Chapter 18
Chapter 18
da Baaba tayi kana suka gaisa da Sa.Jid. "Ina kwana Anti." Raliya ta faɗa lokacin da take goge TV stand, sai a lokacin Zarah ta lura da ita, cikin wani ƙayataccen murmushi ta amsa wanda ya saka Raliyan shiga kogin tunani na dalilin yin murmushin nata. Dinning suka nufa duka harda Baaba da bata cika cin abincin acan ba, Jidda ce tayi serving ɗinsu duka sannan suka fara cin abincin. "Yauwa Zara'u, munyi waya da mahaifinku ɗazu yake gayamin Muhammadu zai iso anjima sannan zuwa jibi zai ƙaraso nan ku zanta akan shirye shiryen da zaku gabatar." cewar Baaba. "Uhmm." shine abinda kawai ta furta bayan ta saka tissue ta goge bakinta. "Kinyiwa Ubanki badani kikeyi ba, mutum sai shegen miskilanci na tsiya." ta kuma faɗa. Idonta ne ya kawo ruwa ta kalli Baaban da nufin yin magana sai ta rigata. "Sulaimanu nake nufi." ta kuma faɗa tana harararta. Dariya Jidda tayi kana tace. "Gaskiya Baaba zanyi missing ɗin dramar ku da Sahibaty." "Mene ne kuma meizu.?" Baaba ta faɗa cikin gyatsina. Wannan karon har Zarah da Saleem saida suka dara sosai. "Rabo da su Baaba kwanan nan zan kaiki London a koya miki turanci kema." cewar Saleem. "A'a ɗan nan meye haɗina da turanci kuma, ku dai da suka asirce ku sai kuyi ta fama." "Kunga idan kuka biyewa Baaba to tabbas yau zaku rasa flight, ku hanzarta na sauke ku a airport ɗin nima aiyuka gareni sosai a office." cewar Zarah tana miƙewa. Suma miƙewa sukayi inda Jidda ta shiga ta fito musu da trolleys ɗinsu. "Mu zamu wuce Baaba sai munzo biki." Inji Saleem. "Ɗan albarka mungode Allah yabar zumunci, ai bikin ma a can Gombe za'ayi muma duk zamu tattara mu biyo bayanku acan za'ayi komai." "Toh Allah ya kawo ku lafiya." "Ameen yaron kirki, a ƙara hakuri dai da juna." "Idan ma da ni kikeyi ba kulaki zanyi ba kinga tafiyata." cewar Jidda. Har gurin mota ta rakasu tana musu addu'ar sauka lafiya har saida taga sun fice a gidan kana ta juya ta koma falo. Basu daɗe da isa airport ɗin ba jirginsu ya tashi bayan sunyi sallama cike da kewar juna da zasuyi, zuciyarta gabaɗaya babu daɗi ta nufi office ɗinta. Bata ko yi minti biyu da zama a kujerarta ba Bala ya shigo bayan ya nemi izini, ganin yanayin da take ciki yasa ya ajiye takardun daya shigo dasu ya fice, takardun da ya ajiye ta jawo tare da fara nazartarsu, bayanai ne kan wani da suke zargin yana safarar miyagun kwayoyi wanda zai shigo garin Bauchi nan da kwana biyu, inda ta wannan hanyar suke fatan tabbar da zarginsu tare da kamashi muddin zarginsu ya tabbata. Tsaki taja mai sauti bayan tayj tunanin hanyar da ita kaɗai ce mafita a garesu batare da sunsha wahala ba, da kanta take so tayi wannan aikin gudun kada a samu matsala musamman yadda yawancin jami'ai yanzu zuciyarsu ta gurɓace da son kuɗi, saidai kuma batason aikin dazai dinga kaita hotel ko kaɗan amma babu yadda ta iya dole wannan karon tayi wannan aikin da kanta. Gabaɗaya wuninta na yau a office tayi shi ne cikin tsara yadda aikin zai kasance cikin sauƙi batare da sunsha wahala ba, sai ƙarfe shida tabar office ɗin bayan ta zaɓi team ɗin da zasuyi aikin tare. Bata tsaya doguwar hira da Baaba ba yau saboda a gajiye take, hakan yasa bayan sunci abincin dare ta wuce ɗakinta ta kwanta. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ "Momi zamu wuce." cewar Abdallah da suka fito a sashin M.J cikin shirinsu na tafiya garin Bauchi ganin amarya Zarah, sunyi kyau cikin dakakkiyar farar shadda da suka saka iri ɗaya sai zuba ƙamshi sukeyi musamman M.J da ya fito a asalin ango mai shirin amarcewa da sabuwar amarya. "Yauwa ƴaƴan kirki ga wannan ku kaiwa ƴar tawa, ku gaishemin da Mamana kuma." cewar Momi dake zaune tana miƙawa Abdallah wata ƙaramar jaka. "Me amaryar mu ta samu ne haka Momi." ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe jakar. Hannunshi ta buge kana tace. "Ban yarda a buɗe ba, ku bata shi yadda na baku." "Toh Momi mun wuce." "Allah ya kiyaye hanya ku gaishesu." M.J ke jan motar yayinda Abdallah ke gefenshi yana zuba surutu, tun yana kulashi har ya gaji ya daina wanda hakan yasa shima Abdallah ya maida hankalinashi kan wayarsa saboda sanin halin miskilanci irin na M. J. ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ Cikin shirinta na ƴan sanda ta sauko ƙasa hannunta riƙe da agogo tana ƙoƙarin ɗaurawa, yayinda take ɗauke da wata jakar baya madaidaiciya mai matuƙar kyau da sheƙi. "Zan wuce office Baaba." ta faɗa bayan ta zauna a hannun kujera tana ƙarasa ɗaura agogon. "Yanzu Zara'u mijin da zaki aura zaizo ganinki amma bazaki haƙura da zuwa aikin nan ba yau." "Aiki mai mahimmanci zan gabatar Baaba sannan bazai wani ɗaukeni dogon lokaci ba idan ya iso ki kirani sai na dawo, sannan Raliya ta shirya musu abinda ya dace." "Shikenan Allah ya bada sa'a ya kuma kare." "Ameen Baabata nagode sosai." ta faɗa tana ficewa a falon. Kai tsaye office ta nufa, bata wani ɓata lokaci sosai ba suka wuce hotel ɗin da zasuyi aikin acan bayan ta canja kaya zuwa doguwar rigar abaya sannan tayi rolling da gyalen rigar. Mintuna kaɗan suka isa, can nesa da gate ɗin sukayi parking, mintuna kaɗan sai ga wata tsadaddiyar mota ta shiga hotel ɗin. "Jeka Bala ka tabbatar kayi kyadda ya dace." Zarah ta faɗa. "Toh ranki ya daɗe." Ya faɗa yana mai fita a motar, tabbas idan bakasan shi ba baza kayi tunanin jami'in tsaro bane saboda kalar shigar da yayi ta ƴan iska, kai tsaye farfajiyar hotel ɗin ya shiga tare da nufar inda motar tayi parking. Glass ɗin motar ya ƙwanƙwansa, sauke gilashin baya akayi inda wani hamshaƙin mutum ke zaune. "Lafiya kuwa ɗan saurayi." cewar Alhajin. Waige-waige Bala tayi kamar mara gaskiya kafin ya fara magana irinta ƴan shaye-shaye yace "Alhaji naga kamar kazo hutawa ne shiyasa nace bari nayi maka tayin zafafa ko zasu tayaka hutawa." "Shigo daga ciki." ya faɗa bayan ya buɗewa Bala ƙofar. "Banason idanun mutane shiyasa nace ka shigo daga ciki, yimin bayani sosai." "Ya Alhaj akwaisu dayawa fa amma yanzu ɗayace ta rage, sunanta end of discussion saboda zazzafa ce sosai." cewar Bala tamkar me maye. "Kada kasani asarar kuɗi fa ka kawomin ƙazama kamar ka." ya faɗa yana gyatsina saboda kayan jikin Bala sun matuƙar yagalgale. "Ina fada maka ya Alhaj, zafafa nake dasu bari na nuna maka hotonta." ya ciro wayarsa a aljihun wandon jikinshi, hoton da Zarah ta ɗauka ɗazu ya nuna mishi wanda take sanye da doguwar riga. Laɓɓansa ya lasa bayan yaga hoton kasancewar sa manemin mata yasa babu ɓata lokaci ya fito da rafar kuɗi na dubu-dubu ya ajiye guda biyu a cinyar Bala tare da faɗin. "Kirata yanzu tazo." Sowa Bala yayi tare da danna kiran wayar Zarah yana faɗin. "End of discussion harka ta tashi maza kizo yau kakarmu ta yanke saka." Katse wayar yayi yace. "Yanzu zaka ganta yanzu ya Alhaj." Buɗe kofar motar akayi inda direban Alhajin ya shigo tare da faɗin. "Na gama komai yallaɓai ga key ɗin ɗakin nan room 234 a sama." "Ohk" kawai yace tare da karɓan key ɗin. A daidai wannan lokacin kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29