Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Ammi su shigo next week sai mu tsara komai da Sis Rahama." Miƙewa tayi zaune daga kwancen da take tace "Wace Ammi." "Ammi nawa muke dasu dama.?" "Wato saboda anjireni a cikin dangi yasa duk wanda zaizo kasar ba'a faɗamin koh". "Ke kika sani nikam na tafi gurin habibi na." Kafin ta kuma magana kashe wayar, miƙewa tayi da nufin zuwa ɗaki sai....✍️ *VIP ayimin haƙuri dan Allah jiya banji daɗi ba shiyasa banyi typing ɗin ba. Sorry dan Allah*👏 *ASP ZARAH*👩‍✈️ Shigowarsu ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin miƙewa da take domin zuwa ɗakinta, sallamar da Abdallah keyi ta amsa ɗauke da murmushi a fuskarta. Bakj M.J ya kyaɓe lokacin daya zauna a kujera tare da faɗin "Mutum a fuska kamar na Allah saidai a baɗini ɓarnar da ake aikatawa ko kare bazai shinshina ba, Allah dai ya shirya wanda ya mayar da kanshi kwarkwar." "Ameen kuma gani kuturwar uwa zama dani dole." ta faɗa cike da basarwa kamar ba ita tayi zancen ba. "Amaryarmu ni dai yunwa nakeji ki rabu da wannan angon naki ki ceto rayuwata." Taƙaitacciyar dariya tayi har kyawawan haƙoranta suka bayyana sannan dimple ɗinta ya lotsa, ta gefen ido ya kalleta cikin rashin sanin dalilin dazai saka yaji haushin fara'ar da takeyi ma Abdallah. Kallo ya bita dashi lokacin data miƙe har ta shige kicin, tsaki ya kuma ja sannan ya kalli Abdallah yace "Akan wani dalili zaka dinga sake mata fuska haka.?" Dariya yayi harda buga ƙafa kana yace. "Ikon Allah! Tunda baza kayi mata fara'a ba ai saika bar masu yimata koh bawai ka dinga jin haushin mu ba." Bai kulashi ba sai miƙewa da yayi ya nufi ɗakin Baaba, shima miƙewa yayi tare da bin bayan shi domin zuwa gaida Baabar. Ganin basa cikin falon yasa ta shirya musu komai a dinning, ɗakinta ta kuma ta ɗau mayafi da makullin mota ta fita domin zuwa kasuwa tayi cefanen abubuwan da zata buƙata na girkin tarbar ɗan uwanta da kuma mahaifinta. Yayanta nason masa sosai shiyasa zata fita da kanta ta siyo sauran abubuwan buƙata na miya da basu dashi. Tare suka fito falon da Baaba inda suka nufi dinning table yin breakfast. "Bari na kirata ta zuba muku, Zara'u" cewar Baaba, Raliya ce ta taho da sauri ta iso gabansu tare da cewa "Hajiya Baaba bari na zuba musu, Anty Zarah ta fita." "Ina taje kuma." "Wallahi bata faɗamin ba amma kaman ba nisa tayi ba, naga batayi shiri ba." "Ai shikenan zuba musu, amma zata fita shine bazata sanar da ni ba." Ranshi ne yaji ya ɓaci saboda mummunan zaton da shaiɗan ke kitsima mishi na cewar gurin wani ta tafi domin suyi lalata, baice komai ba ya cigaba da cin abincinsa batare da ya kula Abdallah dake cewa. "Ko dai anyi mata kiran gaggawa ne." "Ina tunanin haka nima, kasan Zara'u da ƙulafucin aiki bataji bata gani idan aka kira ta wannan aikin nasu duk wani abu da takeyi saita ajiye ta tafi." "Yanayin aikin nasu kenan Baaba sunyi rantsuwar kare haƙƙin mutane." "Toh Allah dai ya tsare." "Ameen" Inji Abdallah Ko da suka gama cin abincin falon suka dawo suka zauna, hira suka cigaba dayi da Baaba wanda yawanci akan dawowar da su Daddy zasuyi ne. "Gashi shigowar yamma zasuyi kuma mu yau mukeson tafiya saboda aiki." "A'a ku tsaya mana dai ku gana duk da ma zaku haɗu acan amma ya kamata ace kun tsaya an tarbesu da ku." "Shikenan saidai muma muyi tafiyar jirgin kenan, bari na duba ko za'a samu jirgin dare." "Mezai hana ku ƙara kwana?." "Baaba nace miki fa akwai aiki." "Ku zama na'ura saboda aiki idan kun so." Dariya M.J yayi yace "Duk rashin son magana da nakeyi sai kinsa ni." "Yo me za'ayi da mutum miskili." "Ba zaki gane bane ai Baaba, babu fa'ida ace mutum ya kasance mai yawan surutu." "Shiyasa ma aka haɗa ka da wacce ta dace dakai gurin rashin son magana." Bai kuma magana ba illa cigaba da danna wayar shi da yayi, itama Baaba miƙewa tayi ta nufi kitchen. 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎 "Raliya! Raliya!! Raliya!!! sau nawa na kiraki?" ya faɗa cikin fusata. Cikin shessheƙar kuka ta amsa mai da "Sau uku ranka ya daɗe." "Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce da batasan abinda takeyi ba, duk tsawon lokacin nan da kika ɗauka a cikin wannan gidan aikin me kikeyi da har yanzu kika kasa samo wani gamsasshen bayani .?" "Kayi haƙuri yallaɓai wallahi ina ƙoƙarin ganin na samu masaniyar inda lu'u lu'un suke." "Kullum abinda kike faɗamin kenan, amma sai yaushe ne zaki kawo min wani bayani mai amfani eye.?" "Fashi da makami." "Ke Raliya! Baki da hankali ne, kada ki kuskura ki fara aikata wannan mummunan kuskuren, wannan hanyar ba mai billewa bace. Da mai amfani ce bazamu kai war haka batare da mun mallaki wannan kadarar ba, ko zamu kuma aikata hakan ba nan kusa ba akwai sauran lokaci." "Amma yallaɓai naji kamar batun aurenta akeyi." A kishingiɗe yake amma jin wannan batun yasa shi miƙewa batare da yasani ba, cin hargagi yake faɗin. "Aure! Aure dai? Meyasa baki faɗan hakan tuntuni ba Raliya, sai zuwa yaushe ne ƙwaƙwalwarki zata dinga yin abinda ya kamata ne." "Kayi haƙur..." "Hell with this fucking word Raliya! Hakurin me zanyi, abubuwa na shirin lalacemin kice wai nayi hakuri." "Amma yallaɓai naga wanda zata aura ɗan gida ne shiyasa banyi tunanin komai." "Wanene wanda zata aura ɗin." "M.J ne." Wani murmushi yayi mai sauti kana yace. "Woow! Komai ya kusa zuwar mana da sauƙi, kin tabbata shine wanda zata aura." "Na tabbata ranka ya daɗe yanzu haka ma yana garin Bauchi yazo ganinta." "Ki tsaya ki saurareni dakyau Raliya, wannan ne lokacin mu na samu ko rashi, a yanzu ne muke da damar yin duk wani abu da muka daɗe muna shiryawa, inaso ki lura sosai da duk wani motsinta daga yau, saboda inada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za'a nemi sauyawa diamonds ɗin nan wajen zama, ki sanar dani duk wasu bayanai da zaki samu, zan organising team ɗin da zakuyi aiki tare da zarar angano inda suke kiyi ƙoƙarin samu mana bayanai kawai." "Zan kula sosai yallaɓai." "Ohk" kawai ya kuma faɗa tare da kashe wayar. Shiru tayi bayan gama wayar tasu tana tunani, tabbas wannan ita kaɗaice damar da take da ita domin ƙara samun kusanci da Alpha, ya zama dole yanzu ta shirya ɗamarar yin fito na fito da Zarah akan Diamonds ɗin nan, ba damuwarta darajarsu ba ko kuɗin da za'a samu akansu, babban abinda ya dameta shine ta wannan hanyar ne kaɗai Alpha zai dinga ganin ƙimarta har ta samu nasarar cusa soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda sanin yadda yake da babban buri akan Diamonds ɗin. "Lokaci yayi da zanja ragamar wasan nima." ta faɗa cikin wani shu'umin murmushi. 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 Gefen hanya ta samu tayi parking motarta saboda kiranta da Jidda keyi a waya, hannu tasa ta ɗauki wayar tare da maida kiran daya kuma katsewa. "Ina kika shiga ne nake kiranki bakya ɗagawa." "Toh shugabar masu ƙorafi tuƙi nakeyi." "Kin fita aiki ne?." "Aa cefane naje yi inaso na shiga kitchen da kaina na shiryawa Big Bros abincin." "Nima ai naso zuwa wallahi Sa.Jid ne ya hanani wai saura

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29