Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

wanda suke cike da gashin gira dana ido, dogon kuma matsakacin hanci ta da kuma ƙaramin bakinta suke ƙara bayyana kyawun da take tattare dashi. Kai tsaye falon Abbansu ta nufa, a zaune ta same su shida Maminsu alamun magana suke mai mahimmanci, bayan ta gaishesu ne ta sanar dasu zata wuce gurin aiki. Abban ne ya dakatar da ita daga shirin miƙewa da take sa'an nan yace "Zarah inaso na ƙara jaddada miki cewa duk rintsi kada ki maidawa Daddyn ku Sulaiman ajiyarshi kowani hali kika tsinci kanki ciki matuƙar bashi ya buƙaci ajiyarsa ba." "Toh Abbah insha Allahu zanyi yadda kace." Ta faɗa cike da ladabi "Allah ya muku albarka gabaɗayan ku ya ƙara haɗe kanku ko bayan bama nan." "Ameen Abbah." Daganan ta miƙe ta musu sallama tare da barin falon hakan takejin wani irin yanayi a tare da ita. Bayan fitarta ne Alhaji Abdul_Jalal ya kalli matarshi yace" Ina tsoron abinda taƙadirin nan zai aikata ga yarinyar." "Babu abinda zai sameta da yardar Allah." "Ameen dai amma wannan mutumi abun tsorone." Haka suka cigaba da tattaunawa game da lamarin Alpha ɗin har zuwa wani lokaci. Ƙarfe sha biyu a cikin Gombe tayi musu kai tsaye suka nufi Gwallaga Inda anan gidansu Zarah yake. Cike da farin cikin ganin juna aka tarɓesu sannan aka cika musu gaba da abubuwan motsa baki. Hira aka cigaba dayi har zuwa lokacin sallar azahar Inda mazan suka wuce masallaci matan ma suka miƙe domin gabatar da tasu. Bayan anyi sallah ne kuma aka zauna cin abincin gargajiyar da Mami ta shirya, cike da barkwancin da kakannin keyiwa jikokin nasu. Haka suka kasance cikin farin ciki har zuwa lokacin da sukayi haramar tafiya. Baba Lado mai gadi na zaune akan wani benci dake jikin gate yaji anyi horn, koda ya leƙa bai gane na cikin motar ba sai ya tsaya batare daya buɗe gate ɗin ba, wani ne ya fito daga cikin motar sanye da manyan kaya ya iso jikin ƙofar inda Baba Lado ke tsaye. "Baba dan Allah me gidan yana ciki kuwa.? " Kafin ya samu damar amsawa yaji an rufe mishi fuska da wani abu, tun daga lokacin bai kuma fahimtar komai ba. Mutumin da kanshi ya buɗe gate ɗin motar tazo ta shige sannan ya kulle. "Bari naje bayi na dawo Inna sai na baki saƙon da zaki kaiwa kishiyar tawa." Faɗin Rahmah dake ƙoƙarin shiga banɗakin dake can gefe a cikin falon. Dariya sukayi gabaɗaya domin dai Rahma akwai barkwanci dason ganin duk wanda ke tare da ita cikin farin ciki. Shigewar Rahma keda wuya aka buɗe ƙofar falon, inda wasu mutane dake sanye da baƙaƙen kaya fuska rufe suka shigo. Adadin su bakwai ne sannan kowanne a cikinsu na riƙe da bindiga. "Kada wanda ya motsa ko ya mana hargowa." Babu wanda ya motsa a ciki saidai Idan mutum ya lura da bakinsu zai gane addu'o'i sukeyi. Babbansu ne ya bada umarnin a ɗauresu gabaɗaya tare da kulle musu sannan a bincika sauran ɗakunan ko akwai wani a ciki, dukkan sashe na gidan suka duba amma ba suga kowa ba. Kasancewar sai an ɗaga labule Kafin aga ƙofar banɗakin da Rahma ke ciki yasa sam basuyi tunanin akwai wata ƙofa a falon ba sakamakon labulayen da suke a jere har gaba da ƙofar bayin, Idan ba ɗan gidan bama babu wanda zai san akwai banɗaki a wurin. Waya wani ya ciro tare da karawa a kunne. "Shugaba rayuka takwas ne cikin gidan a yanzu." Jim akayi daga ɗaya bangaren kafin akayi magana. "Su faɗa muku Inda akwatin yake da mabuɗinsa idan kuma sunyi taurin kai to ku tabbatar babu wanda ya rayu cikin takwas ɗin."..... Bayan ya kashe wayar ne ya juyo tare da maida hankalinshi inda suke, umarni ya bada aka buɗe ma Abba bakin shi dake ɗaure. "Alhaji inaso ka faɗamin inda akwatin da lu'u lu'un ke ciki da kuma mabuɗinsa, ba tashin hankali ya kawo mu ba ku bamu abinda mukeso mu tafi batare da cutar da wani ba." Ya ƙarasa faɗa yana mai saka bindiga a goshin Abban. Motsa jiki da Malam Usmanu keyi ne ya hana Abba magana ganin Ogan nasu ya nufi wajenshi tare da kunce masa ɗaurin dake bakinsa. "Abdul_Jalalu a matsayina na mahaifinka ban yarda ka faɗamusu idan ajiyar da ɗan'uwanka Sulaimanu ya baka ba, idan kayi hakan kuma bazan taɓa yafe maka ba ko bayan raina." Faɗar Malam Usmanu bayan an kunce masa ƙullin dake bakinsa. "Ba muzo nan domin jin musayar kalaman da zakuyi ba, zaka faɗa mana ne ko bazaka faɗa ba.?" Ya maida akalar tambayar shi ga Abba bayan ya ƙara ɗaure ma Malam Usmanu bakinsa. "Bazan iya faɗi inda yake ba." Abban yafaɗa "Shikenan bazamu ɓata lokaci ba zamuyi abinda ya dace." Nufar inda Nusaiba take ɗaure kusada Shahid yayi tare da tsugunawa a gabanta, hannu biyu yasa tare da jan gaban rigarta da ƙarfi hakan yayi sanadiyar yagewar rigar atamfar dake jikinta tun daga sama har ƙasa wanda ya bayyana ƙirjinta da kuma fatar cikinta. Shahid wanda ya gane abinda yakeson aikatawa ga Nusaibar ne yasa ƙafafunshi biyu dake ɗaure ya naushi fuskarsa da ƙarfin gaske, take kuwa ya kuma da baya ya faɗi. Da sauri sauran yaran suka nufi kan Shahid saidai kafin su ƙarasa inda yake Ogan ya dakatar dasu, tashi yayi tare da isa gaban Shahid ɗin batare da yayi magana ba ya zaro wuƙa a gefen cinyarshi take ya caka mishi a ciki tare da zarewa ya ƙara caka mishi. Jini ne ya ɓalle tamkar a kwata take Shahid ya sulale babu rai a jiki. Bakinsu na kulle duka amma hawayene ke bin fuskokinsu na bakin ciki. Sunaji kuma suna gani ya ketama Nusaiba haddi amma babu abinda zasu iya domin sosai aka ɗauresu bazasu iya taɓuka komai ba. Da sauri Rahma ta sake labulen jikinta na karkarwa ganin babu wanda ya ganta ne yasa tayi saurin komawa cikin banɗakin tare da kullewa. Wayarta da bata rabo da ita na hannunta, sau da dama Mami kan hanata shiga da waya banɗaki amma takasa dainawa domin wasu lokutan babu abinda zatayi a banɗaki take shiga saboda kawai kar a sakata wani aikin tana tsaka da chat. Tunawa da wayar da tayi yasa take tafara ƙoƙarin kiran Zarah domin a kawo musu taimako, kuka sosai takeyi amma na zuciya ganin kiran nata shiga ba'a ɗagawa. A ɓangaren Zarah kuwa tun ƙarfe 12:30nr kwamishina ya mata kiran gaggawa domin su gana, fiye da awa ɗaya yanata yi mata surutan da basu shafi gefen da take aiki ba amma a matsayinshi na shugabanta ta kasa tanka mishi duk da tanason komawa gida su gaisa da kakanninta da ƴan uwanta da sukazo. Wayoyinta gabaɗaya suna cikin mota hakan yasa batasan irin kiran da Rahma ke mata ba. Sai da suka tabbatar da babu wani sauran mai rai a cikinsu kafin su bar gidan. Ganin Zarah bata ɗaga kiran ne yasa Rahma danna kiran wani abokin Yayansu Mustapha dake aikin soja, bugu biyu ya ɗaga kiran yana mamakin kiranshi da tayi domin ya daɗe yana mata magiyar soyayyarshi amma tana wulaƙantashi. Yana ƙoƙarin magana ta riga shi. "Ka taimakeni Mustapha zasu kashemin iyayena dan Allah kazo da sauri". Ta faɗa da disasshiyar muryarta saboda

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29