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

zakije gidan, sannan ki tabbatar bata cikin gidan yayinda zakije neman aikin saboda kaucewa matsala." Har zuwa wannan lokaci mai maganar bai bayyana ba illa wata matashiyar yarinya da tafito daga wata kusurwa a cikin falon, kyakkyawa ce daidai gwargwado sannan fatarta ta kasance kalar chocolate. Kallo ɗaya mutum zaiyi mata ta gane tana cikin damuwa sosai sakamakon idanunta da sukayi jazir saboda kukan da tasha. Ƙofar dazata sadata da farfajiyar gidan ta buɗe tare da fita a falon, babban fili ne sosai dake ɗauke da gine gine a wani gefe sannan shukoki kala daban daban da suka ƙawata wajen ciki harda manyan bishoyin kwakwa wanda su sukafi yawa a wajen. Sai ƙananun shukoki da aka tsarasu tamkar a ƙasar turai, a ƙasa kuwa wasu kyawawan duwatsu ne masu haske da sheƙi waɗanda ke ƙara bayyana kyawu da tsarin farfajiyar wannan gida da ya kasance tamkar na sarauta. Jefi-jefi mutane na shawagi a farfajiyar inda yawancinsu suka kasance mata sa'an masu ƙananun shekaru. Tafiya tayi sosai kafin ta iso wani keɓaɓɓen guri da ruwa ke gudana tsakanin waɗansu matsakaitan duwatsu, wasu mata ne ke zaune su uku suna ɓare kwakwa. Ta farko keyin hanya a jikin kwakwar, ta biyu kuma ke ƙarasa barewa yayinda ta ukun cikinsu ke ɗauraye jikin kwakwar bayan a ɓare tare da jerasu cikin wani kyawawan kwando. Zama matashiyar yarinyar tayi a gefe tare da jingina kanta a jikin wata ƙaramar bishiya. Gabaɗaya suka maida hankalinsu kanta, kafin wacce ke wanke kwakwar tace. "Meke faruwa ne Raliya, wani abinda ya miki ne.?" Ɗago kanta tayi tare da maida kallonta garesu tace. "Zanso ace wani abu ne ya shiga tsakanina dashi saidai babu abinda yamin illa aiki dazai turani a gidan da waƴannan lu'u lu'un suke." "Raliya wani lokacin kina saka mana shakku akanki, dukkan mu anan fata muke mubar cikin wannan azzalumin gida ke a lokacin ne keki fatan kasancewa da mai gidan ki dinga aikata haramtaccen abu dashi." Fadin ɗaya daga cikinsu bayan ta maida hankali kan ɓarar kwakwar da takeyi bayan jin furucin Raliyan. "A yanzu bana fatan barin wannan wajen saboda waƴanda nayi fatan ƙara kasance dasu basa duniyar zan fiso na cigaba da kasance anan saboda ko bana nan ɗin zaiyi wuya na tserewa *ALPHA* tunda na rigada nasan wasu sirrika nashi, bazai taɓa barina a raye ba tunani zaiyi asirin shi zan tona." Faɗin Raliya Ɗayar da tun fara maganar bata tofa ba tace. "Ki dinga yiwa kanki kyakkyawan fata Raliya idan ba haka ba zuciyarki zata iya rikeɗewa ta koma irin tasa na marasa imani." "Hauwa kenan ai yanzu haka banajin akwai abinda zuciya da gangar jikina zasu kasayi indai umarnin Alpha ne. Ku da iyayenku kawai ya rabaku ya kawoku nan amma nifa? Da hannayena guda biyu yasa na kashe iyayena, zuciyata ta gama bushewa tun a waccan ranar. Zan iya raba kowaye da jindaɗin sa kamar yadda akasa na raba kaina da nawa jindaɗin." Ta faɗa tana mai maida kanta ga kishingiɗar da tayi a jikin bishiyar. Babu wanda ya kuma tankawa a cikinsu domin dai sun saba da jin kwatankwacin wannan furuci a bakin Raliyan tin bayan da tasamu kusanci da Alpha lokacin da tayi nasarar ganin yatsun hannunshi, mutum ne shi mai matuƙar taka tsantsan kasancewar shi wanda jami'ai ke nema ido rufe shiyasa baya taɓa bada damar a ga wani sashi na jikinshi koda kuwa farce ne. Idan kuwa kayi nasarar ganin wani abu nashi to daga wannan lokaci zaka zama makusancin shi bayan an shiga dakai wani ɗaki mai taken _Kusanci da Alpha_, wata ɗaya cur ake kwashewa ga duk wanda ya samu nasarar shiga wannan ɗakin saidai mutum yakan fito ne a galabaice. Idan mai tsawon kwana ne zaiyi dogowar jinya, idan yazo da ƙarar kwana kuma saidai a wuce da mutum kabari. Babu wanda yasan abinda akeyiwa mutum a cikin wannan ɗakin domin hatta Raliya da aka shigar da ita tace bazata iya tuna komai da ya faru ba. Ko bayan mutum ya samu kusanci dashi bazai ƙara samun damar ganin wani sashi na jikinshi ba saidai zai kasance yana kasa saɓa umarnin Alpha ɗin koda kuwa umartarka yayi da kashe kanka. *Abuja* Cikin kwanciyar hankali da tsari ake gudanar da taron na ƙarawa juna sani a harkar aiki inda Zarah tayi zarra kwarai wajen baiyana dabaru da koma salon aiki da kowani jami'i ya kamata yayi amfani dasu, a cikin kwana huɗun da tayi a gari Abuja an samo nasarar zaƙolo manyan masu laifi da aka daɗe ana nema, hakan yasa aka shirya karramata a ranar ƙarshe da za'a kammala taron a matsayinta na jajirtacciyar ƴar Sanda da hukuma ke son irinta. Kasancewarta mace kuma kyakkyawa yasa manyan masu muƙami a rundunar Ƴan Sanda ke ƙoƙarin janta a jiki amma taƙi bada damar hakan, domin hatta ɗakin da aka kama mata a hotel ɗin da aka sauki baƙi irinta wanda sukazo daga wani gari taƙi karɓa. Gidan wata abokiyar karatunta na sakandire dake zaune da mijinta a cikin garin Abujan nan ta sauka. *Bauchi* A yau ne akayi addu'ar kwana bakwai na rayukan da aka rasa a farfajiyar gidan marigayi Alhaji Abdul_Jalal, inda akayi saukar alqur'ani mai girma tare da yiwa mamatan addu'o'i. Ƙarfe biyu jirginsu Ammi ya ɗaga zuwa Cairo ita da maigidanta da kuma Rahma da suka wuce da ita domin cigaba da duba lafiyar saboda har zuwa wannan lokacin bata magana tun bayan farfaɗowarta. Daddy da Momi ma bayan sallar la'asar suka ɗauki hanyar tafiya Bauchi. Sai gidan ya ragw daga Baaba sai Muhammad Jawwad da wata tsohuwa da Daddy ya samu domin tayasu zama sannan jami'an tsaron da Mustapha ys ɗauki nauyin ajiye musu guda biyar. Shima Muhammad Jawwad a washegarin ranar zai wuce Abuja ya ziyarci wani abokinshi dake aiki acan, sa'an nan daga can ya wuce ƙasar England domin haɗo takardunshi tare da takardar shaidar aiki da yakeyi acan saboda samun sauƙin cigaba da aikinshi a Nigeria. Washegarin kuwa shima ya wuce garin Abuja, kasancewar su Daddy basuyi mishi batun Zarah ba shiyasa baisan tana garin ba. Ƙarfe 12:30nr ya isa garin Abujan inda abokin nashi yazo ta taryeshi a airport ɗin, daga nan kai tsaye gidanshi suka nufa. Bayan yaci abinci ya huta ne ya buƙaci su fita domin zaga gari. Ta fito da nufin tafiya gurin da suke ƙaddamar da taron kiran wata abokiyar aikinta Toyin wacce suka haɗu wajen taron ya shigo wayarta inda ta buƙaci ta biyo ta hotel ɗin da take domin su wuce tare. Agogon hannunta ta kalla taga akwai sauran mintuna 45 kafin a fara taron hakan yasa ta yanke shawarar tsayawa a wani resturant da tagani domin siyan burger da ta tashi da marmarin ci a yau. Suna ƙoƙarin fitowa daga *Koise Delicies* ita kuma tana ƙoƙarin shiga waya kare a kunnenta, karo sukayi da Abdallah wanda ke gaba yayinda Muhammad Jawwad ke bayan shi. "Sannu dan Allah." shine abinda ta furta sannan ta cigaba da tafiya tana mai magana a waya inda takw cewa. "Jirani a reception na hotel ɗin bansan ɗakin ba." Dogon tsaki Muhammad Jawwad ya saki bayan sun shiga mota kafin yace. "Suna fakewa da aikin ƴan sanda suna abinda suka ga dama, yanzu menene abin burgewa ga mace a aikin ƴan sanda

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29