Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 565 words 0 views Progress saved
Download Book

kake duk abinda kaga dama ko.?" Cikin ina ina yace "Ba haka bane yallaɓai ayi min afuwa." Tsawa ya daka mai cikin fusata ya kuma yin magana yace. "Afuwar me za'a maka, wato kai kaje ƙasar waje kana sha'aninka koh, ace ina tare da commisioner of police gabaɗaya amma a kama Raliya kusan fiye da sati uku amma ankasa yin komai akai." "Innalillahi! Yallaɓai Alpha kace an kama Raliya." "Bani da buƙatar maimatawa tunda kaji me nace." "Amma garin yaya waya kamata." "Wa kake tunani.?" Ido C.P ya waro waje kamar wanda yaga wani mummunan abu mai firgitawa yace. "Zarahh.???" "Ka amsa tambayarka." "Ohh shit! Dole zan dawo ƙasar gobe a fito da Raliya." "A fito da Raliya fa kace! kasan ko a wani ofishin ƴan sanda Raliya takr zan iya zuwa na fiddata, amma ba anan take ba bansan a ina yarinyar nan ta ɓoyeta ba. Kayi gaggawar kiranta ka bata umarnin fito da ita a ko ina ta aje ta." "Bari na kira ofishin su yanzu, Raliya bazata kuma kwana a hannunta ba" Umma"Ina jiran sakamako mai kyau." "Toh yallaɓai yanzu zan kira." Cikin rawar jiki ya danna lambar mataimakin shi, ringing biyu ya ɗauka yana gaidashi, bai tsaya amsawa ba ya fara magana. "Ka kira office ɗin ASP Zarah ka bata umarnin sake yarinyar da ta kulle a cell, ka gayamata wannan umarni na ne." "Yallaɓai ai babu wata yarinya a ofishin nan wacce aka kulle." "Ba tambayarka nakeyi ba umarni ne nake baka." "Amma yallaɓai naga Zarah yanzu ba anan take aiki ba, kila bata zda masaniyar abinda ke faruwa ko dai ba ita ɗin bace.?" "Bata aiki kuma ??? ASP Fatimah Zarah Abduljalal nake nufi fa." "Ehh yallaɓai ai ta nemi takardar transfer zuwa Bauchi saboda za'ayi aurenta, jiya ma muka dawo daga ɗaurin auren." "Damn it!! Wane ne ya aiwatar da hakan ba tare da sani na ba." "Yallaɓai ta je Abuja ne daga can ta gama komai, wasu signing ne kawai da akeson kayi ni nayisu a madadinka." "Meyasa ba'a tuntuɓeni ba eyee??" "Ranka ya daɗe kamar naga babu buƙatar hakan." Tsaki ya ja gami da ya kashe wayar batare daya kuma magana ba, kanshi ya dafe cikin taraddadin yadda zai kira Alpha ya gaya mai wannan labarin, gabanshi ne ya faɗi ganin kiranshi na kuma shigowa, cikin fargabar mai zai faru ya ɗaga kiran. "Ya ake ciki??" ya tambaya babu walwala. "Ehmm dama.." "Straight to the point, banason dogon zance." "Yallaɓai wai anyi mata transfer zuwa garin Bauchi saboda zatayi aure acan, jiya ne aka ɗaura auren nata a garin Bauchi." Shiru yayi baiyi magana ba har hakan ya baiwa CP tsoro, sai can yace. "Duk abinda kakeyi kabari a yau ɗin nan ka dawo ƙasar nan, sannan karka kuskura ka kirani matuƙar ba shaidamin zakayi ka kuma Bauchi da aiki ba." daga haka ya yanke kiran. Babu yadda commisioner yayi iya dole ya fara haɗa tarkacensa bayan ya sallami baturiyar da suke tare, cikin lokaci ƙanƙanin lokaci ya gama shirin komawa ƙasarsa Nigeria....✍️✍️✍️ *Tammat bi Hamdulillahi!! Littafi na ɗaya ya ƙare anan, zamu shiga littafi na biyu da izinin Allah kafin sallah. Nima zan ɗanje hutu na kwana biyu kafin mu ɗora.* *Ina yinku sosai Zarah's fans, Mrs. Khaleel from VIP ina yinki sosai ina godiya da ƙaunarki a gareni Allah ya bar xumunci a tsakanin mu. Sai kunjini a kashi na 2*🥰 *By* *Jasmine*🌸🌸

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29