Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,186 words 0 views Progress saved
Download Book

kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_ *Free Page 7* ... "Barka da zuwa ranki ya daɗe." ya faɗa cike da ladabi. Zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun office ɗin sannan ta umarce shi ya zauna shi ma. "Ina son sanin gaskiyar binciken da kayi game da case ɗin fyaɗe da aka kawo maka kwanaki biyar da suka wuce." Zarah ta faɗa tana mai zuba mishi idanu. Daburcewa yayi alamun rashin gaskiya, take kuma zufa ta keto mishi duk da iskar fanka dake kaɗawa a ofishin. Kana yace. "Dama ranki ya daɗe ƙazafi ne ake yiwa yaron amma bai aikata laifin ba." Bata ce komai ba ta ciro wata paper daga cikin jakarta ta miƙa mai tana mai cewa. "Ka cire mana hular mu da belt ɗin mu, sauran kayan kuma idan kaje gida ka aiko mana dasu. Sannan duk wani abu daya kasance mallakin hukumar mu ka dawo mana dashi, karɓi wannan takardar korarka daga hukumar mu ta ƴan sanda ne." Durƙosawa yayi akan gwiwan shi tare da faɗin. "Ki rufamin asiri ranki ya daɗe wallahi zan faɗi gaskiya, wannan aikin dashi nake ci da iyali na da mahaifiyata idan kika rabank dashi bansan ya zanyi ba. Sharrin shaiɗan ne yasa ni karɓa kuɗin toshiyar bakin daya bani." Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan ya bashi damar cigaba da magana inda yace. "Bayan an kawo case ɗin ni da kaina naje har gidansu wanda ake zargin, bayan mun zauna da mahaifinsa ne yake gayamin cewatabbas ɗan sa ya aikata abinda ake zarginsa dashi amma yana so a kori case ɗin inda ya bani kyautar kuɗi naira dubu ɗari uku, dalilin dayasa na kori case ɗin kenan. Dan Allah ranki ya daɗe ayimin afuwa bazan ƙara ba, nayi alƙawari." Tsaye ta miƙe kana ta mayar da takardar cikin jakarta sannan tace. "Ka shirya zama shaida a kotu." "Nagode ranki ya daɗe insha Allah zan kasance mai faɗar gaskiya." Nan ya rakota har bakin motarta yana mai ƙara yimata godiya. Gida ta wuce kai tsaye tana mai tuƙi cikin nutsuwa. "Har kin dawo." cewar Jidda dake tsaye a dinning tana shirya kulolin abinci bayan Zarah ta shigo cikin falon. "Ehh sannu da aiki fa Madam." Hararar wasa ta aika mata sannan tace. "Yauwa ASP." Tsayawa tayi a bakin bene da zai sadata da ɗakinta jin maganar Jidda dake cewa. "Jirani mu haura tare." Hannunta ta riƙe kana suka haura sama inda suka shige ɗakin Zarah wanda yake farko a jerin ɗakunan dake saman. Tsalle Jidda tayi ta faɗa kan gado tare da yin juyi sannan ta fuskanci Zarah dake ƙoƙorin rage kayan jikinta. "Ɗazu Baaba ke tsegunta min wani zance." "Wani zance kenan." "Zancen auren ki da Muhammad Jawwad mana." "Uhmm." "Meyasa ba zaki amince ba Zarah, babu wani fa da zaki aura ya riƙe ki da daraja kamar shi. Idan ma aikin ki kike tunani ai shi ɗan uwanki ne dole zai barki ki cigaba aikin ki batare da tsauwalawa ba, nikam bana tunanin akwai aibu a cikin wannan haɗin." "Kema kinsan dai Daddy uba ne a gare ni ko da ace Abba na yana raye shi mai zaɓa min miji ne, bazan iya cewa a'a ba kawai dai zaɓin Allah nake nema a cikin al'amura na." "Toh Allah ya shige mana gaba baki ɗaya ya kuma zaɓa mana abinda yake mafi alkairi." "Ameen" Zarah ta faɗa tana mai shigewa banɗaki. Duk wasu bincike daya kamata a gudanar sun gama haɗa shi, zuwa yanzu mai laifin ya daɗe da kasancewa a bayan kanta a kulle sai jiran ranar shiga kotu duk da yaƙi amsa laifin nashi. Har zuwa yanzu kuma Zarah bataje office ba tun bayan ranar sa takaiwa C. P rahoton abubuwan da suka faru. Yau dai ta shirya domin zuwa ofishin nata bayan tayi sallama da jama'ar gidan. Kyawawan motoci guda uku ta gani a harabar ofishin nasu wanda ya tabbatar mata da sunyi baƙin manyan mutane. Tun kafin ta ƙarasa ta hango Alhaji Mai Riga zaune a inda suka tanada domin zaman baƙi. Bata ko kalle inda yake ba lokacin da ta ƙaraso kusan shi saima shigewa ofishin ta da Sergent Bala ya buɗe mata ƙofar. Saida ta zauna kafin Sergent din yace. "Ranki ya daɗe wannan mutumin shine wanda yake ta ziryar son ganinki a kwana biyun nan, yau ma tun ƙarfe bakwai yazo saboda na faɗa mai zaki zo office yau." Kai ta gyaɗa sannan tace. "Ka shigo dashi." Fita yayi bada jimawa ba kuma ya ƙara shigowa inda a bayan shi Alhaji Mai Riga ne da wasu body guards dinsa da suka sha baƙaƙen kaya guda biyu. Kujerar da Sergent Bala ya nuna mai ya zauna. Shikuwa Bala sara mata yayi tare da ficewa a office ɗin. "Alhaji a tunani na kaine wanda keson zantawa dani." Faɗin Zarah Washe baki yayi tare da faɗin. "Ehh nine ranki ya daɗe." "Toh tsayuwar me waɗannan keyi anan." Umarni ya basu da su fita waje, nan suka nufi ƙofar fita bayan daya ys ajiye wata brief case a kan teburin........ ✍🏼 *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸 *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ .. "Na kwana biyu ina zuwa nan ranki ya daɗe bana samun ki." cewar Alhaji Mai Riga. "Ayya." ta faɗa a hankali. Zama ya gyara sannan yace. "Dama nazo ne akan maganar case ɗin yaron waje na da aka ce ke kike riƙe dashi, duk da naga wannan case ɗin na ƙananun jami'ai ne ba manya irin ku ba." "Akwai kundin tsarin daya ce babban jami'i kar ya karɓi case ne.?" "Ba haka nake nufi ba ranki ya daɗe, nazo ne kawai muyi magana akan case ɗin ne." "Ka samo mana wata shaidar ne.?" "Ba shaida ba dai ranki shi daɗe, kawai inason ayi wani abu akai ne." "Bangane wani abu ba." "Ehhm nace dama ko za'a bar maganar shiga kotun a sasanta a gida kawai." "Bai aikata abinda ake zarginsa dashi bane.?" "Ranki ya daɗe kinsan halin yara basa tunani kafin su aikata wani abin." "Tambaya ce kawai nayi bai aikata bane." "Ehh toh gaskiya yace min ya aikata amma...'' Hannu ta ɗaga mai alamun batason jin sauran zancen sannan tace. "Toh Alhaji ya aikata ya

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29