Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Asp Jasmine Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kama ranar lahadi inda gobe ranar litinin za'a shiga kotu, dukkan su suna zaune a falo suna hira jefi- jefi wanda akasarin hirar tsakanin Jidda ne da Baaba domin Saleem da Jidda suna gaban na'ura mai kwakwalwa suna gudanar da aiki. Baaba ce ta kalli gefen da su Zarah suke kana tace. "Zara'u ince dai mahaifin naku ya faɗa miki matsayar da ya yanke game da bikin ku." Kallonta Zarah tayi batare da ta tanka ba ta maida hankali kan abinda ta keyi, Jidda ce ta maida hankalinta wurin Baaba tace. "Wace matsaya kuma Baaba tunda ta rigada ta amince.?" "Ai uban nasu yace nan da watanni biyu za'ayi bikin, shima Muhammadun ya kusa dawowa gida domin fara hidimar bikin." inji Baaba "Lallai kice mu ma mu fara shiri kenan Baaba mun kusa zama amare." Jidda ta faɗa cike da zolaya. "Sosai ma kuwa." Faɗin Baaba. "Amma Yaya Sadiq zai dawo bikin koh.?" "Ehh naji Sulaimanu na cewa sun gama karatun zaije da kanshi ya taho dashi, kinsan tunda yaji labarin rasuwar nan shima yake ta noƙe noƙen son cigaba da zama a cikin turawa." "Gaskiya kam ya dawo bikin ƙanwa babu babban Yaya ai ba zaiyi armashi ba." "A toh su daɗi su keji ganin kansu a tsakiyar arna suna shawagi." "Kai Baaba bafa duka bane arna akwai musulmai sosai." "Duk jirgi ɗaya ya kwaso ku ai." "Baaba watarana dai zamu kaiki ƙasar turawan nan kiji yadda akeji idan ana can." "Allah ya tsareni ni Faɗimatu, bana fatan gani ko a mafarki na. Zara'u wani irin aiki ne kuke yi haka da baza ki bari kizo kiyi karin kumallo ba, ina fa lura dake kwana biyun nan sam bakyason cin abinci, shiyasa kike ta ƙarewa kamar kazar mayu." Ta ƙarashe maganar hankalinta na kan Zarah. "Baaba ko kece kika tsinci kanki halin da take ciki baza ki samu nutsuwa ba sai kin kai ga ci." Faɗin Jidda "Yoo wani hali ne take ciki banda na sama kanta damuwa sai an daina cin hanci a ƙasar nan, waɗanda suka fita ma sun gwada sun ƙyale." "A'a fa Baaba case ɗin fyaɗe ne a hannunta kuma gobe za'a shiga kotu, shiyasa take ƙoƙarin tara duk wasu hujjoji gudun kada aka dasu, gashi dama iyayen yarinyar ba masu hali bane." Salati Baaba ta shiga dokawa harda ƴar guntuwar kwalla kafin tace. "Ashe har yanzu ana wannan rashin imanin a ƙasar nan, shikenan dai shi talaka bazai taɓa hutawa ba. Yanzu mene ne ribar yiwa mace fyaɗe, kawai saboda tsantar zalunci da son rugujewa mutum rayuwa. Insha Allahu duk asirin su saiya tuno an hukunta su, shiyasa nake son aikin Zara'u saboda gaskiyar ta. Nayi ma Muhammadu magana ma dole zai barta ta cigaba da aikinta saboda rashin ta zai iya saka al'umma cikin wani hali." "Baaba ƙasar tamu yanzu ai sai dak kawai mu cigaba da addu'ar samun gyara, amma kullum lamura ƙara taɓarɓarewa suke yi." "Kullum cikin addu'a muke kuma bazamu taɓa gajiya wa ba." Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin dake addabar ƙasar ta mu har zuwa lokacin da su Saleem suka gama aikin suka dawo cikin falon aka cigaba da hirar da su. Washe gari da wuri Zarah ta bar gidan bayan tayi sallama da su Jidda da zasu haɗu acan kotun. Kotun ta cika maƙil saboda ba shari'a ɗaya ake gudanarwa ba, baya ga haka kuma abokan hamayyar Alhaji Mai Riga su ma sunzo dan ganin yadda zata kasance. Shari'a biyu aka gudanar kafin azo kan case ɗin Fahima. Kamar kowace shari'a, lauyoyin sun hallara a inda aka tanadar musu domin zama. Nan aka umarci su gabatar da kansu. "Suna na Bar. Labaran Ahmad tare da abokin aiki na Bar. Gideon Wangson mu ne masu kare wanda ake tuhuma." Faɗin ɗaya daga cikin lauyoyi biyu dake zaune a inda aka tanadar musu. "Shin Bar. Labaran bakai bane lauyan masu ƙara." Faɗin Alƙalin. "Bani bane my lord." Inji Labaran. Jinjina kai kawai alƙalin yayi kana yace. "Ina lauyan masu ƙara." Shiru babu amsa. Alhaji Mai Riga ne ya kalli inda Zarah take tare da yin wani shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni, ita ma murmushin ta maida masa mai alamar bakasan me kake yi ba. Kafin ya gama mamakin murmushin daya gani a fuskar ta ya jiyo sautin magana. "Suna na Barrister Saleem Sa'ad ni ne lauyan masu ƙara, my lord ayimin haƙurin lattin da nayi hakan ya faru ne a sanadin cunkoson ababen hawa da na samu a hanya." cewar Saleem wanda shigowarsa kenan ya nufi gurin zaman lauyoyin. "Bar. Saleem a kiyaye na gaba." cewar alƙalin. Ba iya Alhaji Mai Riga bane ya shiga mamaki da ruɗun jin abinda ya fito daga bakin Saleem, hatta Labaran saida ya ruɗe domin dai ko kafin a fara gabatar da zaman kotun na yau sun tattauna da Zarah a matsayin shi na wanda zai tsayawa Fahima. Lallai ya tabbatar ta samu labarin zaiyi tawaye shiyasa ta tanadi wani lauyan. Zufa ce ta fara keto masa ta kowani sashi ba jikinshi, ɗagowa yayi jin alƙali ya buƙaci su gabatar da shaidar su ta farko, sai dai me...............✍🏼 *BY* *Jasmine*🌸🌸 07048961623. *ASSALAMU ALAIKUM* *Uwargida da amarya har yanzu fa ƙofa buɗe take, zaki iya samun damar kasancewa da ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA a cikin zafafan darussan da nake gabatarwa a ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, domin samun dabarun zama da miji, ɓoyayyun sirrikan da zakiyi amfani da su wajen mallake mijinki cikin sauƙi, tare da sahihan kayan gyara na musamman sha yanzu magani yanzu. Kada ki bari ƴar uwarki ta labarta miki.* *Cikin ikon Allah a ƙanƙanin lokaci group ɗin mu na farko ya cika kuma yanzu haka mun buɗe wani sabon group ɗin ga masu buƙatar su shiga a baje wannan kolin dasu. Kada kumanta dai zaku iya samun damar shiga wannan group ta hanyar tuntuɓar wannan number 07048961623. Ina jiran zuwanku, ni ce dai takun da bani da tamka HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA*. *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Paid book_. _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Za'a turo kuɗi ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Zarah ya gani ta kafe shi da idanunta masu rikitarwa, nan take ya ruɗe har saida yaji Gideon na gabatar da tambayoyi ga Kabeer kafin ya maida hankali. Mintuna talatin ana fafatawa tsakanin ɓangare biyun inda Saleem ke gabatar da zafafan shaidun daya tada hankalin Alhaji Mai Riga da muƙarrabansa, domin hatta inda yake cewa Zarah tabbas ɗan shi ya aikata laifin da ake zargin shi saida aka gabatar a gaban kotu. Nan fa kotu ta rikice kowa na faɗin albarkacin bakinsa musamman ƴan adawan Alhaji Mai Riga. Hutun rabin lokaci aka alkali ya bayar, gaba ɗaya jama'a aka fita waje. Duk yadda Mai Riga yaso ganin alkalin a wannan lokacin abu ya gagara, hankalin shi ne yaji ya tashi amma tunawa dayayi da irin maƙudan kuɗin da ya bawa alkalin sai ya ɗan samj nutsuwa tare da tabbatarwa kanshi samun nasara. A daidai wannan lokacin

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29