Chapter 9
Chapter 9
hade kanta da guiwa .... A hankali ya tako ya iso gurin ya zauna gefenta ..yana kallonta.. " Hudallah".... dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kalli motarshi ta sake maida kanta gurinshi ba tare da ta amsa ba ... a hankali yace "Me aka maki Huda? ....wani abu kike so ? .. Kai ta girgiza mashi a hankali tana goge idonta .... "To fada man mana ' ...ko mamanki ta dukeki? ... nan ma kan ta girgiza mashi tare da kura mashi ido ... "To Yaya sa'arki aka batawa rai? ...yauwa Hudallah goge hawayen kinji ki fada man ...oya Yaya Sa'a ce? ..ya fada cikin sigar lallashi .. Daga kai tayi tana fadin ..." Ba lauya bane ya cuci Yaya Sa'a yayi mata hard'e ...kuma sae da nace kar yayi mata ...amma yaki jina!! ..gashi yanzu ya saka mamanmu sae dukanta take ...tana kuka ..." Hard'e ? ...mene haka Huda?....! Harara ta balla mashi tana fadin " karka maidani yarinya mana ...kato da kai baka san Hard'e ba ....wanda idan akayiwa mutanen gidansu suyita kuka??? ..ko baa taba maka bane?.. Shiru yayi yana tunanin me take nufi ...zuwa can yayi saurin kallonta yana fadin ko dae Raping kike nufi ? Ba tare da tace mashi komae ba ta mike zata shige gida ...yayi saurin riko hannunta yana fadin ..." Tsaya man Huda kinji ....please idan kin shiga gidan kice ina son magana da mama ...!! " amma kai mugune ...!! ..baka ga irin marin da ta man ba yau" kake aikeni na mata magana ...so kake ta sake marina kenan. ? kamar yana tsoronta yace " Please Huda ki taimaka kinji ko "... "Idan ta dakeni ' kanka zan rama wallahi " Da sauri yace " Na yarda Hudallah " Shiga tayi ciki zuwa can ta fito tace mashi Idon mamar a rufe yake ....ta mata ...magana taki budewa .....ce mata yayi taje tacewa Yaya Sa'a dan Allah yana son magana da ita .. Kafin ta bashi amsa yaya sa'a ta fito daga gidan da gudu tana kuka ...tare suka shiga gidan har da Mahmoud din... Mama na kwance bata motsi daukarta yayi da sauri ya sakata mota sannan yaya saa da huda suka shiga ciki suna kuka sannan yaja da gudu suka fita daga lungun ... Direct asibiti ya nufa da ita ...cikin gaggawa aka amsheta ....bayan an dubata ne aka tabbatar masu da tana raye ..hawan jini yayi attacking dinta sossae ... Bp dinta 210 ... Daga Hudar har Yaha Saa kuka suke ...Barister Mahmoud kuwa tsaye yayi yana kallonsu ..shi ya biya kudin komae ...aka hada mata magunguna .. Har isha'i yana asibitin ...sae da ta daeo normal sannan likita yace zaa sallameta su tafi gida ..... Barister Mahmoud ya dauko su ya kawo su gida ...da zaya tafine ya fitk da 20k ya bawa mama yace su sayi abinci kafin ya dawo .. Sam Mama taki karba ...tace wanda ya mata bata sani ba ta gode amma wannan bara ta karba ba don yanzu bata bukatar taimakon duk wani mutun Taimakon Allah kawae take so ...Babu irin rantsuwar da bai mata ba ...amma taki karba ... Ganin yafi damuwa da Huda ne ya saka Yaya Sa'a saurin janyo huda jikinta tana hawaye ...don bata kaunar wani namiji ya kula Huda yanzu .....a iya saninta zata iya kashe duk wanda yayi kokarin batawa Huda rayuwa ... ganin kamar basu bukatar shi ya sakashi tashi ya tafi ...zuciyarshi cike da tunanin maganar huda ..."wae Hard'e"...what does she means? ...haka yayi ta sake sake har ya isa gida ... Yana Shiga Mama tace ya dauki matarshi ya tafi da ita ...don wallahi ta gaji da Hanne ....!!!... Ba dan yaso ba ya shiga dakin Hanne tana kwance sae barcinta take hankali kwance ....pillown da ta daura kanta ya dan buga kadan ta mike ba salati tana fadin ..."wane banzane mutun na bacci yake tadashi ? Ba tare da yace mata komae ba ya juya zai fita ..."sam hanne ba da'a" ...abunda ya fada kenan a ranshi ... hannunshi ta riko "Ohhhh ...Yaya ne ....Yi hakuri bansan kai bane yasin" ....ta fada tana dariya ba tare da ya juyo ba yace " ki iskeni falo zamu tafi gidan yau" ... Ihun dadi ta sake tana fadin " Haba yanzu naji magana amma an kunshe mutun cikin gidan sirikai ba damar ya sake sae shegen sa ido "... Ko nuna alamun yaji me take fada baiyi ba ...ya fice daga dakin ...kafin ya zauna har ta fito janye da uwar jikkar ... Mamanshi yayi wa bankwana tare da Abba ...sannan suka tafi ..da yake bai ci komae ba ..ya tsaya wani karamun restaurant zai sayi abinci ... Hanne tace " haba yaya me zaka saya a wannan karamin gurin dan Allah? wallahi ba girmanka bane ...!! Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITER'S..._ *_27 to 28_* Dan juyo yayi kadan yana kallonta cike da mamaki kafin yace " banda wani girma Hanne ..sae dae ke nake tunanin girmanki yakai diyar sarki a babban kauyenku !!! tasan magana ya fada mata sae ta kulle bakinta tayi gum ....har suka isa gida bata kara magana ba ..bareshi da ba kowa yake kulawa ba ... Gidan ya dan nunnuna mata sannan ya shige dakinshi ya barta hangame da baki ... ••°°•• Da kyar Yaya Sa'a tayiwa Mama bayani ta yarda ...ranar tace su tashi suje gidansu Barister Shehu ta fada ubanshi wata kila shi ya sauresu a bi masu Hakkinsu .... Da Mama da Yaya Sa'a sae Huda suka tafi ...cikin saa a harabar gidan suka iske su duka ukun tsaye da alama wani guri zasu ....sae sojojin dake tsaye cirko cirko Hajiyar na ganinsu ta daure fuska tare da kallon Shehu ....Mama ta iso ta gaida Alhajin ...tun yarda ya amsa mata gaisuwar jikinta yayi sanyi ... Tace " Alhaji nazo na sanar dakai abunda ya faru ." .. A wulakance yace "ina saurarenki" . tace " Alhaji mu talakawa bamu da komae sae Allah ...ni da diyata muna zuwa aiki anan gidan ...sae Shehu ya haye mata har ya mata fyad'e ...shine nazo na fada maka ko akwae matakin da zaka sauka " "Bullshit kauyawan banza da wofi!! ....matsayita!! sae uban me dan yayi Raping dinta ....kanta aka fara raping koko kanta aka kare ....? ..Kai Shehu ko yanzu kake bukatar Yarinyar nan ...na yarje maka kayi abunda kake so da ita ....gidan ubanka suka shigo ., ..basu isa su wulakanta me ba har gida...!!! "Dat my dady "....ya fada yana aika masu wani irin matsiyacin kallo ...!! Dad din yace ..".Guard !!....ku fitar man da wadannan matsiyatan ku bar waccen ...!!! ya nuna yaya Sa'a ... Da saurin Mama ta rugumeta tare da janta da gudu zasu fita daga gidan ...amma kafin su fita wani daga cikinsu ya fizge yaya Saa tare da tura mama da karfi waje ....haka ya dauki Hudar ya wurgota waje tana ihu tare da turje turje ..... Mama kuwa kwanciya tayi kasa tana birgima lokaci guda numfashinta ya fara sarke mata ....sam Huda bata lura da halin da mama take ciki ba ...tana jikin Gate din tana kuka tare da buga kanta jikin karfen kamar ranta zai fita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30