Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

kakeson ayi kenan." "Yauwa nace a sasanta kawai anan inyaso sai abiya kuɗin da mahaifan yarinyar suka kashe akan nema mata lafiya." "Baka gudun ya kuma aikatawa." "Toh kinsan halin yaran zamani su komai sukayi gani suke daidai ne." "Yanzu kana nufin a janye ƙarar kenan.?" "Ehh haka nakeso ranki ya daɗe, ni ɗan siyasa ne hakan zai iya jawomin cece kuce a tsakanin jam'iyun adawa. Yanzu ga wannan." Ya ƙarasa faɗa yana mai buɗe jakar da body guard ɗin ya ajiye, kuɗi ne maƙil a cikin jakar rafar dubu ɗaɗɗaya an jere su. Murmushi tayi har saida dimple ɗinta ya lotsa sosai kana ta sa hannu ta taɓa kuɗi tare da ɗaga rafa ɗaya ta jujjuya sannan ta aje. Cikin ƙwarin gwiwa alamun nasara Alhaji Mai Riga yace. "Shiyasa ban turo kowa ba nace bari nazo da kaina ayi maganar zamu fi fahimtar juna." Gyaɗa kai tayi kana tace. "Zan iya tambayan ka idan babu damuwa." "Bakomai ranki ya daɗe yi tambayarki." "Kana da ƴa mace.?" "A'a babu yarona ɗaya ne dai wannan da muke magana akan shi." "Ohk to kana da Yaya ko Ƙanwa mace." "Gaskiya babu dake dukkan mu maza ne iyayen mu suka haifa. Amma lafiya kike min irin tambayar nan ranki ya daɗe." "Ban kai ga ƙarasa tambayata ba idan na gama zan amsa taka tambayar. mahaifiyar yaron nan yakake jinta a ranka a matsayinta na waccw nake tunanin tun auren ƙuruciya shine har yanzu." "Gaskiya bazan iya misalta miki yadda nake jinta a raina ba, wannan dalilin ne ma yasa har yanzu banyi mata kishiya ba." "Masha Allah, yanzu Alhaji misali wani ya shiga gidanka yayi wa matar ka fyaɗe sannan da akayi bincike aka gano mai laifin, wani irin mataki zaka ɗauka.?" "Wallahi da hannu na zan kashe shi, idan ban samu damuwar haka ba kuma zan tsaya da dukiya da ƙarfina har sai naga an yanke mishi mummunan hukunci akan laifin daya aikata min." Dariya Zarah tayi sosai sannan lokaci ɗaya ta gimtse kana ta jawo jakar kuɗin gabanta ta zuge zip ɗin kamar yadda yake tare da tura jakar gaban Alhaji Mai Riga kana tace. "Kamar yadda kakejin zaka tsaya da ƙarfi kuma da dukiyarka ni idan akayi qa matarka fyaɗe, toh ni inajin fiye da hakan wajen ganin na tsayawa kowace mace da aka ketawa haddi domin abi mata haƙƙinta. Wannan kuɗin da ka kawo bazai taɓa canzamin ra'ayi domin na saba riƙe fiye da irinsu, cin hanci koh? Toh kasani cewa bakayi kuɗin da zaka iya bawa Zarah cin hanci ba, wannan kuɗin ko albashin ma'aikatana na wata ɗaya bazai iya biya ba. Shin kasan girman laifin da ka aikata na baiwa ƴar sanda cin hanci.? Tabbas zan baka mamaki kuma dole a yankewa yaron ka hukunci daidai laifin daya aikata. Banason na ƙara jin ko da kalma ɗaya ce ta fito daga bakin ka idan kuma ba haka ba, hmm kulle ka ba wani abu mai girma bane a wajena sannan babu wani jami'in dayasa isa ya saka ni buɗeka idan nayi hakan. Dan haka kaɗau tarkacen kuɗinka ka ficemin daga office." taƙarasa faɗi tana mai buga teburin, wanda hakan ya ƙara ɗarsa tsoro a zuciyar Alhaji Mai Riga domin dai dama ƙarfin hali kawai yakeyi yake iya mata magana amma ba ƙaramin kwarjini take masa ba. Batare da tanka ba kamar yadda tace yaɗau jakar tare da ficewa daga office ɗin yana mai banko ƙofar da ƙarfi. Murmushi Zarah tayi sannan tace. "Mai Riga kenan, ba shirin wasa nayi a kanka ba duk wani motsin ka yanzu a tafin hannu na yake.". Kiran wayar daya shigo ne yasa ta saka hannu ta jawo wayar daga inda take, numbar Daddy da tagani ne yasa bata ɗaga ba har saida ta yanke sannan ta maida kiran. "Assalamu alaikum." "Wa'alaikumus salam daughter barka da safiya." "Daddy ina kwana." "Lafiya lau kun tashi lafiya koh.?" "Lafiya kalau Daddy ya Momi." "Gata nan lafiya lau, yasu Baaban dai da mutanen turai." "Duk suna lafiya Daddy." "Kin fita aiki ne yau.?" "Ehh ina office." "A'a toh bari na bari ki koma gida kar na katse miki aiki, dama nayi tunanin kina gida ne shiyasa na kira muyi magana." "Bakomai Daddy ba aiki nakeyi ba dama, zamu iya magana babu damuwa." "Toh Masha Allah, nace ko Baaba ta isar miki da saƙo na.?" "Ehh Daddy ta gayamin kuma na amince." "A'a Zarah idan kina da wani ki faɗa kar na tauye miki." "Babu kowa Daddy." "Toh nagode kwarai Allah yayi albarka." "Ameen Daddy." "Sai anjima ki gaishe da su Baaban." "Zasuji insha Allah." Nan suka yi sallama ta aje wayar a gefenta tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. "Oh ni Fatimaj Zarah, aure da mijin da bansan shi ba." Sai kuma tayi murmushi ita kaɗai tare da kaɗa kai. ......... Shi kuwa Alhaji Mai Riga bayan fitarsa daga office ɗin Zarah cike da takaicin rashi haɗin kai da bata bashi ba, kai tsaye gidan alƙalin kotun da aka shigar da ƙarar ya nufa. Bai wani sha wahala ba aka shigar dashi cikin gidan, bayan sun gaisa da alƙalin ne yake faɗa mishi abinda ke tafe dashi nason kar a yankewa yaronshi hukunci tare da korar ƙarar gabaɗaya. Toh ƙasar tamu dai ta ɓaci kowa son kuɗi kawai, babu ɓata lokaci alƙalin ya amince gani irin maƙuda kuɗin da aka aje a gabansa. Sallama sukayi zuciyar Alhaji Mai Riga fal da farin ciki. *By* *Jasmine*🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Paid book_. _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki._Za'a turo kuɗi ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Page 9* *ALPHA VILLA*👽 Kamar koda yaushe ba'a taɓa ganin daga inda yake magana saidai a jiyo sautin muryar sa. "Raliya ki kula sosai banaso a samu wata matsala, yanzu idan kuka bar nan za'a kaiki filin jirgi inda daga can zaki wuce Gombe, kiyi amfani da adireshin dana baki ki isa zuwa gidan kamar yadda na tsara miki, ki tafiyar da komai cikin tsari kada ki bari a gano ki. Gobe da safe ne zaki isa zuwa gidan bayan ta fita zuwa gurin aiki. Kin fahimce ni." "Na fahimta Oga zanyj komai yadda kace." Raliya dake rakuɓe a gefen ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ta faɗa kanta a sunkuye. "Banason rawar kai Raliya, samo masaniyar inda lu'u lu'un yake shine kawai aikinki, ban baki damar kiyi yunƙurin sacewa ba wannan aikin ba naki bane. Ina ƙara jaddada mi ki." "Ba za'a samu matsala ba Oga." "Ki tashi kije ki gama kintsawa ƙarfe biyar za ku wuce." "Toh na barka lafiya yallaɓai." ta faɗa tana mai miƙewa daga durƙushen da ta ke sa'an nan ta nufi ƙofar da zata fidda ta daga cikin falon. ........................................ Haka Alhaji Mai Riga yayi ta zagawa yana siye bakin waɗanda ke da masaniya akan case ɗin hatta lauyan bogi da Zarah ta ɗauka saida ya bashi maƙudan kuɗi akan ranar da za'a shiga kotu yayi tawaye yace shi lauya ne mai kare wanda ake zargi. Yau ta

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29