Chapter 3
Chapter 3
sakashi sakin bindigar kasa ..... Feedohm馃挒 馃挧馃挧 _*A DALILIN YAYATA..馃崄馃崄*_ 馃崄 *_HASKEN WRITERS ASSOCIATION馃挕_* Na Feedohm馃挒 _*DEDICATED TO*_ _EXCLUSIVE WRITERS..._ 7 to 8 Weldon Barister ...ba dae kace zaka hanani aikata abunda nake so ba ....good gashi yanzu zaayi komae da kai ... Barister Shehu ya fada lokacin da yake takowa kusa dashi ... Bai san lokacin da ya sauke mashi mari ba tare da shakarar wuyan rigashi ... wadanda suke tare sukayi saurin banbareshi tare da maida hannunshi baya suka rike ... Shehu ya sake dariyar mugunta yace .. Kayi abunda kake so Barister ....zaka bimu gidan mu karbi abunda nake bukata sannan ka tafi ....ko kuma na watsa wadannan pictures din a duniya na rubuta bayan na kaiwa Marayu Hakkinsu ...baristern duniya yaje da yan fashi sun karbe asirinsu ya tonu ...kayi tunanin makomar baristoci sannan kayi tunanin mutuncin mahaifinka sannan da son da yake maka ....na tabbata daga rannar da ubanka ya sami wannan labarin bara ya kara motsi ba ...kana sane da yana da hawan jini ....amma rufe wannan zancan shi zaya saka na goge wannan pictures din bayan wasu shekaru ....na lura kana so ka tuna man asiri ... don haka zabi ya rage naka ... Idanuwanshi suka ciko da kwallah ....tabbas indae har mahaifinshi yaga wannan labarin ya tabbata bakinciki zai zama ajalinsa .....ba tare da yace komae ba ya nuna kofar gidan da hannu ...alamun su tafi ... Mask suka saka sannan Barister Shehu ya sakawa Mahmud suka shiga .....kauren an turoshi da alamun haka suke rufeshi dan an kangeshi da dutse ta ciki ...... Baka jin motsin komae sae kukan kaji dake tashi cikin ....suka kutsa kai suka shiga ciki ...kamar rakumi da akala haka Barister Mahmud ke binsu ..... Barister shehu ne ya saka kafa ya naushi mamar dake bacci ....tayi firgigi ta mike tana tasbihi .... Nan da nan ya canza murya yace ina kudin da aka kawo masu .... Bamu da kudi Wallahi dan Allah kuyi hakuri ....ta fada tana hawaye . Karyane shegiya ....wani ya fada da karfi .. Kaine dae Shegen munafuki ....Huda dake bacci ta farka tare da bashi amsa ....ya kai mata uban duka da yake dama ba kaunarta yake ba .... Ta sake uban kara tana fadin ....Allah ya isa shege mugu ....ka bugi Uwarka na kashi ....... Bata rufe baki ba ya kara daga hannu da niyar dukanta ....Saa ta rungumeta tana kuka tare da bashi hakuri .... Mahmud dake tsaye kamar gunki ..yace ...No.........kayi abunda ya kawoka amma banda duka ....ya karashe maganar da karfi ... Gurin Uwar ya dawo yace....kina son ranki Hajiya ....ki fito man da kudin da aka kawo maki yau naira million goma da marece ko kuma na kasheki anan ... Wallahi hakkin marayune kuyi hakuri dan Allah ....ku barmu hakkinsu ...ta fada cikin kuka ... Duka ya kai hannu zai mata saa ta rarrafo tare da rike mashi hannu tana kuka ...Dan Allah karku dakar mana Umma wallahi inda kudine zan fito maku dashi ...ku barmu dan San Allah ..... Karkashin gado ta leka ta janyo jikkar bakko....ta fitar da tsumman dake ciki sannan ta janyo masu jikkar ta aje gabansu tana kuka .... Huda tayi tsalle tare da dira saman jikkar ta cire kallabinta ta daure a kugu tana kuka tana fadin ....Wallahi ko uwayenku zasu zo nan bara ku fita da jikkar nan ba .... Barister Shehu ya hankadata gefe guda ta fada jikin mahmud ....rikeshi tayi gam tana fadin ....karku tafi da ita Dan Allah ...da itane Mamana zata sakani Js One ....ku bar mana don Allah .... Lumshe ido yayi ya banbareta daga jikinshi ya fita daga dakin da sauri .. Motarsa ya fada ya cire Mask din dake fuskarshi ya jefar sannan ya data motar ya fita da ita daga lungun da gudu ....ko da ya koma gida Dad dinshi na zaune baki gate yana jiranshi ...yana ganshi ya taso tare da rungumoshi yana fadin .... Lafiya dae ko ..... Dauriya ya saka a ranshi ya sakar mashi murmushi yana fadin ....Alhmd dad ....me kake anan har yanzu .. hannunshi ya kama yana fadin ...taya hankali zai kwanta banga ka kwanta ba har 12 ..... Baice komae ba sae dae ya bishi da kallo suka shige ciki ...sae da Dad din ya rakashi har part dinshi sannan ya dawo ya kwanta .... Feedohm馃挒 馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...馃崄馃崄_* 馃崄 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_* Na Feedohm馃挒 _*DEDICATED TO*_ _EXCLUSIVE WRITERS..._ 9 to 10 Tunda suka tafi mutanen gidan suka hade guri guda suna kuka ...mamarce ke karfin halin lallashinsu amma sam Huda taki shiru sae ma abunda yaci gaba .....bawae yawan kudin takewa kuka ba ...wae Mamarta ta mata alkwarin idan har aka samu kudi ta kaita Js one zata dinga bata naira Hamsin na break to shi takewa kuka .... Saa kadae ta fahimci abunda Huda kewa kuka ...don sae da mama ta fita sallar asuba sannan ta rarrafa tare da kwanciya saman cinyar Saa tana fadin ....Yanzu Shikenan Yaya Saa tunda an dauke kudin mama bara ta dinga bani naira hamsin din da tace ba ta tara .....ta saka bayan hannu tare da share hawayen tana fadin ...Allah ya isa ban yafe ba ...kullun naira hamsin in kashe ashiri na saka talatin asusu ..don Allah nawa zan tara yaya Saa ... Saa tayi shiru tana jinjina rashin wayau na Huda ...bawae kudin suka dameta ba ...aa hamsin din da zaa bata takewa wannan ihun dama ....share mata hawayen tayi tana fadin ...Allah zai kawo wasu Huda kinji .. Karfe 9:30 na safe barister shehu yazo gidan karbar kudin wae zaa kaiwa wadanda zaa sayi gidan gurinsu .... tunda ya fara magana ...maman huda ke kuka har sae da ya dasa aya .....sannan ta fada mashi duk abunda ya faru ..... Salati ya fara yana dafe kai .....har da hawaye ..yana nuna yama fisu damuwa da dauke kudin da akayi .....don cewa yayi daga gidan police station ya nufa zai kai report dole a nemo wadanda suka sace kudin ...... Tace .. kawae ya barsu police babu abunda zasu iya yi a kae ...su sun barsu da Allah ko su waye ... Cemata yayi zaya je ya dawo in Allah ya yarda yanzu ...sannan ya mike ya tafi .....cikin kudin da ya sace ya dauko dubu dari biyar ya kawo mata ....yace tayi jari da su ...... Godiya ta dinga mashi har da kukanta ......Huda ta shigo dakin tayi saurin dukawa gurin mamarta ta ... Mamana me aka maki ....dan Allah kiyi shiru idan ma naira hamsin da zaki dinga bani kikewa kuka ...wallahi na yafe ki dinga bani arba'in idan kin samu ......ta karashe maganar kamar zatayi kuka ... Huda Lauya ya bamu taimako ...banda bakin gode mashi ....ku tayani godiya ....ta share hawayenta ... Mamana dama ya kawo ya sace.. kuma ya sake kawowa zai kuma sacewa ne .....ta fada tana kallonshi.... zumbur ya mike yana fadin ....Huda waye ....nan da nan zuba ta fara keto mashi .... Da hannu ta nunashi tana fadin ...eh mana banda kai waye yasan muna da kudi .... Mamanta tayi saurin buge mata baki tare da korata ta fice waje tana kwalla ... tana fita gurin motarshi ta nufa ....ta samu kwalba duk ta bula tayoyin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30