Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

dole sai mutum yazo inda suke." "Allah sarki to baki da mai taimaka miki ne.? " "Da inada mai taimakamin ba zaki ganni ni ɗaya ba ƴata." "Sunana Fatimah Zarah ne, ga wannan sadaka ce babu yawa." ta miƙa mata kuɗin. "Allah ya saka da alkhairi Batula, Allah ya albarkaci rayuwarki ya kareki daga sharrin maƙiya. Allah ya bani ikon taimaka miki watarana kamar yadda kika taimakamin." Cike da jindaɗi Zarah ke amsa addu'o'in kasancewarta mutum mai son taga babba nayi mata addu'a. "Bari naje direba na jirana zan dinga tsayawa wani lokaci mu dinga gaisawa." "Toh nagode Allah ya albarkaci rayuwarki." Almajirar ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta cewa take "Bazaki ƙara ganina ba yau ɗinma na fito ne da niyyar taimakon mai taimako ne, kuma gashi kinyi sa'ar kasancewa wacce zan taimakawa. Tun daga wannan lokacin sai ya kasance duk dare Zarah zatayi mafarkin wannan almajira sannan kullum zancen da take maimaita mata a cikin mafarkin shine. _Zaki haɗu da ƙalubale da dama a rayuwarki, ki zama mai hakuri da juriya tare da fauwalawa Allah lamuranki a duk lokacin da kika tsinci kanki cikin tsanani, sannan ki zama mai gaskiya a dukkan lamuranki. Kada kiyi zalunci kuma ki bari wasu su aikata, ki jajirce wajen bada gudumawar da za'a kauda zalunci a cikin al'umma._ Da farko abin baya damunta amma bayan tayi satikai tana neman wannan almajira a inda ta ganta sai abin yafara tsorata ta musamman da mutanen wajen ke faɗin basusan wata almajira ba, hatta Baba Sule data karɓi kuɗi a hannunshi wancan ranar yace bai san ina taje ba bayan ta fita a wannan rana. Lamarin na matuƙar damunta saidai ta kasa tunkarar kowa da lamarin. A wata ranar lahadi ne tayi mafarkin ƙarshe da almajirar wacce bata kuma zuwa mata ba saidai maganganun data gayamata a wannan rana sun tsorata ta. _Ni ba mutum bace ALJANA CE! kuma lokaci yayi dazan koma nahiyarmu, BATULA nayi miki alƙawari bazan ƙara zuwa miki a mafarki ko a zahiri ba amma kamar yadda na alƙawaranta zan taimaka miki idan lokacin taimakon yayi. Kada ki manta da nasihata a gareki domin zata taimaka miki sosai._ Tundaga wannan lokaci bata ƙara mafarkinta ba wanda ya gaskata mata cewa aljana ta taimakawa. Lokacin data fara aikin ƴan sanda sai ya kasance ta jajirce sosai wajen ganin ta ƙwaci duk wani haƙƙin talaka da ake dannewa, hakan ya jawo mata farin jini tare da ƙarin matsayi akai-akai har zuwa yanzu da take matsayin ASP. Alhaji Sulaiman, wato ɗan'uwan mahaifin Zarah nada tarin dukiya sosai da baisan adadinta ba. Babba kuma sanannen kamfaninshi shine _M.J JEWELS_. Kamfanin ya samu sunan ne daga Muhammad Jawwad wato ɗan shi na fari. Ana sarrafa duk wasu nau'ika na kayan ƙaleƙale a wannan kamfani kama daga kan ƴan kunnaye, sarƙa, awarwaro, zobuna, agogo da sauransu wanda ake sarrafasu daga ma'adanai daban daban danginsu zinari, azurfa, lu'u lu'u da dai sauransu. A shekarar data gabata ne yasamu nasarar mallakar lu'u lu'u wanda ya siya a hannun turawa da darajarshi takai dallar amurka miliyan talatin, an sakashi a wani akwatin tsaro na musamman wanda babu wani abu dazai iya fasashi koda guduma ne da bindiga dole sai mabuɗin shi wanda yake tamkar flash na jikin laptop. Kasancewar sai yayi shekaru da dama a ajiye kafin a iya sarrafashi yasa ya ɗaukeshi daga gidanshi inda yake da farko aka maida kamfaninshi saboda hare-haren ƴan fashi. Inda aka ajiyeshi a wani ɗakin sirri dake kamfaninshi, amma duk da hakan ba'a daina barazanar satar shi ba. Ganin hakan ne yasa shida ɗan'uwan shi Alhaji Abdul_Jalal suka yanke shawarar maida shi gidansa dake bauchi bayan an damƙa tsaronshi a hannun Zarah. Hatta iyayen basuda masaniyar a inda lu'u lu'un da akwatin tsaronsa suke tun bayan da aka damƙa mata ajiyarshi. *ALPHA*👽 Alpha wani taƙadirin ɗan ta'adda ne dayayi ƙaurin suna a Nigeria dama maƙotanta, ya shahara sosai wajen sace-sace da fashi gami da kisan kai. Saidai abinda yake matuƙar damun al'umma shine babu wanda ya sanshi bare inda yake zaune domin yanada yara da dama masu yimasa aiki saidai hatta wasu daga cikin masu yimai aiki basu sanshi ba. A duk lokacin da suka yi wani gagarumin laifi suna barin tambarinsu wanda yake sunan ALPHA ne haɗi da zanen bishiyar kwakwa🏝️, ta hakane ake ganewa idan sun aikata laifi saidai har yanzu ƴan sanda sun kasa kama koda ɗaya ne daga cikin masu yimasa aiki sakamakon manyan gwamnati da suke tare dashi. Tun bayan daya samu labarin wannan lu'u lu'u daga bakin wani yaronshi na sirri wanda yake aiki a _M.J JEWELS_. Yasha alwashin sace shi saidai matakan tsaron dake jikin akwatin ne ya hanashi samun damar satarshi amma yana kan shiri wajen ganin ya mallaki wannan kadara tare da ɗaiɗaita kamfanin _M.J JEWELS_. Bayan ya samu labarin inda aka maida lu'u lu'un sai yafara kiran Alhaji Abdul_Jalal tare da yimasa barazanar kashe wani nasa muddin bai sanya Zarah ta damƙa mishi akwatin da lu'u lu'un ke ciki ba, ganin bai samu nasara ba sai ya maida akalar barazanar shi ga Zarah ganin ita mace ce saidai yayi mamakin taurin kai irin nata domin akoda yaushe idan ya kira musayar maganganu marasa daɗi ne yake wakana a tsakaninsu duk da barazanar dayake mata na rasa wani daga cikin danginta. Dalilin dayasa ya yanke shawarar taɓa wani a cikin danginta ko zata saduda. _____________________________ Ciwon ciki mai tsanani ne yake damun Rahma wanda yayi sanadin harta kwanta a gadon asibiti, satinta biyu aka sallamota bayan jikinta yayi sauƙi sosai. Kasancewar lokaci ne na hutu yasa Ammi dake ƙasar Cairo ta yanke shawarar zuwa duba jikin Rahman tare da samarin ƴan biyunta, a garin Gombe jirginsu ya sauka hakan yasa dole suka ƙarasa garin Deba domin kwana washegari sai su wuce Bauchi. Bayan gaishe-gaishe da hirar yaushe gamo ne suma tsoffin suka yanke shawarar ayi tafiyar dasu domin suma dai basuje dubata ba tunda tayi rashin lafiyar, nan suka yanke cewa zasuyi sammako gabaɗaya suje domin a ranar tsoffin sukeson suje su dawo saidai tafiyar bazata yiwu da Baba Faɗimatu ba sakamakon ciwon ƙafa da take fama dashi. Da daddare Momi matar Alhaji Sulaiman ta kira Ammi tayi mata ban gajiya inda ta roƙeta akan tabar tata tafiyar sai jibi domin su tafi tare saboda gobe zataje ganin likitan ido akan matsalar ido da take fama dashi. Nan Ammi ta yanke shawarar barin tafiyar sai jibi kamar yadda ta buƙata wanda hakan zai bata daman zama da Baba Faɗimatu da za'a bari a gida ita kaɗai a ranar. Washegari kuwa kamar yadda suka tsara ƙarfe takwas suka ɗauki hanyar zuwa gari Bauchi bayan sun tsaya a cikin garin Gombe sun ɗauki Nusaiba a gidan Alhaji Sulaiman wacce itama za'ayi tafiyar tare da ita, Shahid ne ke tuƙa motar Adil na gefenshi yayinda Malam Usmanu, Malam Adamu, Baba Aisha da Nusaiba ke baya. A haka suke tafiya lokaci zuwa lokaci suna ɗan taɓa hira. Safiyar yau bayan Zarah tayi shirinta na tafiya aiki kamar koda yaushe akan kayan aikinta ta ɗaura Abaya sannan tayi rolling da mayafinta, fara ce kuma kyakkawa ce ajin ƙarshe daga kyawun fuska har na jiki, tana da tsayi amma ba sosai ba. Kyakkyawar fuskarta na ɗauke da dara-daran idanu

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29