Chapter 17
Chapter 17
hawayen kamar yadda take da tabbacin kuka Ammi keson farawa. Miƙewa tayi ta shiga toilet domin yin wanka, jim kaɗan ta fito ɗaure da ƙaramin towel. A gaban madubi ta tsaya, goge jikinta tayi kana ta murza lotion a jikinta sama-sama, hoda ta shafa a fuskarta kaɗan tare da goga lipbalm. Cikin sauri ta saka doguwar rigar atamfa tare da yana ƙaramin mayafi akanta, wayarta ta ɗauka tare da nufar falon. Baaba da Jidda ne ke zaune a kujera, yayinda Raliya take can gefe a rakuɓe. Zama tayi a kusa da kujerar da Jidda take kana tace. "Barka da yamma Baab." Kauda kai tayi daga kallo ta kamar ba da ita take magana ba. Murmushi mai sauti Zarah tayi sannan tace. "Har yanzu baki gama fushin bane Baaba ta." Jidda ce ta fashe da dariya ganin yadda Baaba take yatsina tamkar taga abin ƙazanta. "Ina ganin mu bar yin alkubus din nan sai gobe ko.? Ta faɗa tana ƙoƙarin maida dariyar dake taso mata, tana sane tayi maganar saboda tasan Baaba na matuƙar son alkubus. "Haba ƴaƴan albarka, kuyi mana shi da dare, na daɗe banci ba nima." cewar Baaba fuska a sake. Dariya sukayi gabaɗaya kana Zarah tace. "Sa.Jid ki kwaɓa mana a saka shi a rana kafin anjima." "Mene ne ma'anar wannan sojut ɗin da kike kiranta dashi." Inji Baaba. Dariya Zarah da Jidda keyi sosai har saida Jidda tabar kan kujerar ta dawo ƙasa, tsagaitawa da dariyar tayi tace. "Ke dai Baaba kowani suna saikin ɓata shi, Sa.Jid fa aka ce ba Sojut ba." "Mene ne ma'anar hakan.?" "Yauwa kinga Sa. farkon sunan Saleem ne sai Jid kuma farkon Jidda, shine aka haɗa kalmomin biyu ake faɗin Sa.Jid." Taɓe baki Baaba tayi tace. "Boko dai baiyi muku rana ba." Miƙewa sukayi su biyun suka nufi hanyar kitchen batare da sun kuma magana ba. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ Kiran wayar dake shigowa wayarsa ne akai akai ne yayi sanadin tashin shi daga daddaɗan baccin daya ɗauke shi tun bayan da yayi sallar asubahi, hannu ya miƙa tare da jawo wayar dake akan bedsite drawer, tsaki yayi mai sauti bayan yaga sunan wanda yake kiran nashi tare da kara wayar a kunne. "Dama nasan babu wanda zai dinga yimin irin wannan kiran idan ba kai ba, sarkin naci mai zan maka kake damuna." Daga ɗaya ɓangaren Abdallah ne yayi dariya kana yace. "Haba mana M. J kiran arziki na maka fa bana tsiya ba." "Naji faɗi dalilin kiran." "Yaushe zaka dawo Naija ne mu fara shirye shirye, kasan bamu da wani isasshen lokaci fa." "Shirye shiryen me kenan." "Banasan wulaƙanci fa M. J, kana nufin auren naka guda ba zamu gwangwaje ba.?" "Dalilin kiran naka kenan.?" "Ehh shi ne dalilin kiran najj yaushe zaka shigo." "Toh sai anjima, bana da lokacin tattauna magana mara amfani yanzu." "Zancen auren naka ne babu amfani." "Sai anjima please." ya faɗa yana mai katse kiran. Tsaki ya kuma yi a karo na ba adadi cike da takaicin wannan auren da za'a yi mishi, duk wasu tsari nashi an rusa mai, babu yadda ya iya dole yayiwa mahaifinsa biyayya amma tabbas yana da shiri sosai akan matar da aka ce za'a haɗa shi ta ita. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ Ƙishin ruwa ne ya damu Zarah wacce ke kwance akan tamfatsetsen gadonta, agogo ta kalla ƙarfe 2:15nd, a hankali ta saukk daga kan gadon tare da zura silifas a ƙafarta ta nufi ƙofar fita daga ɗakin zuwa kitchen domin ɗauko ruwan da yau ta manta bata shigo dashi ba yau, saboda yawan shan ruwan da takeyi duk sanda zata farka da dare. Gora biyu ta ɗauka bayan ta isa kitchen ɗin tare da apple ɗaya kana ta rufe ƙofar kitchen. Kamar ance ta waiwaya, haske ta hango a babban falon da Abbansu ke saukar baƙi lokacin da yake raye, cike da mamaki ta nufi hanyar falon domin dai ta tabba ta kashe wutan falon kafin su kwanta bacci. Abinda ta gani ne ya matuƙar bata mamaki tare da tabbatar mata da duk wani zarginta, Raliya ce....... ✍🏼 _Ku yimin uzuri please, ina shirin rubuta jarabawa ne shiyasa bana samun damar yin long pages. Ur prayers also needed._ By Jasmine *ASP ZARAH* _PAID BOOK_. _Domin samun damar cigaba da karantawa biya N300 kacal ko kuma N500 na VIP. Tuntuɓi 07048961623 domin biya a saka ki a group._ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *M*. *W*. *A* *Free page* ____Raliya ta gani riƙe da wani abu da take da tabbacin camera ne tana ƙoƙarin mannawa a gefen inda wani babban family photo ɗin su yake, take ta samu duk wasu amsoshin da take buƙata akanta domin tun kallon farko da tayi mata ta hango alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Rakuɓewa tayi a jikin window bayan ta hangota ta nufi ƙofar fita daga cikin falon, tana tsaye harta wuce ta shiga ɗakin da aka bata a matsayinta na ƴar aiki, shiga tayi cikin falon batare da ta kunna wutan da ta kashe ba ta nufi inda taga ta ajiye abun, kamar yadda tayi tsammani camera ce da zata iya ɗaukan duk wani shige da fice a falon sannan idan ba mutum ya sani ba babu wanda zaiyi tunanin akwai camera a gun. Ɗauka tayi tare da nufar ɗakin Raliyan, ta wani ɗan rami dake jikin ƙofar ta leƙa ga mamakinta sai ganinta tayi zaune akan katifar ɗakin da ƙaramar laptop a gaban wanda tana iya hangar abinda ke wakana a cikin laptop ɗin, ido ta waro gani hoton ɗakin ta ya bayyana a ciki tare da duk wani abu da ta gabatar tun daga dawowarta har zuwa yanzu. Kunnenta ta kara a jikin ƙofar ganin Raliya ta ɗauki wayarta ta kara a kunne. Batasan me aka faɗa ba daga ɗaya bangaren sai amsar da ta bayar. "A'a ranka ya daɗe, ina tunanin sun chanja tsarin gidan ne domin gabaɗaya an canja tiles ɗin da muka sani an saka wasu shiyasa bangane wanda zai kaini underground din ba." "Alpha." Zarah ta furta a hankali. Tabbas yanzu zarginta ya tabbata Alpha ne wanda ya turo Raliya tayi basaja a matsayin ƴar aiki, bayan sun tabbatar da bata gida a lokacin domin tabbas da tana gida baza a ɗauki Raliya aiki ba. Rufe na'urar taga tayi tare da kwanciya akan katifar, wani murmushi ne ya suɓuce mata bayan ta gama haɗa wasu abubuwa a cikin kwaƙwalwarta, hanyar ɗakinta ta nufa cikin sassarfa. Tsayawa tayi a tsakiyar dakin tana tunanin ta ina zata fara bincikar cameera din, wardrobe, haka taji tamkar anyi mata raɗa a kunne da sauri ta nufi wajen ta tsaya tare da karema wajen kallo sosai har lokacin da idonta ya hasko mata karamar camera acan saman wardrobe din, murmushi tayi tare da jawo stool ta hau sannan ta ciro camera ɗin. Jujjuyashi tayi a hannunta kafin ta ciro wani ƙaramin box ta saka a ciki, ruwan da ta ɗauko ta zauna tasha kana ta koma ta kwanta. Washegari bayan tayi sallar asubahi da kanta ta shiga kicin ta haɗa musu abin karyawa saboda tafiyar safe su Jidda zasuyi zuwa Bauchi, ƙarfe bakwai na safiya ta gama shirya komai a dinning kana ta nufi ɗakinta domin yin wanka kasancewar itama zata fita aiki. Cikin shirinta ta fito ta samesu a falo harda Baaba suna zaune, gaishe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29