Chapter 27
Chapter 27
buɗe kaɗan ganin mutanen ɗakin basa cikin hayyacinsu bare su lura da ita, tsananin tashin hankali da firgici ne ya ziyarceta lokaci guda ta fara ɗika saboda zufar da tayiwa jikinta ƙawanya lokaci ƙanƙani.. Wata irin shaƙa Zarah takai mata........✍️ 😱😱😱😱😱😱😱 *YANZU NE FA ZA'A FARA ASALIN LABARIN _ASP ZARAH_👩✈️ MATAR MUHAMMAD JAWWAD KAWAR JIDDAH MATAR SALEEM. LOKACIN DA ZAMUGA ƁOYAYYEN SIRRIN DAKE TATTARE DA JIDDAH YAYI FA🤔* *SHIN ZARAH ZATA MAIDAWA DADDY DIAMONDS ƊINSA KO KUWA ZATA BARSHI A WAJENTA HAR SAI ZUWA LOKACIN DA ZATA KAUDA ALPHA.???* *ME ZAI FARU TSAKANIN ZARAH DA RALIYA NE A WANNAN FITO NA FITO DA SUKAYI.???* *WANI MATAKI DADDY ZAIYI NE IDAN YAJI LABARIN ABINDA ƊANSHI YAKE AIKATAWA GA YARINYAR DATA SADAUKAR DA KOMAI NATA DOMIN KARE DUKIYARSA WACCE TA DALILIN HAKANE TA RASA IYAYANTA SANNAN ƳAR'UWARTA TA FICE A HAYYACINTA.???* *AURAN MUHAMMAD JAWWAD DA FATIMAH ZARAH NA YIWUWA KUWA.???* *SHIN ALPHA YANA SAMUN NASARAR MALLAKAR WAƊANNAN LU'U LU'U MASU MATUƘAR DARAJA.???* *YA BATUN RAHAMA A CAIRO. INA MUSTAPHA KUMA???.* *SHIN TANA SAMUN NASARAR KAMA ALPHA KAMAR YADDA TASHA ALWASHI.???* *MEZAI FARU NE IDAN M.J YA GANE IRIN SADAUKARWAR DA ZARAH TAYI AKAN DUKIYAR MAHAIFINSHI.???* *INA BATUN ALMAJIRAR DA ZARAH TA TAƁA HAƊUWA DA ITA NE.???* _DUK AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WASU NA TARE DA JASMINE🌸🌸 A CIKIN LITTAFIN ASP ZARAH👩✈️, YANZU AKA FARA_. *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH* Wata irin shaƙa Zarah takai mata saidai cikin zafin nama ta kauce tare da hankaɗa Zarah ta faɗi ƙasa sannan ta nufi hanyar matattakalar da zai sadata ƙasa, ganinta tayi a gabanta tamkar wacce aka jefo kafin ta ankare taji saukar duka ta ko ina a jikinta ta yadda babu ta inda zata iya kare kanta, dukanta takeyi sosai tamkar wacce ta kama ɓarawo a bayan kanta. "Baki da hankali ne Zara'u me tayi miki kike dukanta? Ki sake ta tun kafin raina ya ɓaci." Baaba kenan ke faɗi bayan ta fito taga abinda ke faruwa, shikuwa Sadiq yana gefe a tsaye bai tanka ba domin yasan hakan nan Zarah baza ta yiwa Raliya wannan dukan ba idan ba wani mumminan laifi ta kamata dashi ba. Saida taga ta daina motsi kafin ta sassauta duk kuwa da hargowar da Baaba keyi mata akan ta rabu da ita, hannu ta saka ta fincike hijabin dake jikin Raliyan saidai ga mamakinta ba hijabi ɗaya bane a jikinta, saida ta cire hijabai uku kafin tayi tozali da jikinta kai tsaye hannu ta saka ta juyata daga kwancen da take kamar gawa ta duba gefen wuyanta, kamar yadda tayi tsammani kuwa zanen tatto ne a gefen wuyan nata, bishiyar kwakwa ne da sunan Alpha da aka ƙayata ta hanyar zanen, ɗaki ta shiga ta ɗauko wayarta ta ɗauki hoton gurin kana ta danna kiran waya tana karawa a kunnenta. "Kuzo da mota biyu gidan mu." shine kawai abinda ta faɗa kafin ta juya ga Baaba wacce ke sharar kwalla tana sambatu. Hannunta ta riƙo suka koma cikin ɗakin ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna tare da karɓar ruwan da Yayanta ke miƙa mata tasha sannan ta maida kofin yaƙara tsiyayawa ta miƙa ma Baaba itama. "Shikenan kin ja mana zagi a gari Zara'u za'ace mun kasa riƙe waɗanda ke ƙarƙashin mu." "Baaba tun ranar da kika gayamin kin ɗauki yarinyar nan aiki na nunq miki banso ba, haka ne." "Eh sai me dan bakiso ba ai ni inaso, shiyasa kike neman ki mata lahani tana marainiya." "Wai ke waya gaya miki wannan yarinyar marainiya ce Baaba? Spy ce fa aka turo mana a matsayin mai aiki." "Mene ne haka.?" "Ƴar leƙen asiri mana, Alpha ne fa ya turota.? Wani zabura duka su biyun sukayi a tare suka kuma haɗa baki wajen faɗin "Alpha.???" "Kwarai kuwa." "Kin tabbata little.?" "Sosai na daɗe da tabbatar da haka banaso na kamata a bisa zargi ne shiyasa amma da ta daɗe da zama a kurkuku, zo muje ɗakinta ka gani." Miƙewa sukayi duka suka nufi ɗakin Raliyan, sosai Baaba tasha mamakin abubuwan da Zarah ta nuna musu a ɗakin wanda babu ko tantama duk wanda yaga wannan yasan akwai abinda ake ƙullawa. "Tabbas ɗan adam na da wuyar fahimta, ki duba kiga yadda yarinyar nan ta ɓadda kama ta zo min a maraice tana roƙon abata aiki ashe cutar mu tazo tayi, Allah ya toni asirinta. Allah sarki Zara'u shiyasa sam baki yadda ko gurin zama ku haɗa ashe kinsan abinda kika gani, ni kuma duk da haka ban fahimci komai ba." "Gaba saiki kiyaye kisan waɗanda zaki dinga zaɓa kuyi mu'amala tare..." Ringing ɗin wayarta ne ya hanata kai aya a zancen nata. "Ehh ku shigo falo" haka kawai ta faɗa ta kashe wayar. "Jami'ai sun iso muje." "Ina za'a kaita ne little." "Za'a cigaba da tsaronta har zuwa lokacin da za'a kama maigidan nasu a yanke musu hukunci." "Kina ganin hakan bazai janyo wata matsalar ba." "Babu abinda zai faru Yayana da izinin Allah." "Toh Allah yasa." "Amin " suka haɗa baki wajen faɗa ita da Baaba, sannan suka bar ɗakin zuwa falo inda jami'an suke. "Ku tafi da ita Nura a fara kaita asibiti a duba lafiyarta daganan sai a wuce da ita station a rufe ta, ban yarda ko waye yazo a fito da ita ba, sannan duk wanda yazo belinta indai ba jami'i bane to a haɗa dashi a rufe, kuna jin abinda na faɗa koh." "Zamu kiyaye ranki ya daɗe." "Joy da Halima ku ɗauketa ku kaita mota sai ku wuce." Sara mata sukayi duka sannan sukayi kamar yadda tace suka fita a falon. "Allah ya kyauta ya daɗa karemu daga kaidin wannan mutumin." "Amin thumma Amin.'' cewarsu duka. "Yauwa Baaba sai batun auren Little da M.J gaskiya za'a janye ba za'ayi wannan auren ba." "Akan wani dalili za'a janye batun auren? Toh indai akan abinda Muhammadu yakeyi ne wannan auran babu fashi sai anyi shi, watarana ko kuɗi aka bashi yayi wannan abun bazai iya ba." "Amma fa kinajin irin alwashin da yake ɗauka akanta muddin ta amince akayi auran." "Naji tun ba yau ba nasan duk abubuwan da yake faɗa game da ita wanda nasan ba haka bane amma inaso mu tura mishi aniyarsa ayi auran. Duk abubuwan da suke faruwa fa bai sani ba na tabbata ranar dazai san wani abu a game da abinda takeyi zaiyi nadamar komai daya aikata a gare ta, dan haka aure nan da sati biyu babu fashi." "Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhari." "Amin ai addu'ar daya kamata kayi kenan Allah ya zaɓa mata abinda yake shine alkhairi a wannan auren." "Uhmm! Little me kuka shirya game da events ne." "Babu abinda zamuyi Yaya." "Bai kamata ba gaskiya, ko sports daya ai zamuyi." "Hakane fa Bro kuma kamar kasan mun daɗe bama yin sport wallahi." "Eh nasan Sis Rahama zataso hakan sosai." Murmushi kawai tayi mai kama dana ciwo domin duk sanda za'ayi maganar sports sai ta tuna mahaifanta. "Wani wasa kika zaɓa." "Dear inajin volley ball zaifi tunda kaga harda mata a ciki." "Hakane amma gidan Daddy akwai pitch ne." "Ehh mana ai saboda mu yasa akayi sports garden tun waccen lokacin idan mukaje muna playing dasu brother Adil da Nusaiba..." sai kuma hawaye shar ya biyo bayan maganarta ta. "Bana sonki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29