Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

 *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* _Putting smile on our readers faces._ https://www.facebook.com/0946102referrer=whatsapp ___________________________________ *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.* *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_ *Free PAGE 1* "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Shine abinda matashiyar yarinya wacce ke sanye da kayan ƴan sanda take maimaitawa, alamu sun nuna cewa suma tayi aka watsa mata ruwa ta farfaɗo duba da yadda take a kwance a ƙasa idanu a rufe ga fuskarta data jiƙe da ruwan da aka watsa mata. Jin ana ƙoƙarin ɗagata a ƙasan ne yasata buɗe ido domin ganin mai taɓatan, Ammi ce wacce take matsayin ƙanwa ga mahaifinta. Kallon fuskar Ammin tayi wacce ta kumbura tayi jazir saboda kukan da tasha domin hatta idanunta sun koma can ciki ba'a ganinsu sosai saboda kumburin da fatar idon nata tayi. "Zarah kuka ba shine mafita ba a yanzu, kizo kiyi sallama dasu domin a samu damar kaisu makwancinsu da wuri." Ammin ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta. Buɗe baki tayi domin magana amma kukan data kasayi tun farko ya riga maganartata fitowa, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro. Hannunta Ammi ta kama ta ɗagota tare da nufar inda gawarwakin mutane takwas dake sanye da suturarsu ta ƙarshe a cikin makara, koda ta iso da ita wajen sake hannunta tayi tare dayin baya domin kukane yakeson ƙara kece mata. Cikin rawar hannu ta fara yaye mayafen daya lulluɓewa gawarwakin fuska tundaga kan gawa ta farko. "Mahaifina, Mahaifiyata, Kakannina uku, ƴan biyun ƙannena sannan ƙaramar ƙanwata. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ta ƙara fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya, lokaci ɗaya kuma ta tsagaita tare da gyara rufuwar mayafan sannan ta ɗaga hannu sama ta fara addu'a. "Ya rabbi, Ya rabbi, Ya rabbi. Ya Hayyu ya Qayyum ya Allah ina gode maka a cikin kowani yanayi dana tsinci kaina. Ya Allah kaine shaidata ban shiga aikin ƴan sanda ba saidan na taimaka gurin gyara ƙasata, Ya Allah kasani ina tsare duk wasu dokokinka bana saɓawa da gangan saidai a rashin sani. Ya ubangijina nasan ka fini son waɗannan bayi naka shiyasa ka karɓesu daga aron daka bamu, na karɓi wannan jarabawa hannu biyu sannan ina ƙara gode maka. Ya Allah ga bayinka nan zasu iso gabanka Ya Allah kayi musu gafara ka yafemusu zunubansu wanda sukasan sun aikata dama wanda basu sani ba, Allah kayi musu rahama, Ya Allah ka tsare daga duk wata fitina dake cikin kabari Allah ka karɓi shahadarsu. Ya Allah kabasu wani ɓangare a cikin Aljannarka. Ya rabbi baka aikata zalunci sannan baka barin masu aikawa, Ya Allah na kawo ƙarar duk wani wanda yake da hannu a cikin mutuwar bayinka muminai." Hatta mazan dake farfajiyar wajen saida suka zubda hawaye tare da jinjina jarumtar Zarah. Batare da ɓata lokaci ba aka sallaci gawarwakin sannan aka tafi sadasu da gidajensu na gaskiya. _Kafin faruwar wannan al'amarin_. Tsantsar abota da aminci ne a tsakanin Malam Usmanu da Malam Adamu wanda ya rikiɗe ya kuma ƴan'uwantaka hakan ya samo asaline tun daga iyayensu da sukayi zaman aminci tare, hakan kuma ya ƙarayin sanadin da yaransu suka taso cikin shaƙuwa da son juna tamkar iyayen nasu sakamakon gidajensu dake maƙotaka da juna. Asalinsu mutanen garin Deba ne a jihar Gombe kuma a nan suke da zama da iyalansu, da sana'arsu ta noma suke rufawa kansu da iyalansu asiri. Malam Usmanu yanada mata ɗaya Faɗimatu da ɗansu Abdul_Jalal wanda shi kaɗai suka haifa. Yayinda Malam Usmanu keda yara biyu Sulaiman da Rumaisa sannan matarsa Aishatu. Yaran sun taso cikin so da kulawar iyayensu, tare sukeyin komai tun yarinta har zuwa girmansu. Sulaiman shine babba cikinsu wanda a yanzu haka yake zaune a cikin garin gombe tare da yaransa biyu Muhammad Jawwad da Nusaiba dakuma matarsa Safiyat wacce yaran ke kira da Momi. Inda ya kasance ɗan kasuwane a fannin ma'adanai. Sannan Abduljalal dake zaune a garin bauchi da nashi iyalan inda yake aiki a babban asibitin tarayya dake jihar bauchi. Yanada matarshi ɗaya mai suna Zainab (Mami) sai yaransa uku Abubakar Sadiq, Rahma, sai Fatimah Zarah. Rumaisa kuwa(Ammi) a ƙasar Cairo take zaune da mijinta wanda ya kasance ɗan kasuwa da ƴan biyun ta Muhammad Adil da Muhammad Shahid. Duk da kasancewar ba guri ɗaya suke rayuwa ba, sukan ware lokuta domin zuwa ziyartar iyayensu a garin Deba. Hakan yasa yaran sukayi sabo da juna sosai in banda Muhammad Jawwad da tun bayan kammala karatunshi na firamari aka kaishi England domin ya cigaba da karatunshi a can. Haka wannan familyn suke kasancewa koda yaushe cikin so da ƙaunar juna. Mafarkin Zarah nason zama ƴar sanda ya fara tun lokuta da dama da take ganin ana zaluntar talakawa sannan ƴan sanda suƙi ɗaukan mataki, hakan yasa tasha alwashin zama ƴar sanda. Daƙyar iyayenta suka aminci da wannan buƙatarta ta domin saida ta kaita ga kwanciya a asibiti tamkar bazata rayu ba, ganin haka ne yasa suka amince tare da kafa mata sharuɗɗan kare mutuncinta dana danginta. Wani al'amari daya faru a rayuwarta wanda ta kasa mantawa shine. _Garin Bauchi_ 12:30nr Gosulo ne sosai akan titin wanda ya kasance ana yawan samun cunkuson ababen hawa duk ranar juma'a saboda tare wasu hanyoyi da akeyi sakamakon sallar juma'a da ake gabatarwa. Cikin waɗanda gosulon ya tsayar harda direban daya ɗauko Zarah daga makaranta. Saidai gabaɗaya hankalin Zarah dake cikin motar ya koma ga wata tsohuwar almajirah dake gefen hanya zaune da roba tana bara, sosai ta bata tausayi ganin babu wasu masu bata sadaka dayawa. Jakar makarantarta ta duba saidai naira ɗari biyu ne aciki.. "Baba Sule akwai kuɗi a hannunka ne". Ta tambayi direbansu dake jan motar. "Ehh baza'a rasa ba". "Zasu kai nawa ne." "Inajin zasu kai dubu biyar ko sufi haka". Ya faɗa sanda yake ƙoƙarin ƙirga kuɗin daya zaro a aljihunshi. Karɓa tayi tare da fita a motar ta nufi inda matar ke zaune. "Sannu Baba ya zaki zauna a rana ki koma inuwa mana". Cewar Zarah lokacin data ƙaraso gurin. "Ƴar nan idan kayi nesa da jama'a wasu bazasu zo inda kake su taimaka ba

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29