Chapter 6
Chapter 6
gudu ta nufi hanyar ɗakinta...... Da gudu ta nufi cikin ɗakin tare da nufar inda ƙaramar na'urarta take ajiye, sashin abubuwan da suka faru a cikin satin ta shiga tare da playing daga ranar farko. Daddy da sauran mutanen gidan ne suka shigo ɗakin, gabaɗaya suka zauna domin kallon abinda ke wakana a cikin na'urar. Saidai gabaɗaya babu abubuwan da suka faro a kwanaki uku da suka wuce wanda hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani wanda ya shaidama Alpha na'urar da ta saka. Cike da takaici ta rufe na'urar tare da kwanciya akan gadonta. Babu wanda ya tanka duk suka fice a ɗakin. Babu daɗewa kira ya shigo wayar Zarah, hannu ta kai ta janyo wayar tare da kallon fuskar wayar domin ganin mai kira. Ɓoyayyiyar number ce ke kira, tamkar bazata ɗaga kiran ba saida ta kusa yankewa kafin ta ɗaga tare da karawa a kunnenta batare da tayi magana ba. "Na tabbatar yanzu kin fara gaskata abinda Alpha yake da damar yi ga duk wanda ya shiga gonarsa." Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa Zaune ta miƙe batare da tayi magana domin ta gane wanda yake maganar. Magana ya cigaba dayi ta hanyar faɗin "Kada kiyi saurin karaya ta hanyar ajiye aikinki Zarah domin kin riga kin shiga wasan da baki da damar fita, ba'ayi komai ba tukun. Kin shirya bada kadarar ko baki shirya.?" Mamaki ne ya cikata jin abinda ya faɗa, tabbas Alpha ba ƙaramin shiri yayi akanta ba domin da Daddy kaɗai tayi maganar ajiye aiki kuma shiɗin ma bai goyi bayan hakan ba sannan tanada tabbacin cewa ba wajen Daddy yaji wannan batun ba. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye kafin tace "Bana zuwa akan lokaci amma tabbas idan na iso waje ina jan ragamar kowani wasa tare da kasancewa mai nasara, ka faɗama kowaye ya sanar dakai cewa Zarah zata ajiye aiki da yaje ofishinta a gobe ranar litinin domin ya samu maka cikakken bayani." Bata jira mai zaice ba ta kashe wayar gabaɗaya. Takalmi ta zura tare da fita zuwa falo, dukkan su suna zaune kamar yadda suke da farko. Zama tayi kusada ƙafafun Daddy tare da faɗin "Daddy inaso gobe zan koma bakin aiki." "Zara'u wace irin magana kikeyi haka, kodai kema ƙwaƙwalwarki ta taɓo ne kamar yadda ƴar uwarki ta samu.?" Faɗin Baaba wacce maganar da Zarah tayi ya tadata Zaune daga kishingiɗen da take. Sunkuyar da kai tayi batare da tayi magana ba. Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa. "Baaba ina ganin mu barta ta koma bakin aikinta ƙila akwai wani muhimmin abu da zata gudanar ne bayan haka kuma zamanta a gida bashine zai dawo mana da waƴanda muka rasa ba. Hasalima aikin nata zai taimaka wajen binciko da masu hannu akan wannan lamarin." Jinjina kai Baaba tayi cikin gamsuwa da maganganun Daddyn sa'an nan tace. "Toh yaya batun Rahmatu kuma.?" "Ehh Amminsu zata wuce da ita can Cairo a cigaba da duba lafiyarta tunda maigidan nata ya amince, Zarah kuma zata zauna anan saboda binciken da zata cigaba da gudanarw. Sannan ina neman alfarmarki Baaba da ki cigaba da zama anan tare da ita, kasancewar mace bai kamata ta zauna ita kaɗai ba saboda kare mutuncinta. Insha Allahu kuma zamuyi ƙoƙarin ziyartar ku lokaci lokaci kamar yadda muka saba." Cewar Daddy "Babu damuwa Sulaimanu Allah yayi albarka ya albarkaci zuri'a." Da Ameen sika amsa gabaɗaya kafin kowa ya miƙe domin zuwa kwanciyar bacci wanda a zahiri ba haka bane domin raba dare suke gaban mahalicci suna kai mishi kukansu. Washegari tun ƙarfe bakwai Zarah ta fito cikin shirinta sanye da kakinsu na ƴan sanda, baƙin wando da shuɗiyar riga, inda ta ɗora baƙar Abaya mai ratsin shuɗi a saman kayan sannan tayi rolling da gelen rigar. Ammi kaɗai ta tarar zaune a falo tana jan carbi, ƙarasawa tayi tare da zaunawa a ƙasan kujerar da Ammin ke zaune. "Barka da safiya Ammi." Kanta Ammin ta kwantar akan cinyarta tare da shafawa a hankali. "Ina fatan kintashi lafiya.?" "Lafiya lau Ammi, zan wuce aiki ina barar addu'a." cewar Zarah lokacin da take gyara kanta a cinyar Ammin. "Allah ya kareki daga dukkan sharrin masu sharri, Allah ya nesanta zuciyarki da aikata abinda ba daidai ba, Ina roƙon Allah ya baki nasara ga duk abinda kikasa a gaba. Allah ya albarkaci rayuwarki." Cike da jindaɗin addu'o'in Ammin take amsawa da Ameen kafin ta miƙe tare da mata sallama ta nufi hanyar fita daga cikin falon. Gurin motarta da yaran Mustapha suka wanke mata ta nufa domin masu yi musu aiki tun bayan faruwar wannan lamarin suka aje aiki saboda tsoron kada a ƙara kawo wani harin a haɗa dasu tunda na farko dai hodar saka bacci aka shaƙa musu basusanai zai iya faruwa ba nan gaba. Cikin mintuna ƙalilan ta isa ofishin nasu, tun kafin ta ƙarasa parking sergent Bala ya iso inda motar take ya buɗe mata ƙofa bayan ta gyara tsayuwar motar. Ƙamewa yayi har saida ta fito sannan ya kulle motar. "Ranki ya daɗe barka da safiya. Ya ƙarin haƙurin mu." "Barka dai Bala, haƙuri mungode Allah." ta faɗa tana mai fara tafiya domin isa ofishinta. Karbar jakarta yayi bayan yace" Allah ya gafarta musu." "Ameen." tace a taƙaice. Haka ƙananun jami'an suka jigaba da mata gaisuwa harta ƙarasa cikin ofishin ta. Tana ƙoƙarin ajiye wayarta akan tebirinta kira ya shigo, ganin mai kiran ne yasata sakin wani kyakkyawan murmushi. "Assalamu alaiki ya habibaty." abinda aka faɗa kenan bayan ta kara wayar a kunnenta "Wa'alaiki salam Dr. Jiddah amaryar Bar. Saleem." Zarah ta faɗa tanamai zama a kujerarta ''Ki faɗawa wanda bai sani ba, naga alama tsokanar da bakiyi kwana biyu ba kikeson yi kuma ba kulaki zanyi ba. Dafatan kin tashi lafiya yasu Ammi." "Lafiya lau suke duka." "Ya ƙarin haƙuri kuma." "Alhamdulillah." "Allah ya musu Rahama." "Ameen Ameen. Ina kika baro maƙalematan naki banji motsinsa ba." Zarah ta faɗa cike da barkwanci. "Ke dai bari habibaty, jiya kwana nayi ina mishi kukan nagaji da zama a cikin masu jajayen kunnuwa shine yau ba shiri ya fita domin fara haɗa tarkacensa." Jidda kenan take maganar cikin sanyi murya. "Babu kyau abinda kike aikatawa fa, ki dinga damun bawan Allah yana miki abinda kikeso koda shi bayaso ɗin." "Auren kenan ai kema kiyi kigani ko baza'a miki abinda kikeso ba." Kafin tayi magana aka kwankwasa ƙofar ofishin nata da haka tace. "Zamuyi magana anjima SA.JID zan fara aiki a ofis." "Innalillahi! Yanzu Zarah tun ba'a sadakar bakwai bama har kin fara fita wannan ƙaddararren aikin, so kike ki jama kanki zance a gari." Shiru Zarah tayi na wani lokaci kafin tace" Jiddah ya zanyi to, *Alpha* kinsani Idan ban kasance a ofis ba na wani lokaci mutane da dama zasu rasa abubuwa masu mahimmanci sanadin wannan mutumin." "Shikenan Allah ya taimaka, nima dai Insha Allah zuwa wani watan zamu dawo." Jiddah ta taɗa cike da tausayin Zarah. Sallama sukayi sannan suka katse kiran lokaci guda. Umarni ta bada a shigo lokacin da take ajiye wayar a kan teburinta. Sergent Bala ne ya kuma shigowa hannunshi ɗauke da farar takarda, saida ya sara mata kafin ya fara magana. "Ranki ya daɗe wannan saƙo ne daga ofishin mai girma kwamishina, jiya da yamma ya aiko
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29