Chapter 21
Chapter 21
takeji tamkar xata tsago ƙirjinta ta faɗo, a yau tanaji duk wanda zai kirata da kalmar _Marainiya_ bazata ƙi amsawa ba, kamar ko da yaushe idan ranta ya ɓaci bata taɓa iya yin kuka na hawaye saidai na zuciya. Abdallah ne yayi ƙarfin halin magana ta hanyar faɗin "Dan Allah Zarah kiyi haƙu...." "Karka ƙarasa Abdallah mutane masu daraja ake baiwa haƙuri idan anyi musu ba daidai amma ba marasa tarbiyya irinta ba, tashu mu tafi." Bai kuma tankawa ba saboda tsananin ɓacin rai illa bayanshi da yabi bayan shi suka fice a falon. Tafi mintuna talatin a zaune ta kasa ko da motsawa, bakin ciki tamkar zai kashe ta, murmushin yake tayi ƙoƙarin yi saboda muryar Baaba da taji a bakin ƙofar falon. "Me kikeyi anan kuma Zara'u bayan sun tafi." cewar Baaba daga bakin ƙofar. Miƙewa tayi cikin fara'ar da ta aro tace "Tunanin masoyina nakeyi, inajin tamkar na kai kaina gidanshi mu cigaba da rayuwa." Kaucewa tayi daga dukan da Baaba ta kawo mata tana dariya. "Allahu ya shiryaki Zara'u, muje kici abinci nasan wunin yau duka bakisa komai a cikinki ba." Nan suka fice a falon tana ta ƙoƙarin biyewa zolayar Baaba cikin dauriya gudun kada ta fahimci wani abu, sai da ɗan tsakuri abincin kafin ta barta ta wuce ɗakinta. Gaban hoton iyayenta ta isa tare da ɗauka ta rungume a ƙirjinta, sai a wannan lokacin kukan yayi nasarar zuwa mata, batayi jayayya ba domin itama tanason yin kukan ko zai rage mata raɗaɗin da takeji a zuciyarta, nan ta shiga rera shi mai taɓa zuciya. Ƙarar da wayarta keyi ne yasa ta tsagaita da kukan tare da miƙa hannu ta ɗauki wayar , ganin mai kiran nata ne murmushin da batasan dashi ba ya kwace mata, da sallama a bakinta ta kara wayar a kunne, sai da ya amsa sallamar kafin ya fara jero mata tambayoyi. "Meyasa kika amince da auren Bro Jawwad.? Dama kuna soyayya? Meya hanaki sanar dani halin da ake ciki har kina shirin yin aure amma kin kasa sanar dani? Meke damunki ne?" "Duk wannan tambayoyin Bro wacce kakeso nafara amsa maka ne.?" Ta faɗa cikin marairaicewa "Duka nakeso ki amsamin, haba mana little wannan zurfin cikin naki yayi yawa." "Toh ya kakeso nayi Yaya, me kakeso nace maka." "Gaskiya nakeso ki faɗamin tsakaninki da Allah, kada ki ɓoyemin komai dan girman Allah baki da wanda ya fini a halin yanzu kinji." Cikin sanyin jiki ta amsa mishi da "Toh". "Kuna soyayya da M.J ne.'' Tambayar tazo mata wani irin amma ba yadda ta iya tunda tayi alƙawarin faɗar gaskiya duk da bataso wani yasan halin da take ciki. "A'a Yaya" Numfashi yaja mai ƙarfi kafin yace. "Ya akayi kuma kuke shirin yin aure?" Shiru tayi batare da tayi magana ba. "Ki amsamin banason nadawo nayi abinda bai kamata bane." "Dear zakazo ne." cikin ɗoki tayi tambayar. "Ehh" ya faɗa a takaice sannan ta cigaba da cewa. "Ki amsamin tambayata, kun haɗu da juna ne." "Ehh basu daɗe da tafiya ba ma yazo Bauchi" "Ya kukayi dashi." "Yaya..." "Shikenan tunda bakyason magana idan nazo zan nemi mafita da kaina ko da kuwa dakatar da auren ne.'' ''Haba Bro...." Bai jira ta ƙarasa ba ya kashe wayar gabaɗaya, zama tayi ta dafe kanta da hannuwa biyu, lallai ya kamata tasan yadda zatayi ta rarrashi ɗan uwan nata akan maganar auren nan duk da itama a yanzu tana dana sanin amincewa amma ƙaddara ta rigayi fata. 🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢 Babu wanda ke magana a cikinsu har suka isa masaukin nasu, sun daɗe a zaune kafin Abdallah yace "Yanzu M.J abinda kayi kana ganin ka kyauta kenan.?" "Mene abin rashin kyautawa anan." "Oh kai kana gani kayi daidai kenan, ya za'ayi kaje kana zagin baiwar Allah batare da ka tabbatar da abinda kake zargi ba, ina faɗa maka aikin ƴan sanda babu inda baya iya kai mutum daga inda ya dace har inda bai dace ba, amma kaje kana cin zarafin yarinyar nan, baya ga haka ma fa ƴar uwarka ce, why M.J?" "Idan ka gama saika faɗamin, look Abdallah wannan rayuwata ce and yarinyar nan ni zan zauna da ita ba wani ba, banason ka kuma yin magana akai babu ruwanka da lamarin dake tsakanina da yarinyar nan." "Kamar yadda kace zan fita a lamuranka da yarinyar nan amma inaso ka saka a ranka cewa ranar da zakazo kana neman alfarmata na shiga lamuran bazan shiga ba." "Bazan buƙace ka bama" yana gama faɗin haka ya shige bandaki, shikuwa Abdallah miƙewa yayi yaje reception da nufin binciken tun yaushe Zarah suka kama ɗakin, saidai hirar da wasu matasa sukeyi ta ɗauke mai hankali, nan ya zauna can gefe yana sauraron su, mata biyu ne da namiji ɗaya. Ɗaya daga cikin matan ne tace. "Wallahi bantaɓa jin ƴan sanda sun matuƙar burgeni kamar yau ba, kiga yadda yarinyar nan ta kama munafikin mutumin nan cikin sauƙin da babu wanda zaiyi tunanin." "Ai baku ga komai ba indai ASP Zarah ce, idan ta zaƙolo muku wani mai laifin sai mamaki ya kusa kar ku, wanda kake tunanin bazai taɓa aika wani mummunan laifi ba idan kaji laifin shi sai kayi ta mamakin yadda yake aikatasu." cewar saurayin. Hirar Zarah suka cigaba dayi wanda yawanci yabonta ne sukeyi tare da jinjina ma yanayin yadda take aiki da gaskiya da riƙon amana, gabansu Abdallah ya ƙarasa tare da baiwa saurayin hannu suka gaisa sannan yace.....✍️ *By* *Jasmine*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩✈️ "Dan Allah naji kuna magana akan wata ƴar sanda shine nace bari nazo naji gaskiyar batun." Dake saurayin irin masu surutun nan ne bai tsaya wani dogon nazari ba ya fara labarta mishi abinda ya faru awanni uku da suka wuce, na yadda Zarah ta jagoranci jami'i sukayi basaja suka kama mutumin da babu wanda zaiyi zaton mai laifi ne, ya daɗe yana zayyano mishi kyawawan halinta tun daga kan shiga har fannin aiki, ganin saurayin bashi sa niyar dakatawa ne yasa Abdallah miƙewa tare da ajiye musu rafar kuɗi akan teburin da suke zaune ya wuce sama. Murmushi yayi mai cike da ma'anoni, tabbas bazai gayawa M.J wani abu da ya sani akan Zarah ba, zai barshi har zuwa lokacin da zai gano da kanshi, a wannan lokacin zai taya Zarah ramuwar abinda ya mata amma duk da haka yana fatan ya saduda da wuri kafin dare yamai nisa. Ko da ya kuma ɗakin bai nuna mishi wata alama dazai gane yana cikin wani yanayi akan abinda ya faru ba, hirarsu suka cigaba dayi har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka fito masallacin dake farfajiyar hotel ɗin domin sauke farali. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Duk yadda taso taƙi saka abin a ranta ta kasa, kusan kwana tayi a zaune tana tunanin mafita babu shawarar da zuciyarta bata raya mata ba daga mai kyau har wanda bai dace ba, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar ɗaukar lamarin a duk yadda yazo mata, zata karɓi tayin kowane irin zama da yakeso suyi, damuwarta ɗaya ce kuma ya magance mata wato cigaba da aikinta, bata da wani sauran abinda zata damu dashi matuƙar zai yarje mata cigaba da aiki. Washe gari idonta yayi luhu-luhu saboda rashin baccin da bata samu ba ga kuma kuka da tayi sosai, hakan ya haddasa mata ciwon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29