Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

kwana nawa ne ma da duk zaku dawo Gomben." "Saboda ke gaki mai ƙafar yawo ko.?" "Hmm! Kin cika ni da surutun ku na ƴan sanda baki barni na faɗi dalilin kiran nawa ba." "Wato surutu ma na cika ki dashi ko.?" "Baza dai ki barni na faɗi abinda zan faɗa ba kenan.?" "Ohh sorry ina jinki." "Akwai matsala fa" "Wacce irin matsala kuma." "Jiya naje gidan Momi take gayamin wai a ɗaya part ɗin nan zaki zauna kafin a ƙarasa muku gyaran gidan da zaku zauna." "Yanzu ya za'ayi kenan." "Baki zaki buɗe ki gayawa Daddy kin fiso a gyara muku gidan tukun, idan babu hali ma sai a ɗaga bikin tunda kinga abu ne mahimmaci zamuyi." "Haka za'ayi zamuyi maganar." "Toh shikenan sai anjima ki gaishemin dasu idan sun sauka." "Ok bye." Motar ta kunna bayan ta ajiye wayar sannan ta nufi gida kai tsaye, M.J kaɗai ta tarar a falon bayan shigarta ciki da sallama, bata kulashi ba ta nufi hanyar kitchen, juyuwa tayi tare da aika mishi wani sihirtaccen kallon jin abinda yake faɗa. "Allah yasa dai kin wanke najasar tun a waje baki dawo dashi cikin tsarkakken gidan nan ba." Shigewa tayi batare da tace komai ba, shikuwa tsaki ya furzar mai sauti tare da miƙewa ya bar cikin falon. A zaune ta tadda Baaba a kitchen ɗin tana yankan ɗanyar kuɓewa, ledojin hannunta ta ajiye tare da faɗin "Me zakiyi da kuɓewa kuma Baaba.?" "Babanku ne yace yanaso a mishi shine nafara gyarawa kafin ki dawo, ina kikaje ne.?" "Kasuwa naje na siyo sauran abubuwan da bamu dashi a kitchen ɗin." "Gashi ki ƙarasa wannan bacci ne yaketa ƙoƙarin kamani tun ɗazu zanje na ɗan kwanta, saiki kira Raliya ta kama miki wasu aiyukan." "Toh" tace tare da karɓar rubar da kuɓewar ke ciki, ita kuma Baaba ta fice a kitchen ɗin, saida ta gyara komai tare da fitar da duk wani abu da zata buƙata kafin itama ta wuce ɗakinta tayi wanka da sallah kafin ta fara aikin. Tun ƙarfe biyu ta shiga kitchen ɗin tafara hada-hadar haɗa abincin tarbar baƙin nasu, ita kaɗai takeyin duk wasu aiyuka ba kamar yadda Baaba tace ta nemi taimakon Raliya ba, a dole ne kawai take haƙuri Raliy na kusantar inda take bawai dan tanaso ba, saboda tsanar da takeyiwa Alpha da duk wanda ya dangance shi. Kasancewarta mai saurin aiki yasa kafin la'asar harta gama haɗa komai illa kawai masa ɗin da bata soya ba wanda shima rashin tashin da baiyi ba ne ya hanata soyawa. Baaba ce ta kuma shigowa kitchen ɗin da sallama tana faɗin. "Yanzu Zara'u da nace ki kira Raliya ta kama miki wannan aikin shine kika ƙi koh.?" Sai a lokacin Zarah ta lura da Raliya dake bayan Baaba, kau da kai tayi tare da faɗin. "Naga aikin ba mai yawa bane shiyasa." "Allah ya kyauta wannan halin naki, saka min tuwon nikam idan kin gama." "Toh kije zan kawo miki." "Ban yarda ba sakamin na tafi dashi ko kibawa Raliya ta kawomin." Ba yadda ta iya haka ta saka mata malmalar tuwon guda biyu a plate sannan miya a ƙaramin glass bowl, a wani ƙaramin faranti ta jere mata tare da ɗora mata kwalbar soyayyen man shanu ta miƙawa Raliya farantin suka fice tare. Saida ta wanke abubuwan da tayi amfani dasu kafin ta nufi ɗaki saboda kiran sallar la'asar da akeyi, cikin sauri ta watsa ruwa ta fito bayan shigarta banɗakin sannan ta shimfiɗa darduma tare da tayar da sallah. Ko da ta idar gaban dressing mirro ta nufa domin shiryawa, saboda ƙarfe biyar jirginsu Daddyn zai sauka, simple makeup tayi wanda ya matuƙar yi mata kyau saboda yadda ta tsara shi, wardrobe ta kuma tare da zaro wasu rantsattsun riga da siket na wani dark blue ɗin less mai ratsin fari, cikin hanzari ta saka kayan ganin lokaci na ƙurewa, ba ƙaramin karɓar jikinta kayan sukayi ba musamman data yafa farin gyale mai duwatsu sanna ta saka farin takalmi, wayarta ta ɗauka ganin har ƙarfe 4:40pm yasa ta fita da sauri, bata tarar da Baaba a falo ba hakan yasa tabarwa Raliya dake ƙoƙarin shiga kitchen sallahun soya mata sinasir ɗin tare da faɗama Baaba cewar ta wuce airport. A farfajiyar gidan ta gansu suna ƙoƙarin shiga mota wanda tana da tabbacin suma airport ɗin suka nufa, inda motarta take itama ta nufa batare da ta kuma kallon inda suke ba. "Amaryarmu irin wannan kyau haka kamar wacce ke shirin zuwa gasar kyau na duniya gabaɗaya." cewar Abdallah daya leƙo da kanshi ta window yana magana. "Banda zuga dai." "Da gaske fa, kizo mu wuce tare mana ko ba airport ɗin kika nufa ba kema." "A'a kuje kawai yanzu zan biyo bayanku." "Sai tayi yawon dandin nata kafin nan, kaga bazata haɗa hanya damu mu hanata aikata kudurinta ba." cewar M.J yana taɓe baki kamar yaga wani abin kyama. Hawaye taji......✍️ *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ ...Hawaye taji masu zafi suna ƙoƙarin silalo mata, da sauri ta buɗe motar ta shige domin batason M.J ya gano lagonta. Ta rigasu isa airport ɗin dan haka ta samu guri tayi parking sannan ta fito da jingina da motar ta yadda waɗanda take jira zasu iya hangenta, batayi minti goma da tsayuwa ba jirgin ya fara ƙoƙarin sauka ƙasa daidai lokacin kuma motarsu Abdallah ta iso gurin inda sukayi parking a kusa da tata motar. Matafiya ne suka fara saukowa cikin takon isa na hamshaƙan da suka baro ƙasar turawa, ɗaya bayan ɗaya suka jero akan matattakalar da zata sauko dasu daga jirgin, ido ta baza sosai ta inda zata gano ɗan'uwan nata. Duk da yawan video call da sukeyi amma dakyar idanuwanta suka iya ganeshi saboda kyau daya ƙara, nufowa suke domin ƙarasowa inda suke tsaye ita da su Abdallah, saidai bazata iya jira su ƙaraso ba dan haka ne ta ruga a guje ta ƙarasa inda suke tare da rungume ɗan'uwan nata cikin tsantsar farin ciki, shima hannayensa biyu yasa ka ya maida mata rungumar tare da ɗan bubbuga bayanta jin tana shessheƙar kuka. "Bakyason ganina ne na koma inda na fito ko.?" ya tambaya cikin son yaga ta daina hawayen. Da sauri ta sakeshi tana saka bayan hannunta ta goge hawayen kana tace. "A'a dear murnar ganinka ce kawai ta saka hakan, idan kace zaka koma to nima binka zanyi mu koma tare." Daddy dake tsaye yana kallonsu ne yace. "Wato ni ko sannu fa zuwar ma bazan samu ba duk da ni naje na taho dashi, ai babu damuwa nikam naga warayya ƙarara a fili."Cikin zolaya ya ƙarasa maganar. Ɗan durƙusawa tayi da hanzari tana faɗin "Sorry Daddyna ai nafi kowa murnar son ganinka, barka da dawowa ayimin afuwa." "Babu komai daughter mu hanzarta mu wuce gida naga hadari ya haɗo." Hannushi ta riƙe kamar wata yarinya suka ƙarasa wajen motocin, cikin fara'a suma sukayi musu barka da dawowa, nan aka ɗanyi raha irin wacce ke tsakanin uba da ƴaƴansa kana suka fara ƙoƙarin shigar da kayansu mota domin shigewa gida, Zarah kam hannun Sadiq taja zuwa motarta ta buɗe mishi gidan gaba ya zauna sannan ta dawo domin ɗaukar wasu kayan ta saka a tata motar, daidai lokacin daya sunkuya domin ɗaukar wata jaka itama lokacin

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29