Chapter 25
Chapter 25
da sunkuya zata ɗauka, a hankali yayi magana ta yadda ko Daddy dake tsaye agun bazaiji mai ya faɗa ba yace. "Wato ke a ko ina saikin bayyana salon karuwancin naki ko, saboda asan kin shahara a bariki ne zaki rungume mutum a bainar nasi kuma ki ƙi sakinsa saboda ke ga ƴar bariki ko? Toh Allah yasa dai rungumar iya ta ƴan'uwan taka ta tsaya bata kauce hanya ba." Da sauri ta ɗaga idonta da sukayi jazir saboda ɓacin rai ta kalleshi, wato cin mutuncin nasa har yakai matakin dazai iya zarginta akan ɗan'uwanta da suka fito ciki ɗaya, abubuwan da M.J yake mata idan ta mutu bata rama ba toh tabbas bata yafe mishi ba, batace komai ba ta ɗauki jakar ta nufi motarta. Cikin ƙoƙarin danne ɓacin ran da take ciki ta buɗe mazaunin direba ta shiga motar tana faɗin "Sorry dear na barka kana jira." Kasa amsawa yayi illa idanunshi daya kafeta dasu yanason gano wani abu tattare da ita. "Zarahty kina kallon kanki a madubi kuwa.?" ya tambaya da alamun mamaki a tattare dashi, leƙawa tayi kaɗan ta kalli madubi motar sannan ta ɗan juya ta kalleshi tana cewa. "Nifa Yaya banga inda kwalliyar nan ta ɓaci ba, kawai ka saba da ganin fuskar turawa ne shiyasa komai kake kallonshi sabo." Wanj murmushi yayi da iyaka fuska ya tsaya yace. "Ba batun kwalliya nakeyi ba, ke baki taɓa tsayuwa a gaban mirro kin fahimci how not ok are you ba, baki ga irin ramar da kikayi ba kamar wacce ta fito a prison, wai meke damunki ne haka little." "Ka dawo kenan ai Yaya, toh nidai aikine sukemin yawa bana samun lokacin hutu shiyasa kaga ina ramewa, ni banga ramar danayi ba ma fa." "Ke kam ai bazaki gani ba, amma nasan tabbas bayan aiki akwai wani abu daban a cikin ranki." "Uhmm nidai babu komai fa" "Shikenan I'll figure out myself tunda nadawo ƙasar, ja mota mu tafi gida gashi harsu Daddy sun wuce sun barmu." "Toh" ta faɗa sannan ta tayar da motar suka bar farfajiyar wajen, suna tafe suna hira tamkar wasu sa'anni ko kuma abokai saboda yanayin yadda suke hirar cikin raha da tsokanar juna, wannan na ɗaya daga cikin tarbiyar da iyayansu suka basu a zamanin da suke raye, son juna da kulawa ba tare da la'akarin babba ko yaro ba. Cikin Mintuna ƙalilan suka iso gidan horn tayi aka buɗe ƙofar sannan ta nausa kan motar zuwa ciki, a farfajiyar gidan suka tarar da Baaba tsaye tana jiran ƙarasowarsu. "Sannu da zuwa angona na kaina." tace lokacin data ƙaraso jikin motar, Sadiq ne ya fara buɗewa ya fita ta gefen da take tsayen, baki ta riƙe tare da zaro ido kamar tsohuwar da ta kama kwarto a ɗakin suruka, saboda mamakin yadda jikan nata ya sauya gabaɗaya duk kuwa da yawan ganinshibda takeyi idan suna video call, dariya yayi mai sauti ganin yanayin Baaban da kuma irin tsayuwar da tayi yace. "Haba amaryata irin wannan kallon haka, ko kina tsoron ayi saurin kwace miki ni ne.?" "Kwacewa ta nawa kuma Habu, ai yadda ka rikiɗe ka kuma bature nasan baza'a rasa wata baturiyar data kwace ka ba." "Toh ki kwantar da hankalinki ni ɗin naki ne ke kaɗai kinji my one and only kakaty." "Nifa banason wannan salon iskanci, daga dawowa zaka fara zagina tun daga kan iyaye da kakannina da wannan ɗan iskan yaren." Dariya yayi sosai kafin ya dakata yace "Toh yi haƙuri rabin raina, mu ƙarasa ciki sai muyi magana." Juyawa yayi yana waige-waige yace "Little ta shige ta barmu a tsaye ashe." "Wannan mai baƙin miskilancin ai ba tsayawa zatayi ba." "Ohh tana nan da halin ashe." "Sai abinda ya ƙaru." "Little ba dama Allah ya yaye mata." "Amin idan mai barin ta ne." Nan suka shige falon suka samesu idan Zarah ke zaune a ƙasan kujerar da Daddy yake kai ta ɗaura kanta akan cinyarshi, Abdallah da M.J kuwa suna zaune ne a kujera two seater. Zama sukayi aka shiga gaisuwar yaushe gamo da kuma ƙarin ta'aziyar da aka yiwa juna, sun jima suna hirar kafin Baaba ta umarci duk su miƙe domin zuwa dinning, Zarah ce tayi serving kuwa da abinda yakeso sannan suka fara cin abincin cikin nutsuwa da yadda addini ya koyar. Ko da suka gama ita ta tattare gurin ta kimtsa shi yabkoma kamar ba'aci abinci a gurin ba, falon ta kuma inda ta samu Daddy ya wuce sashin baƙi domin hutawa, zama tayi a gefen Baaba akan doguwar kujera tace. "Dear ba zakaje kayi wanka ka huta ba kaima." "Ke Zara'u kowa saikin ɓata mishi suna ne, mene ne kuma giya ɗin da kike kiranshi dashi." Dariya sukayi gabaɗayan su har M.J da hankalinshi yake akan wayarsa saida ya ɗan murmusa, tsagaitawa Sadiq yayi yace "Gaskiya ba ƙaramin wauta nayi ba na barin Nigeria ko wannan comedy ɗin da kike cirewa ai ya ishi mutum farin ciki na sati guda, Little jeki haɗamin ruwan wanka ganinan zuwa." Miƙewa Zarah tayi cikin dariya tabar falon. "Turanci bai yi muku rana ba tunda kun zubar da al'adun ku." "Kakaty kenan, bari naje nayi wanka na huta sai na dawo mu cigaba." Shima miƙewa yayi tare da bawa Abdallah hannu sukayi musabaha, hannu kawai M.J ya ɗaga mishi lokacin daya miƙa mishi hannu da nufin yin musabahar, baiyi mamaki ba domin tun zuwanshi ya fahimci ɗabi'un M.J ɗin musamman a gareshi da yake ganin tamkar baiyi farin ciki da dawowar tasa bane, kaɗa kai kawai yayi sannan ya nufi hanyar side ɗinshi. A tsaye ya tadda ta tana ƙara kimtsa mishi ɗakin, murmushi yayi mai sauti yace. "Ke dai bakya iya zama bakiyi aikin komai ba." "Tab! Ina hutawa mana, kawai naga baka da wanda zai maka ne shiyasa nakeyi." "Ai kuwa nagode na kusa kawo miki Anty ki huta." "Da gaske Yaya." ta faɗa da ɗoki "A'a bance ba karki kaini gaba." dariya sukayi duka sannan ya shige banɗakin yana faɗin. "Idan kin gama ki ɗaukomin fresh milk." "Toh" Sai da ta kimtsa ɗakin sosai duk da jiya ta shigo ta gyara amma tana ganin abubuwan da yakamata ta gyara musu waje, fita tayi domin zuwa ɗauko fresh milk ɗin. Baaba kaɗai ta tarar a zaune tana kallo sai Raliya dake ƴan goge-goge a gefe. "Yauwa Zara'u yanzu nake shirin aika Raliya ta kiramin ke." "Me zanyi miki kuma." "Bani ke nemanki ba, Abdullahi ke nemanki zakuyi sallama domin daga masallaci zasu wuce." "Ayya bari na haɗo saƙon Momi naje muyi sallama, suna ina ne." "Suna can falon baƙi." "Ina zuwa." Ta faɗa tana haurawa sama da gudu, ɗakinta ta shiga tare da nufar inda ta ajiye jakar tsaraba data tanadar musu da wacce takeso a kaiwa Momi, rufuwar jakunkunan ta gyara sannan ta ɗaukosu ta fito falon, kallon Baaba tayi tace. "Dan Allah Baaba Raliya ta kaiwa Yayana fresh milk karya fito yaga ban kai mishi ba." "Ɗaukomin ni na kai mishi." "Yauwa" ajiye kayan tayi akan kujera sannan ta nufi kitchen ta ɗauko fresh milk ɗin da cup ta miƙa mata, kayan ta ɗauka ta nufi falon baƙin ita kuma Baaba ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiq ɗin. "Ahh Baaba da kanki kuma, ita little ɗin me takeyi da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29