Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

saka kaya batare data shafa man ba, turo ƙofar da akayi ne yasata dakatawa tare da maida kallonta ga Baaba dake shigowa bakinta ɗauke da sallama. Amsa wa tayi tare da faɗin. "Wannan tsohuwa me zakiyi min a ɗaki ne haka daya saki haurowa sama, dan wannan zuwan naki kam akwai abinda ta kawoki tunda nasan ba haurowa sama kikeyi ba." "Yo idan ba wani abu ba mai zanzo nayi a bene nikam salon watarana na faɗi a garin sauka." Baaba ta faɗa tana mai zama a gefen gadon Zarah. Sai da suka gama barkwancin jika da kaka sannan Baaba tayi gyaran murya tace. "Zara'u." Ɗagowa tayi ta kalleta, gani yanayin fuskarta ne yasa tagane magana ce mai mahimmanci zasuyi. "Na'am Baaba." "Kin sani Zara'u kin kai mun zalin daya kamata ace kema kinyi aure kamar ƴar uwarki Jidda, aure shine darajar duk wata ƴa mace koda kuwa tana da tarin dukiya, kyau, muƙami ko nasaba. Ba mu da yawan zuri'a Zara'u kune muke fatan ku hayayyafa ku sama mana masu yi mana addu'a damu daku gaba ɗaya koda bama a raye, shekarunki na haihuwa fa yanzu 23 yakamata ace kinyi aure kin sama kanki daraja musamman a irin yanayin aikin da kikeyi da ake tunanin duk wata mace da takeyin shi bata da kamun kai. Dan Allah ki siya mana mutunci da kanki kar a fara maganar a gari ana cewa mun barki sakaka." Shiru Zarah tayi batare da tayi magana ba, Baaba ce ta kuma cewa. "Munyi magana da babanku Sulaiman yace nagaya miki ki turo mishi wanda kika tsayar domin manya su shiga maganar." "Baaba bawai auren ne banaso ba, akwai burika na da nakeson cikawa wanda nasan va kowani namiji dazan aura bane zai bani damar cikasu, shiyasa ma bana saka auren cikin lissafina a yanzu amma idan lokaci yayi zanyi insha Allahu." Ta faɗa alamun maganar Baaba bata wani dame ta ba. "Toh akwai wani wanda kuka sasanta ne ko kuma kukeson ku sasanta tsakaninku dashi.?" "Dan Allah Baaba ki barni ni babu wani da nakeso ko muke soyayya, aikina shine a gabana yanzu." Cewar Zarah da ta miƙe ta nufi gaban durowar kayanta. "Nima ai ina fatan ki kasance tare da aikinki kodan kawo ƙarshen waɗanda azzaluman mutanen, amma ki dawo ki zauna muyi magana domin bankai ga faɗin sakon da aka aikoni na isar ba." "Waye kuma ya aikoki.?" "Toh da farko dai mai saƙon yace bazai zo da kanshi bane gudun kada kiji nauyin shi kiyi abinda bashi ranki ke so ba, alfarma ce yake nema a gurin ki nason haɗa zuri'a dake, ma'ana dai yana neman alfarmar ki akan yanason ya haɗaki da ɗansa ku raya sunnar manzo S. A. W a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Kuma yana fatan ace wani bai riga shi ba sannan yace a barki kiyi shawara kafin ki bada amsa." Wani kallo Zarah ta mata kafin tace. "Waye da wannan doguwar wasiƙa kuma Baaba." Miƙewa tayi kana tace. "Doddon ku mana Sulaimanu yace yana neman alfarmar ki amince da auren ɗan sa Muhammad Jawwad." Dariya sosai Zarah tayi jin yadda Baaba ta kira Daddy wai Doddo kana ta tsagaita ganin har Baaba takai kusa da ƙofa, ƙarasa wa tayi inda take sannan tace. "Ban fahimce ki sosai ba Baaba." "Ke dai ba kurma bace sannan kuma ke ba mahaukaciya bace bare nace bakya fahimta, abinda dai kikaji shi nake nufi idan kuma kina tantama ne to ki ɗau waya ki kirashi ya miki ƙarin bayani." ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin. Ta daɗe tsaye a inda Baaba ta barta tana sakawa da kuncewa akan maganganun Baaban, lokaci ɗaya kuma ta watsar da zance daga tunaninta sannan ta nufi durowar ta ɗauko wata doguwar rigar atamfa super ta zura. Mai kawai ta shafa a leɓanta kana ta zura takalmi ta fice zuwa falo inda tasan Jidda na jiranta. A zaune ta same su ita da Saleem sun tasa laptop a gaba da alama abu suke gani a ciki mai mahimmanci. Jidda ce ta ɗago ta kalleta tace. "Madam ASP tun ɗazu muke jiranki anan munkawo ƙara.'' Kyaɓe baki tayi kana ta gaishe da Saleem sannan ta kalli Jidda ta kuma cewa. "Ace mutum shi kullum cikin zolaya kamar mara damuwa." "Wace damuwa ne dani nikam, ga mijina a gefe ai sai farin ciki ko da yaushe." Jidda ta fada. Bata kulata ba sakamakon abinda Saleem yake nuna mata a cikin laptop ɗin, shiru sukayi gaba ɗaya suna mai maida hankalinsu kan laptop ɗin. "Na rigada na gama bincike kuma na tabbatar shi ne mai laifin shaidune kawai suka rage mana, sannan nayi magana da babban likitan asibitin da yarinyar take akan Jidda zataje ta gudanar da duk wasu bincike da rahoton likita da za'a buƙata a kotu, yanzu binciken ya rage na ɓangarenki daga nan kuma a shigar da ƙara kotu." Cewar Saleem "Abun zaizo da sauƙi ai, nima yanzu nake so na fita na gudanar da wasu bincike na saboda gobe nakeson a shigar da ƙara kotu." Faɗin Zarah. "Yanzu baiyi yamma ba Zarah.?" Cewar Jidda. Kaɗa kai tayi kana tace. "Inason zuwa ofishin ƴan sanda da suka fara kai ƙara ne domin haɗuwa da Inspector ɗin wajen, na samu labarin yafi zama a office a irin wannan lokaci." "Ki tsare shi ya faɗa miki gaskiya fa Zarah kuma ya gayamiki nawa a bashi ya danne gaskiya." Jidda ta faɗa cike da takaicin abinda aka aikatawa Fahima. Dariya Zarah tayi sannan ta maida kallonta ga Saleem tace. "Gaskiya Sa.Jid ina tunanin kwanan nan zan shigar da matar ka aikin ƴan sanda ita ma, naga alama ta fini zaƙewa akan aikin nan." "A'a ki rufamin asiri, ai aikin ƴan sanda sai irinkj jajirtattu bana su Jidda bane." Faɗin Saleem cike da zolaya. Dariya suka yi duka kafin Zarah ta miƙe ta koma ɗakinta inda ta ɗauko mayafi da jaga, sallama ta musu sa'an nan ta fice domin zuwa inda ta faɗa musu. A hankali take driving har ta iso bakin ofishin, kallon gurin tayi wanda ke tsabtace sosai sai ƴan sanda da mutane dake shawagi ɗaɗɗaya. Kasancewae gilashin motar mai duhu ne yasa jami'an basu gane wacce ke ciki ba har saida ta fito, nan tsirarun da suke farfajiyar wajen suka ƙaraso gabanta da hanzari suka sara mata. Kai kawai ta jinjina sannan ta fara tafiya a hankali inda suke take mata baya har zuwa ofishin Inspector ɗin. Miƙewa yayi da sauri daga kishingiɗen da yake tare da miƙewa...... *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* _Putting smile on our readers face_ https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp ___________________________________ *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.* *Littafin ASP ZARAH na

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29