Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

tambaya fuska a yamutse. "Ƴar aiki na samu mana, tunda Iya Delu dai bamusan ranar dawowarta ba." "Ƴar aiki kuma.?" "Ehh ko banyi daidai bane uwata.?" "A'a kawai nayi mamakin inda kika samo ƴar aikin ne bayan ba fita kikeyi ba." "Nan tazo neman aikin, toh ganin muna buƙata yasa na ɗauketa, kuma naga tana da hankali da nutsuwa shiyasa bayan haka kuma marainiya ce." "Ana ɗaukan aiki batare da bincike bane Baaba.?" Harara Baaba ta wurga mata kana tace. "Nasan ki ai da shigen bin ƙwaƙƙwafi shiyasa ma na nemi wacce ta kawo ta birnin muka zanta, bayan haka kuma ga lambar ta nan na karɓa idan kinason jin ƙarin bayani, mtsww." "Me yayi zafi Baaba tunda ke zata dinga taimakawa, nikam ai bani da matsala tunda ba gidan nake wuni ba." "Yo ai nayi tunanin koh kulle ni zakayi tunda nayi abu batare da izinin ki ba." Ita dai Jidda bata saka baki ba, tana zaune a kujera ta kurɓar fresh milk ɗin da ta ɗauko, saboda surutunta ne ma yasa bata saka baki ba domin dai Baaba batasan a fara magana a bari ta daɗi ba, shiyasa ta barta da Zarah sanin da tayi cewa Zarah bata da magana sosai, tasan zancen bazai yi nisa ba za'a ƙarƙareshi. "Kin ci dambun ne Baaba.?" Zarah ta tambaya fuska babu walwala. "Na ɗebo kenan zanci ai kuka shigomin a birkice." Batace komai ba ta ɗau plate ɗin dambun ta nufi hanyar kicin. "Ina zaki kaimin abincin kuma.?'' "Yau ba dambu na tsara zamu ci a gidan nan ba, dan haka babu mai ci. Habibaty taso mu dafa wani abu mai sauƙi kafin SaJid ɗin naki da baya jurar yunwa ya dawo." ta faɗa tana mai shigewa corridor ɗin dazai sada ta da kitchen. Jidda ma tashi tayi da sauri ta bita tun kafin Baaba tayi magana. "Ki kiyayeni fa Zara'u wallahi zan saɓa miki, ki kawomim abincin nan tun kafin na iso gurin na sameki." Faɗin Baaba dake ƙoƙarin tashi ta nufi kitchen ɗin. "Kulle ƙofar nan SaJid karta zo ta dame mu." "Toh ke wai meye dalilinki na hanata cin dambun ne, nima wallahi ya bani sha'awa so nake naci." "Kawai naji ban yarda da girkin bane, dan haka babu mai ci." "Kamar ya baki yarda da girkin ba? tsabtar shi ko me.?" "A'a bansan hanyoyin da aka bi aka sarrafa shi ba ne shiyasa, da ace ina gida ma babu wata ƴar aiki da zamu ɗauka saidai mu jira har zuwa lokacin da Iya delu zata dawo." "Ƙyanƙyami ne kawai irin naki amma kina ganin dambun nan ai kinsan an tsabtace shi, nikam banga ƴar aiki da ake magana akanta ba ma." "Ƙila tana ɗakin da Iya Delu ta zauna. Mu haɗa Jallof ɗin cous-cous kawai nima yunwar nakeji sosai." Cikin ƙanƙanin lokaci suka haɗa lafiyayyen cous-cous da yaji kayan haɗi da nama, sai lemun citta da fruit salat da suka yi. A faranti suka jere komai, inda Jidda ta ɗauka domin zuwa ta jere a dinning, ita kuwa Zarah fruit salad ta ɗeba a plate ta nufi cikin falon. Baaba na nan zaune inda ta barta, saɓanin ɗazu da take ita kaɗai yanzu tare suke da wata da bata ga fuskarta ba, remote ta ɗauka tare da canja tasha daga Sunnah TV zuwa TVC News kana ta zauna a kujerar dake fuskantar Raliya dake zaune a ƙasa rakuɓe a jikin kujera. "Ya zaki canja mana tasha muna kallon wa'azi zuwa tashar arna." Faɗin Baaba a hassale. "Kiyu haƙuri Baaba ta ki daina wannan fushin da ni kinji, labarai kawai zan kalla na tashi." Sai a wannan lokacin Raliya da tayi nisa a cikin tunani ta lura da shigowar Zarah, kallonta tayi ta ƙasan ido, ai nan dake ta ɗauke kanta daga kanta saboda wani irin kwarjinin Zarah da ta hango. Cikin dakiya da dauriya tace. "Ina wuni ranki ya daɗe." Kafeta da ido Zarah tayi tana son gano wani ɓoyayyen abu a tattare da ita. Ita kuwa Raliya kai ta sunkuyar cikin ruɗu tare da tunanin ko Zarah ta gane ta ne. "Banason haka fa Zara'u kin kafe baiwar Allah da ido tamkar mai laifi a bayan kanta." "Marabar kaɗan ne." cewar Zarah a cikin ranta duk da batada wani tabbaci akan yanayin rashin gaskiya da zuciyarta ke gayamata akan Raliyan. "Lafiya." ta faɗa a taƙaice tana mai cigaba da cin fruit salad ɗin. Sunanan a zaune a falon har lokacin da Saleem ya dawo, Baaba ce take tambayar Saleem ɗin yadda shari'ar ta kasance, baki ya buɗe da nufin labarta mana amma saidai kallon da Zarah ta mishi ne yasa shi cewa. "Baaba munyi nasara." yafaɗa a takaice domin ya gane ma'anar kallon Zarah a gareshi, nufinta karya faɗi yadda shari'ar ta kasance. "Hubby kai muke jira tun ɗazu, mu ƙarasa dinning yunwa mukeji." Su uku suka miƙe suka nufi dinning ɗin, Jidda ce tayi serving ɗinsu, nan suka fara cin abincin. Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta batare da ta amsa tambayar da Jidda ke mata ba...... *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Paid book._ _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP kuma N500. A tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._ *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Free Page* Haka nan taji tamkar ana umartarta ta zuwa ɗakin, da sallama a bakinta ta shiga duk da tasan babu kowa a cikin ɗakin, maida ƙofar tayi ta rufe kana ta jingina jikinta a jikin ƙofar tana mai ƙarewa yanayin ɗakin, yana nan kamar yadda ta barshi. Gaban durowar kayanta ta isa tare da tsayawa tana kallon gurin, tabbas wani ɓangare na umartarta da bincikar gurin saidai ɗaya ɓangare na hanata ƙoƙarin haka. Ƙarar wayar ta ne ya fargar da ita, kallon fuskar wayar tayi taga Ammi ce mai kiran, saida ta zauna a bakin gadon tukun kafin ta ɗaga wayar. "Ammi na." ta faɗa a hankali.. "Na'am daughter ya kuke." "Lafiya lau Ammi ya jikin Rahma." "Alhamdulullahi jiki ya fara samuwa, yanzu tana iya yin magana wasu lokutan amma ba sosai ba." "Allah ya ƙara lafiya." "Kin fara gyaran jiki kuwa Zarah." cewar Ammi Cikin son gane mai take nufi Zarah tace. "Wani irin gyara jiki kuma Ammi.?" "Zan saɓa miki fa, kina nufin baki fara amfani da kayan da Momin ku ta turo miki ba." cewar Ammin. Dafe kai Zarah tayi, sam ta manta batun kayan da Momi ta aiko mata dasu. Jin shiru ne yasa Ammi cewa. "Kina nufin haka zakije gidan mijin kamar almajira." "Ni fa Ammi.." "Ke fa me, toh wallahi ki fara amfani da kayan nan tun wuri, nima ina nan tafe zuwa wani watan domin mu fara shirye shirye da wuri." "Toh Ammi, Allah ya kawo lafiya." "Amin ki gaidamin da Baaba, su Jidda sun wuce Bauchi ne.?" "A'a sai zuwa jibi tukun, akwai wani case da muka gudanar da Saleem ne shiyasa basu tafi ba." "Ya batun binciken nan Zarah." Ammi ta tambaya cike da rauni. "Ammi batun bincike ai babu shi tunda an riga da ansan mai laifin." "Allah ya saka mana wannan zaluncin da ya aikata mana." cewar Ammi cikin rawar murya. Sallama Zarah tayi mata gudun kada itama ta fara

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29