Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

da yawan kukan nan fa little, addu'a kawai zamu cigaba dayi musu, ko kinaso ki haifi yara a rasa gane wacece uwar idan kuna kuka dukanku." Hannayenta ta saka ta rufe fuska tana faɗin. "Kai Yaya." "Ehh mana, tashi muje kitchen mu haɗa dinner kafin Daddy ya dawo." "Ohh kasan na manta da Daddy na gidan nan, ina yaje ne." "Ya fita yun ɗazu zai haɗu da wani abokin kasuwancinsa." "Nagode wa Allah da bayanan wannan abu ya faru." "Muje kitchen ɗin." "Yaya akwai abinci fa." "Ni dai muje muyi ko ma mene ne, da kwaɗayi na dawo ƙasar." Hanyar kitchen ɗin suka nufa suna hira kamar wasu ƙawaye. ''Allah ya shirya ku." "Amin" Zarah ta faɗa daga kitchen ɗin...✍️ *Ayimin uzuri da wannan pls banjin daɗi ne, ayi haƙuri.*👏👏👏👏 *Jasmine*🌸🌸 *ASP ZARAH* _Duk abinda aka sama lokaci..._ Kamar yadda yau ta kasance saura kwanaki biyu kacal a ɗaura auran Zarah da angonta M.J, baƙi na nesa da na kusa duk sun hallara, inda Ammi da Momi suka dage wajen gyara Zarah sosai tamkar wacce zata auri shugaban ƙasa. Babu wasu events da akayi sai sports day da sukayi sai kuma walima da za'ayi bayan ɗaura aure. Suna zaune su uku a wani keɓaɓɓen guri a cikin garden ɗin gidan Daddy, Sadiq ne a tsakiya sai Zarah da Rahama da suke a gefensa kowaccensu ta ɗaura kanta a kafaɗarsa, kallo ɗaya zakayi musu duka ka tabbatar da cewa suna cikin damuwa sosai, idan ko mutum yasa da mutuwar mahaifansu toh tabbas za'ace maraici ne ke damunsu. Sadiq ne yayi gyaran murya yace. "Sis kinji abinda ke shirin faruwa da little fa kuma Baaba ta hana a dakatar da bikin nan, ni banaso taje tana shiga damuwa ne kinsanta da rauni." Rahama wacce tun bayan abinda ya faru ta zama miskila ta wucin gadi, shiru tayi na mintoci kafin tace. "Dakatar da auren bashi ne mafita ba Yaya, mu bari muga idan anyi auren yana cutar da ita sai mu nemi mafita." "Bakomai amma indai ya cutar da ita sai na bi mata haƙƙinta ko da kuwa igiyar zumuncin dake tsakanin mu zata tsinke." "Haka ma bazata faru ba." "Toh Allah yasa, little tashi kije Daddy na nemanki tun ɗazu mantawa nayi ban gaya miki ba." Cikin sanyin jiki Zarah ta miƙe tana faɗin "Ku jira ni fa yanzu zan dawo." "Mu ma yanzu zamu shigo gidan." "Toh sai kunzo". Kai tsaye falon Daddy ta nufa inda yake zaune shi kaɗai da alama ita yake jira, gaishe shi tayi sannan ta zauna a gefe, bansan me suka tattauna ba sai dai daga ƙarshe muryar Daddyn naji yana ta godiya tare da samata albarka. "Daddy ka daina bani kunya ta hanyar gode min, idan kana hakan sai naga kamar baka ɗauke ni a matsayin ƴarka bane." "Har abada zaki cigaba da kasancewa ƴata, amma kinsani cewa godiya wajibi ne ga wanda aka kyautatawa, Allah ya miki albarka ya baki zaman lafiya a ɗakin aurenki." "Amin Daddy." "Babu wani abu da kike buƙata ko." "Babu komai." "Tashi ki kuma cikin ƴan uwa da iyayenki." Cikin rashin kuzari ta miƙe tare da ficewa a falon, wata hanya ƙarama tabi sai gata ta ɓullo a wani babban falo wanda aka wadata da kayan alatu na more rayuwa tamkar ɗakin shugaban ƙasa, Jidda kaɗai ta gani a falon tana duba wasu takardu, zama tayi a gefenta tace. "Ya naga gidan yayi shiru haka." "Ehh duk suna backyard wajen gyaran naman nan, saboda Momi tace kar a barwa ƴan aiki aikin zasu lalata shi." "Ok nima daga falon Daddy nake." Kallonta Jidda tayi na wasu sakanni kafin tace "Ina fata komai ya zama steady." "Ehh babu wata matsala yanzu." "Wa kun haɗu da angon kuwa.?" "Uhmm tun ranar daya bar Bauchi ba mu ƙara haɗuwa ba, Abdallah ne ke jigilar zuwa da kuma kira." "Sai kinyi haƙuri da lamarin angon nan naki idan ba haka ba zai ɓata mana shirin mu." "Dole zan kula domin nima jikina yana bani cewa na kusa kama Alpha da hannuna." "Nima inajin hakan, ya batun Raliya kuwa." "Na saka an ɓoyeta a wani keɓaɓɓan guri sai ranar da burina ya cika zan fito da ita." "Hakan yayi kyau, ya kukayi da oganki ne da kikaje neman transfer." "Ohh Mr. C.P ai saida na tabbatar baya ƙasar kafin naje na processing komai, saidai kawai ya dawo yaji labarin nayi aure a wani gari na barsu da garinsu." Dariya Jidda tayi kafin tace "Kin manta waye CP kenan zai iya miki makircin nasa." Dariya dukayi duka tare da miƙewa suka fice a falon. 💫💫💫💫💫💫💫 A yau ne dai aka ɗaura auren Muhammad Jawwad Sulaiman da Fatimah Zarah AbdulJalal sai fatan samun zaman lafiya a tsakanin ma'auratan biyu duk da ba haka aka tsara ba. Duk da ba'a shirya shagula ba amma mutane sunzo sosai harda waɗanda ma ba'a gayyata ba duk sun nuna bajin ta, da yamma kuma akayi walimar mata a cikin gidan inda malamai sukayi wa'azi sosai wanda duk akan zamantakewar aure ne. An raba kyaututtuka sosai baƙi duk sun tafi suna farin ciki tare da fatan alkhairi. Nasiha sosai Momi da Ammi suka yi wa Zarah wanda ko da mahaifiyar ta ce iyakar abinda zata iya faɗa mata kenan, ita kam in banda kuka babu abinda takeyi saboda tuno mahaifanta da tayi, shikuwa Daddy da aka kai mishi Zarah domin yi mata faɗa kasawa yayi illa kawai yace. "Fatimah yadda kikemin biyayya a matsayina na mahaifinki ina roƙon Allah ya baki masu yi miki fiye da yadda zakimin, nasan ko ba'a faɗa miki ba zakiyi wa mijinki biyayya, Allah ya kareki daga sharrin maƙiya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya dauwamar da farin ciki a zuciya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki nasara akan duk abinda kika sa a gaba." Mutanen dake falon ne suka amsa da Amin, daga haka kuma yabar falon ya shige ɗakinsa domin kwallace ke neman sauko mishi. Ita kam Baaba da aka kai mata Zarah miƙewa kawai tayi ta bar gurin tana kuka kamar ranta zai fita wanda mutane da dama suka fara zargin akwai dalilin da yasa ake ta wannan koke-koken, duk da cewa ansan wannan kukan ya zama kamar na al'ada amma wanda sukeyi ya wuce ƙa'ida. A haka a sakata a mota aka wuce da ita gidanta dake Federal lowcost Gombe, duk wannan budurin da akeyi Jidda bata ciki domin tun yamma Saleem yazo ya ɗauketa a gidan bikin saboda irin kukan da takeyi. Duk yadda Abdallah yaso amma M.J ya tubure akan babu wani wanda zaiyi mishi rakiyar ango, dole suka rabo dashi ya wuce gidansa shi kaɗai. Da haka dai biki ya watse sai fatan zaman lafiya ga amarya da ango. :::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::: Wayarsa dake ta faman ruri ne ya saka dole ya sake baturiyar suke manne da juna akan gado ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, ganin mai kiran ne yasa shi firgita tare da sauka a gadon yana kara wayar a kunne. "Barka dai yallaɓai." "Don't dare to yallaɓai me, wato kaje ƙasar waje kana hutawa kabar komai yana lalacewa anan ko, wannan shine amanar da zaka yi min eye? Saboda na wadata ka da kuɗi shiyasa

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29